Lafiya Uwar Jiki

  • Home
  • Lafiya Uwar Jiki

Lafiya Uwar Jiki domin samun bayanai ingantattu na kiwon lafiya.ku cigaba da bibiyarmu a wannan shafi.mungode

Zafin jiki ko zazzaɓi a jarirai da yara alama ce da bai kamata iyaye mata su yi buris da ita ba. Iyaye mata wace dabara ...
04/08/2025

Zafin jiki ko zazzaɓi a jarirai da yara alama ce da bai kamata iyaye mata su yi buris da ita ba.

Iyaye mata wace dabara kuke amfani da ita a gida kafin zuwa asibiti idan jikin yaro yai zafi?

KAMAR WANE LOKACINE YA DACE MACE MAI CIKI TA DINGA KWANCIYA TA ƁANGAREN TA HAGU? Wannan wata tambaya ce mai matuƙar mahi...
04/08/2025

KAMAR WANE LOKACINE YA DACE MACE MAI CIKI TA DINGA KWANCIYA TA ƁANGAREN TA HAGU?

Wannan wata tambaya ce mai matuƙar mahimmanci da ya kamata mu amsa, wadda da ɗaya daga cikin mabiya wannan shafin tayi a rubutun mu da ya gabata.

Masana sun ba da shawara ga mata masu ciki da su fara koyon yi barci a gefen hagunsu daga kan makonni 20-24 (watanni 5-6 kenan). Domin hakan zai tmatuƙar taimaka musu wajen fara koyon barci a gefen hagu da wuri-wuri domin ya zama kin saba da hakan.

Zaki kuma iya farawa daga kan makonni 12 (watanni 3), idan har kin kasance kina jin daɗin yin barci a gefen hannunki na hagu, kuma ki tabbatar da cewa ba ki da wani yanayi na rashin lafiya da ya hanaki kwanciya ta ɓangaren.

Haka kuma shima babu laifi idan an fara daga kan makonni 16 (watanni 4 kenan) na goyon ciki, domin yin hakan zai taimaka miki ya zamo miki jiki. Ta yadda za ki saba da hakan tun da wurwuri kamin ciki ya kara tsufa.

Kar ku manta cewa barci ta ɓangaren hannu hagu na taimakawa mai juna biyu ta hanyoyi kamar haka:

-Rage ciwon baya
- Yana inganta gudanawar jini zuwa mahaifa.
- Yana Ƙara oxygenation ga jariri
- Yana rage takura ga hanta da ma shi kansa cikin.
- Yana inganta aikin da koda keyi ga jiki a kullum.

Idan kina neman shawara akan hakan, kya iya tuntuɓar unguwar zomanki domin samun keɓaɓɓen jagoranci da shawarwarin da k**e buƙata a karan kanki domin lafiyarki da ta jarinrinki.

Haƙƙin Mallaka: Ciki Da Raino

--------
Karku manta kuyi mana likes, shares, comments tare da gayyato mana Abokai suyi mana following.

Ku taya mu yaɗa wannan rubutun domin kaiwa ga wanda ba ma tare dasu a wannan shafin domin suma su amfana kuma muyi tarayya daku a cikin ladan.

"Faman ya'amal misƙala zarratin khairan yarah".

The Hidden Dangers of Ma********on and Po*******hy: A Threat to S*xual Life, Love Life, and RelationshipsIn today's soci...
04/08/2025

The Hidden Dangers of Ma********on and Po*******hy: A Threat to S*xual Life, Love Life, and Relationships

In today's society, the topics of ma********on and po*******hy are often shrouded in secrecy and shame. However, it's essential to discuss the potential consequences of these behaviors on our s*xual lives, love lives, and relationships. Excessive ma********on and po*******hy consumption can lead to a myriad of problems, including uncertainty in s*xual life, low s*x drive, premature ej*******on, and even a diminished attraction to the opposite s*x.

The Psychological Impact

Research has shown that excessive ma********on and po*******hy consumption can have severe psychological consequences, including:

1. Addiction: Ma********on and po*******hy can activate the brain's reward system, releasing dopamine and creating a feeling of pleasure. However, this can lead to addiction, as individuals become increasingly dependent on these behaviors to feel good.
2. Anxiety and Depression: The guilt and shame associated with excessive ma********on and po*******hy consumption can contribute to anxiety and depression. Individuals may feel trapped in a cycle of secrecy and shame, leading to feelings of hopelessness and despair.

3. Low Self-Esteem: The negative self-image and feelings of inadequacy that can result from excessive ma********on and po*******hy consumption can lead to low self-esteem. Individuals may feel unable to control their behaviors, leading to feelings of powerlessness and worthlessness.

The Impact on S*xual Life:

Excessive ma********on and po*******hy consumption can have severe consequences on an individual's s*xual life, including:

1. Low S*x Drive: Excessive ma********on can lead to a decrease in s*x drive, as individuals become desensitized to normal s*xual stimuli.
2. Premature Ej*******on: Ma********on can lead to premature ej*******on, as individuals become conditioned to rapid and intense stimulation.
3. Uncertainty in S*xual Life: Excessive ma********on and po*******hy consumption can lead to uncertainty in s*xual life, as individuals struggle to form meaningful connections with others.

The Impact on Relationships

1. Intimacy Issues: Excessive ma********on and po*******hy consumption can lead to intimacy issues, as individuals struggle to form meaningful connections with others.
2. Communication Breakdown: The shame and guilt associated with excessive ma********on and po*******hy consumption can make it challenging to communicate openly with partners.
3. Emotional Disconnection: Excessive ma********on and po*******hy consumption can create emotional distance, making it difficult to form deep connections with others.

Spiritual and Religious Perspectives

1. Islamic Perspective: In Islam, excessive ma********on is considered a sinful behavior that can lead to spiritual corruption.
2. Christian : In Christianity, excessive ma********on and po*******hy consumption are viewed as behaviors that can lead to spiritual impurity and separation from God.

Breaking the Cycle
If you're struggling with excessive ma********on and po*******hy consumption, know that you're not alone. Seeking help is the first step towards recovery. A mental health professional can help you:

1. dentify Underlying Issues: Understand the root causes of your behavior and develop strategies to address them.
2. Develop Healthy Coping Mechanisms: Learn new ways to manage stress, anxiety, and other emotions.
3. Improve Relationships: Work on building stronger, more meaningful connections with others.

Excessive ma********on and po*******hy consumption can have severe consequences on an individual's s*xual life, love life, and relationships. It's important to educate oneself about the potential risks and consequences of these behaviors. By seeking help and support, individuals can break the cycle of addiction and develop healthier, more meaningful connections with others.

‎DALILAN DA KE HANA ZUWAN AL’ADA GA MATA (Menstrual Delay or Absence)‎______________________________________‎‎1. Juna (P...
03/08/2025

‎DALILAN DA KE HANA ZUWAN AL’ADA GA MATA (Menstrual Delay or Absence)
‎______________________________________

‎1. Juna (Pregnancy) – Idan mace ta sami juna to al’ada na daina zuwa.

‎2. Canjin Hormone (Hormonal Imbalance) – Rashin daidaiton sinadaran hormone a jiki yana hana ovulation da zuwan al’ada.

‎3. Damuwa ko yawan tunani (Stress) – Yana iya katse aikin kwakwalwa da ke sarrafa zuwan al’ada.

‎4. Rashin abinci mai gina jiki ko ramewa sosai – Yawan rama ko rashin cin isasshen abinci na hana zuwan al'ada ko rikicewar ta.

‎5. Kiba (Obesity) – Yawaitar kiba na dagula tsarin fitar hormone Wanda me sa a sami karancin Al'ada.

‎6. Cutar PCOS (Polycystic O***y Syndrome) – Cuta ce da ke hana kwai girma yadda ya kamata, kuma na jawo al’ada ta ragu ko ta daina zuwa gaba ɗaya.

‎7. Shan magunguna barkatai ko magungunan family planning (contraceptives) – Suna iya dagula tsarin al’ada na wani lokaci.
‎________________________________________

‎SHAWARA:
‎Idan al’ada ta daina zuwa fiye da wata 2 ba tare da samun juna ba, yana da kyau a ga likita domin a gano musabbabin faruwar hakan tare da bada maganganun da s**a dace.
‎________________________________________

‎Kuyi Like, kuyi share, sannan kuyi following na wannan shafin dan samun irin wadannan rubututtukan da zarar mun dora Sani Abdullahi Wada

‎Ku biyo mu a shafin mu na TikTok dan samun videos da s**a shafi kiwon lafiya: tiktok.com/

‎Sannan kuna iya aiko da tambayoyin ku na kiwon lafiya Kai tsaye.

‎03/08/2025

Doctor, is hepatitis B curable? Well, it depends on the phase. If you have acute hepatitis B, yes, it's curable. If your...
03/08/2025

Doctor, is hepatitis B curable?

Well, it depends on the phase. If you have acute hepatitis B, yes, it's curable. If your immune system is strong enough, it will eliminate it without you even taking medication. Or, if you start antiviral treatment within 3 to 6months, with a good viral load, you will recover. Above 90 to 95 % of people actually recover, and that's because they detected it earlier.

That's why I advise you not to always assume you have malaria or typhoid and do self-medication. The more information you have about a disease, the better you'll make informed decisions. If you have any of these signs and symptoms similar to malaria,

Here are the signs and symptoms of hepatitis B:

Common Symptoms:
1. Fatigue: Feeling extremely tired and weak
2. Loss of appetite: Decreased appetite and weight loss
3. Nausea and vomiting: Feeling queasy or vomiting
4. Abdominal pain: Pain or discomfort in the upper right side of the abdomen
5. Dark urine: Urine that is darker than usual
6. Jaundice: Yellowing of the skin and whites of the eyes
7. Joint pain: Pain or stiffness in the joints
8. Fever: Elevated body temperature
9. Weakness: Feeling weak or lacking energy

Additional Symptoms:

1. Pale or clay-colored stools
2. Itching or skin Rashes
3. Headaches
4. Muscle pain
5. Swelling in the legs, ankles, or feet

Asymptomatic Cases:
Some people with hepatitis B may not experience any noticeable symptoms, especially in the early stages. Regular testing and screening are essential for early detection and treatment.

When you get to the hospital or laboratory, ask them to screen you for hepatitis. On your own, once a year, always do LFT (Liver Function Test) and an abdominal scan for your liver to check how it's doing. If you haven't been vaccinated for hepatitis B, please do so..

Chronic Risk:
About 5-10% of adults and a higher percentage of infants and young children may develop chronic hepatitis B.

Chronic Hepatitis B Symptoms:
Chronic hepatitis B symptoms can vary depending on the degree of underlying liver damage. Some common symptoms include:

- Fatigue: Feeling tired and lacking energy
- Abdominal pain: Discomfort or pain in the upper right part of the abdomen
- Jaundice: Yellowing of the skin and whites of the eyes
- Dark urine: Urine that appears darker in color than usual
- Loss of appetite: Decreased appetite and weight loss
- Nausea and vomiting: Feeling queasy or vomiting
- Joint pain: Pain or stiffness in the joints
- Spider angiomas: Small spider-like blood vessels visible in the skin
- Palmar erythema: Redness of the palms
- Ascites: Accumulation of fluid within the abdomen
- Bleeding tendencies: A tendency to bleed or bruise easily

Complications of Chronic Hepatitis B:
If left untreated, chronic hepatitis B can lead to serious complications, such as:

- Cirrhosis: Scarring of the liver, which can lead to liver failure
- Liver cancer: Increased risk of developing liver cancer
- Liver failure: Liver loses its ability to fight infection and remove harmful substances from the blood
- Encephalopathy: Deterioration of brain function due to liver malfunction

Why Hepatitis B is a Concern:
Hepatitis B can be more deadly than HIV/AIDS in some ways because:

- Higher risk of liver cancer: Chronic hepatitis B increases the risk of liver cancer
- Liver damage: Untreated chronic hepatitis B can lead to cirrhosis and liver failure
- Transmission risk: Hepatitis B can be transmitted through bodily fluids, including blood and semen.

Let's keep it real, folks! Hepatitis B is a serious disease that requires attention and proper care. If you're experiencing any symptoms or have concerns, don't hesitate to consult a healthcare professional.

~Dr Zainab Suleiman Buhari

Mafitsara na daga cikin halittun da suke da makobtaka da mahaifa.Wannan dalilin yasa mata masu juna biyu musamman idan c...
03/08/2025

Mafitsara na daga cikin halittun da suke da makobtaka da mahaifa.

Wannan dalilin yasa mata masu juna biyu musamman idan ciki ya fara girma basa iya rike fitsari saboda pressure.

Idan mace lokacin haihuwar ta yayi ta fara nakuda, daga cikin dalilan da yasa akan samu dogon lokaci kafin kan jariri ya iya fita daga cikin kwankwaso,akwai taruwar fitsari a mafitsara.

Ko yaya fitsari yake,zamansa ba tare da an yishi ba yana rage girman diameter din kashin kwankwaso yadda zaiyyi kankantar da kokon kan yaro bazai iya wucewa ba.

Mafita daya ce,shine mace taje tayi fitsari lokacin nakuda ko da bata ji.

Idan fitsari ya gaza fita ko ta kasa yi,wannan shine dalilin da yasa ake amfani da robar fitsari da ake cewa Catheter.

Idan an sakawa mace wannan robar fitsarin,hakan zai saka fitsari bazai taba taruwa ba bare ya hana kan jariri fitowa Idan mace na nakuda.

Nayi dan wannan bayanin ne saboda yadda mutane suke yawan korafin akan dalilin da yasa Idan an kawo mace asibiti muke rubuta musu su sayo catheter, domin wasu sunce basu san amfanin hakan ba.

Allah ya horewa magidanta abun sayar magunguna,masu juna biyu kuma Allah ya sauke ku lafiya. Ameen

Wannan hoton kwatankwacin yadda mafitsara ke zaune kusa da mahaifa ne cikin kwankwason mace.

Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad
RN,RM,PND

30/07/2025

Kada ka yarda ayima allura ba'a janye tufafi a wurin ba, za'a Iya samun babbar illa
A kula

Me ye matsalar cisge ta?A turance ana kiranta da "hangnail". Ƴar fata ce da ke tasowa daga fatar tushen farce. Wannan ƴa...
30/07/2025

Me ye matsalar cisge ta?

A turance ana kiranta da "hangnail". Ƴar fata ce da ke tasowa daga fatar tushen farce. Wannan ƴar fata tana tasowa sakamakon yawan bushewar fatar hannu, ayyukan hannu, cin farce, amfani da sinadarai ko kemikal masu lahani ga fata, da dai sauransu.

Tana ciwo ita kaɗai ma, ko kuma idan ta dunguri wani abu ko kuma zaren tufafi ya riƙe ta.

Kasancewar fatar hannu cikin damshi saɓanin bushewa, amfani da safar hannu, daina cin farce, shafa man shafawa duk na iya taimakawa kiyaye wannan matsala.

Domin yanke ta kuwa, ana iya sanya hannu cikin ruwan ɗumi sannan a yanke ta, ko kuma a shafa man shafawa sannan a yanke ta bayan ta yi laushi saɓanin cisge ta wanda hakan na iya janyo ciwo da kumburi.

Haka nan, cisge ta na iya bayar da kafar shigar ƙwayoyin cutuka cikin yatsa wanda hakan na iya zama karkare.

© Physiotherapy Hausa

WANE IRIN ATISAYE NE YAKE MAGANIN CIWON BAYA?Sau da yawa idan mutum ya ce "ina fama da ciwon baya", sai ka ji wani ya ce...
30/07/2025

WANE IRIN ATISAYE NE YAKE MAGANIN CIWON BAYA?

Sau da yawa idan mutum ya ce "ina fama da ciwon baya", sai ka ji wani ya ce "ba ka motsa jiki ne", ko kuma ya ce "ka riƙa motsa jiki akai-akai". To amma abin tambaya a nan shi ne: wanne irin atisaye ko motsa jiki ne ke taimaka wa mai ciwon baya?

Da farko dai, ya kamata mu bambance tsakanin "motsa jiki" da kuma "atisaye".

Motsa jiki na nufin duk wani yunƙuri da ya haifar da motsin jiki ko gaɓoɓi saɓanin hutu. Wato hutu shi ne lokacin da mutum ke kwance ko zaune ba tare da yana yin wani aiki ba. Misalan motsa jiki sun haɗar da: ayyukan gida, aikin gona/lambu, tafiya, sassarfa, gudu, tuƙa keke da sauran ayyukan yau da kullum.

Amma atisaye, kamar yadda Bahaushe ya aro kalmar daga turanci, wato "exercise", sannan ya yi mata kwaskwarima zuwa "atisaye". Atisaye na nufin tsararre, aunanne, ƙayyadajje, kuma keɓaɓɓen motsa jiki domin magance wata matsala ko bunƙasa aikin wani sashin jiki ko gaɓa ko kuma bunƙasa karsashin jiki gaba ɗaya.

Saboda haka, kamar yadda nau'o'in ƙwayar magani ke da yawa, kuma kowacce ƙwaya ke da keɓaɓɓen aiki domin ciwuka daban-daban, haka ma atisaye ke da nau'o'i daban-daban kuma domin ciwukan jiki ko gaɓoɓi daban-daban. Har ila yau, nau'in atisayen mai ciwon gwiwa ba zai zama iri ɗaya da na mai ciwon baya ko wuya ba.

Bugu da ƙari, shi kansa ciwon bayan yana da sabuba daban-daban. Wani ciwon bayan ya faru ne sakamakon tsinkewa/cirar nama, targaɗe, fashewa, bulli ko zaizayewar faifan tsakankanin ƙasusuwan gadon baya, gocewa ko karayar ƙashin gadon baya da dai sauransu. To yanzu mene ne sababin ciwon bayanka?

Saboda haka, kamar yadda sabuban ciwon baya s**a sha bamban, tilas ma nau'o'in atisayen da za su magance nau'o'in ciwon bayan su bambanta.

Abu mafi ban tsoro a kasadar fara atisaye ga masu ciwon baya ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba shi ne; sau da yawa, wasu ire-iren motsa jiki ko atisayen da mutane ke yi sune ke ƙara ta'azzara ciwon bayan. Ko kuma a shafe tsawon lokaci ana yi amma babu sauƙi.

Daga ƙarshe, ya zama wajibi ga duk mai wani nau'in ciwo: ciwon baya, ciwon wuya, ciwon ƙafaɗa, ko ciwon baya da ya guji fara yin duk wani irin motsa jiki ko atisaye da zimmar magance wani ciwo ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba.

Saboda kafin a samar da wani nau'in atisaye ga mai wani nau'in ciwon baya, sai an nazarci sababin ciwo, sannan a ɗora mutum a kan ƙeɓaɓɓen atisaye da shawarwarin da za su taimaka wajen sauƙaƙa ko magance ciwon.

Har wa yau, akwai kayan aiki da nau'rori na musamman da likitocin fisiyo ke amfani da su wajen rage raɗaɗin ciwon baya. Wannan hanya ce da ake magance ciwo ba tare da dogaro da shan ƙwayar maganin rage ciwo kullum ba.

Don haka, yin atisaye ko motsa jiki ga mai ciwon baya, ciwon gwiwa da sauransu, ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba tamkar shan magani ne ba tare da tuntuɓar likita ba.

© Physiotherapy Hausa

🌸 Bude Wuyan Mahaifa: Hanya Zuwa HaihuwaYayin nakuda, wuyan mahaifa yana budewa (wato yana fadada) domin bai wa jariri d...
30/07/2025

🌸 Bude Wuyan Mahaifa: Hanya Zuwa Haihuwa

Yayin nakuda, wuyan mahaifa yana budewa (wato yana fadada) domin bai wa jariri damar wucewa ta hanyar haihuwa.

📏 Matakan Bude Wuyan Mahaifa:
0️⃣ cm – Bai bude ba
3️⃣ cm – Farkon nakuda
6️⃣ cm – Nakuda mai ƙarfi
1️⃣0️⃣ cm – Cikakken budewa, lokaci ne na turawa!

💡 Bude wuyan mahaifa na iya ɗaukar awanni (musamman ga masu haihuwa karo na farko), amma kowanne cm na nufin kina kara kusantar ganawa da jaririnki. 👶💕

Domin samun lafiyayyen ciki, ana son mai juna biyu ta kula da wadannan abubuwa guda 30 da muka kawo a kasa domin samun y...
30/07/2025

Domin samun lafiyayyen ciki, ana son mai juna biyu ta kula da wadannan abubuwa guda 30 da muka kawo a kasa domin samun yin goyon ciki har zuwa haihuwa cikin nasara.

1. Fara zuwa awon ciki(antenatal care) da wurwuri

2. Cin lafiyayyen abinci da cin kayan marmari da kayan lambu.

3. Nisantar cin nama ko kwai din da Bai dahu ba.

4. Wanke yayan itace sosai, kafin ai amfani da su.

5. Shan Folic Acid supplements a watanni uku na farkon goyon ciki.

6. Motsa jiki akai-akai na da mahimmancin gamai juna biyu (Misali, tafiya, yoga dss)

7. Ki dinga motsa jiki na pelvic floor exercises.

8. Nisantar shan kayan maye, Misali irin su giya, taba sigari da sauransu.

9. Nisantar yawan amfani da duk wani abu mai dauke da sinadarin caffeine. (Coffee)

10. Ki dinga samun lokaci ki na hutawa ko yaya ne a duk lokacin da k**e da iko.

11. Shan ruwa sosai kullum don hana bushewar jiki.

12. Samun isasshen barci da hutu.

13. Cin abinci mai dauke da iron (irin su nama, kifi, wake).

14. Shan maganin iron idan likita ya rubuta.

15. Kula da tsaftar jiki da muhalli.

16. Nisantar damuwa da tashin hankali.

17. Kar a yi amfani da magunguna ba tare da shawarar likita ba.

18. Ziyarci likita idan kin ga wani canji mara kyau a jikinki.

19. Kar a dinga yawan daukar kaya masu nauyi.

20. Samun kukawa da tallafi daga miji da iyalai.

21. Kiyaye tsaftar baki da hakora.

22. Cin abinci mai sinadarin calcium kamar madara da yogurt.

23. Gujewa cin abinci mai yawan gishiri da maiko da yawa.

24. Kula da nauyin jiki, kada ya yi yawa ko yayi kadan.

25. Gujewa shan magunguna gargajiya ba tare da izinin likita ba.

26. Kula da lafiyar zuciya da hawan jini.

27. Zama a waje mai tsafta da iska mai kyau.

28. Kula da lafiyar fata, musamman wajen kauce wa kurajen ciki.

29. Gujewa yawan zama a rana ko zafi mai yawa.

3. Samun ilimi da shawarwari daga likitoci shafuka irin su Jaridar Ciki da Raino da kuma ma’aikatan lafiya lafiya.

Allah ya sauke ku lafiya!

Haƙƙin Mallaka: Ciki Da Raino

Karku manta ku taya mu yada (Share) wannan sako, domin muyi tarayya daku a cikin wannan aikin alkhairi.


Annabi yai gaskiya, ku duba yadda yai ta nusar da mu muhimmancin yin asuwaki fa. Ga shi sai a yau, wani bincike ya gano ...
29/07/2025

Annabi yai gaskiya, ku duba yadda yai ta nusar da mu muhimmancin yin asuwaki fa. Ga shi sai a yau, wani bincike ya gano cewa "rashin tsabtar haƙora na da alaƙa da motsewar hifokamfas, wace ita ce cibiyar hadda ta ƙwaƙwalwa".

© Physiotherapy Hausa

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lafiya Uwar Jiki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Lafiya Uwar Jiki:

  • Want your practice to be the top-listed Clinic?

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram