23/03/2025
Hauka wani ciwone mai matukar muni ga rayuwar dan'adam a wani lokacin ma akan gwammace ace mutum mutuwa yayi da ace ya haukace yana faruwa da mutum sau daya ne amman da dama akan karar da rayuwa a cikin sa domin yana faruwa ne ta dalilin tabuwar kwakwalwa ko kuma kwakwalwar ta dauki nauyin da yafi karfin ta.
Idan kwakwalwa ta riga ta tabu to yanada matukar wahala a samu ta dawo daidai k**ar yanda take a farkon marra zaka ga komai tsayin lokaci idan sanyi yai mata yawa tana saurin rikicewa, idan ta rikice saita harbawa zuciya yawan tsoro ko halarto da abinda baya yiwuwa amman kaga zai yiwu ko munanan mafarkai ko masu k**a da almara ko yawan shiru da zurfafawa acikin tinani mai nisa tare da karyewar zuciya sa'annan tana haddasa yawan mantuwa mai ban mamaki wani lokacin kaga mutum yana kuka babu dalili shima da kansa bai san me yake yiwa kuka ba to wannan alamun suna nuna kwakwalwa bata aikin ta daidai kenan kuma zata iya tabuwa a kowwane lokaci Allah ya kare.
1.Buguwa mai tsanani aka
2.Razanannen tsoro
3.Sihiri ko shafar aljan
4.Ciwon kai me tsanani wanda yaki jin magani ko kuma baa magance shiba
5.Mutum yaki yin barci ya tara shi har yai masa yawa
6.Ciwon hakki (Zalumci)
7. Haihuwa idan wani abu mara dadi ya faru
8. Zazzabin maleria ko typoid idan yaje kwakwalwa
9 dik ciwon da yake iya hana barci k**ar hawanjini da sauran su.
Wadannan dik idan mutum bai dauki mataki a kansu ba suna iya zamar wa mutum dalilin kamuwa da ciwon hauka amman a wani dalilin akan samu waraka gaba daya