04/02/2024
Barbushe Ɗan Bazume ɗan Garageje ɗan Dala shi ne wanda ake ɗauka a matsayin jagoran da ya fara assasa tsarin tafiyar da al'umma a Kano. Ya kasance ɗaya daga cikin jikokin babban ɗan Dala mafarauci wato Garageje inda ya yi fice wajen jajircewa a harkokin su na bauta da hidima ga iskokai.
Shi ne kaɗai manzon tsumburbura zuwa ga al'ummar masu bauta inda shi kaɗai ne ke iya shiga ɗakin da aka ware mata a kan Dutsen Dala domin ganawa da ita. Duk wanda kuma ya yi wani yunƙurin shiga to tabbas zai gamu da ajalinsa ne nan take.
Barbushe ya kasance idan ya hau kan Dutsen Dala ba ya sakkowa sai sau biyu a shekara kawai. Wannan lokutan sun yi daidai da lokacin sallah ƙarama da kuma babbar sallah. Duk da cewa suna bautar rana ne da bishiyar kuka da ake kira Shamas, mutanen wancan lokacin su na kiyaye tsarin ƙissafin kalandar rana da kuma na wata tuda da su ne ɗin ne su ke anfani wajen sanin lokutan bukukuwansu da kuma ayyukan su na noma.
A duk lokacin da Barbushe ya sakko ƙasa ya kan zo ne da saƙonnin Tsumburbura kan duk abubuwan da za su faru a wanna shekarar. Mutane sun gama sakankancewa da duk labarun da manzon Tsumburbura ya ne zuwa musu da shi domin kuwa su na ganin yanda su ne faruwa a kan idon su.
Ana gabatar ta kayan baiko ko sadaukarwa domin nuna gidiya ga Tsumburbura. Akan yanka baƙaƙen bunsuraye da sauran kayan anfanin gona a matsayin kayan kyauta gareta domin neman biyan buƙatu, gidiya ko kuma neman tsari.
A shekarar da Barbushe ya hango ranar mutuwarsa ya yi matuƙar baƙin ciki sannan kuma ya sanar da su wata ishara ta zuwan Bagaudawa waɗanda abindanya hango ya nuna wani ƙaƙƙarfan mutum na nan tafe wanda zai kawo ƙarshen mulkinda tasirin zuri'ar Dala daga Kano. Ya bayyana musu cewa wannan mutum zai rusa matsafarsu da kuma karkashe danginsu da wargaza gayyarsu da ɗaiɗaita al'adunsu da kuma tarwatsa zumuncinsu.
Wannan abu kuwa sai da ya kasnce bayan zuwa Bagauda da kuma kafuwar mulkin jikokinsa irin su Gijimasu da su ka tarwatsa matsafar Dala bayan da jagororin bauta na wancan lokaco su ka tsaya kai da fata kan cewa ba za su taɓa yarɗa su bada kai bori ya hau ba wajen bayyanawa bare sirrin Dakiri wato wannan abin da a ƙudundune da fatar baƙin bunsuru aka ɓoye a wani ɗakin da ke kan Dutsen Dala.
Tatsuniya