18/07/2025
SIRRIN MATA
1. Idan mace tana fushi, fiye da rabin abin da take faɗa ba gaskiya bane. Idan zai yiwu, rungumeta don ta natsu.
2. Lokaci mafi wuya a rayuwar mace shine lokacin da take nesa da namijin da take ƙauna sosai. Wannan na iya damun ta sosai.
3. Yana ɗaukar lokaci mace ta amince da namiji, amma idan ta yarda da kai, yana da wahala a sauya ra’ayinta. Sai dai idan ka bata mata rai sosai, to, ka manta da komai kenan.
4. Mace makaranta ce da ba zaka taɓa kamala daga cikinta ba.
5. Shaidar aure da kuka mallaka ba lasisin tuƙi bane, sai dai izinin fara koyon yadda za ka kula da ita. Ka ci gaba da jan hankalinta da kulawa.
6. Zata iya zama mai ɗaci, amma ta koma mai sanyi daga baya, duk ya dogara ne da yadda ka kusance ta. Ka rika kyautata mata koyaushe.
7. Mace ba ta manta abu da sauƙi ba, musamman raɗaɗin da ka jefa mata. Ka guji cutar da ita, ka guji maganganu marasa daɗi, ka rika yaba mata akai-akai.
8. Mace na iya zama mai ɓoye damuwa sosai. Sau da yawa idan suna ƙin nuna rauni a gaban namiji, sai su je su yi kuka a cikin sirri ko su shaida wa kawaye. Ka mai da matarka abokiyar rayuwar ka.
9. Mata suna son a roƙe su. Maza da dama ba su gane haka ba. Ee, wani lokaci s**an so a rika kula da su kamar yara.
10. Kowace mace tana da irin nata hali da ƙima kamar gishiri, ba a lura da gishiri sosai a cikin abinci, sai dai idan babu shi, sai komai ya zama ba daɗi.
11. Idan mace tana ƙaunarka da gaske, zata iya yi maka komai muddin yana faranta maka rai. Amma kar ka taɓa tilasta mata.
12. Idan ba ka kula da ita ba, zata samu wanda zai kula da ita. Suna nan masu ƙwazo da kulawa, sai dai ita ta zabe ka.
13. Idan mace tana ƙaunarka da gaske, ma har neman kuɗi daga gare ka tana jin kunya. Amma kai namiji na gari, kar ka jira sai ta nema. Idan tana ƙaunarka, ba zata bar ka ka ɓata kuɗi kan banza ba, wannan ne ke sa su zama na musamman.
Idan kana da mace mai kirki a rayuwarka, kar ka rainata.
Mata masu kyau tamkar kayan alfarma ne. Kada ka cutar da su domin da yawa a waje na roƙon samun irinta.
A duk nasarar namiji, akwai mace mai gaskiya a bayansa.
Milhart ✍️