08/11/2024
Amfanin Albasa
Albasa tana Qunshe da Sinadai masu yawa. Irin su Protien, Calcium, Vitamin A, Vitamin B, Vitamin C, Vitamin E, Da kuma wani Sinadarin mai suna Allicin.
Shi wannan ALLICIN din shi ke haddasa idanun mutum yake hawaye, aduk lokacin da ake yanka albasa.
Fresh Albasa (wato danya wacce ba'a dade da cirota ba) tana maganin Bacteria, Hypertension, Tarin Qwatai, tarin Mura, har ma da ciwon Qoda.
ALBASA tana maganin Shock, Suma, Farfadiya, Ciwon Zuciya, Ciwon Ciki, Ciwon Sugar, Asthma, Gastric Ulcer, da sauransu. Musamman ma idan an gaurayata da tafarnuwa.
Mutumin da ya fadi ya suma, idan aka samu albasa aka fere aka sanya masa akofar hancinsa guda, Insha Allahu wannan Qamshin albasan zai.Wartsakar da hanyoyin numfashinsa kuma zai farfado.
Don haka ne ake so Majinyatan da suke fama da Matsalar HEART ATTACK su rika yawan cin 'Danyar
Albasa a cikin abincinsu na yau da kullum.
ALBASA tana maganin ARTERIOSCLERIOSIS
(wato daskarewa ko Qekashewar Manyan jijiyoyin cikin zuciyar Dan Adam, da manyan hanyoyin jinin da s**a Turowa jini da kuma janyoshi daga zuciyar Dan Adam).
Don haka tana magance BLOOD PRESSURE kuma tana Qara taimakawa wajen blood circulation
(zagayawar jini ajikin Dan Adam).
MASU CUTAR DIABETES: Su samu Lansur mai kyau, awankeshi sosai. Sannan ayanyankashi, Asamu garin Qarago (kuli-kuli) cokali 3 tare da
Garin hulba cokali guda da rabi.
Barbada Wannan garin, sannan asamu Qatuwar Albasa ('Danya) ayanka aciki. Insha Allahu wannan abincin idan kana ci kamar sau 2 asati guda, zai zabge maka Sugar wanda ke cikin jininka, kuma zai kore maka Cholestrol daga jikinka.
Wanda yake fama da ZAZZABI, ko Mura, ko ciwon makogoro (makoshi) Ya samu zuma rabin kofi ya yanka Qatuwar albasa mai kyau aciki, Sannan ya cinye tare da zuman Insha Allahu zai samu lafiya da gaggawa.
Hakanan mai fama da Ulcer, ko jin zafi alokacin fitsari, shima idan yaci wannan hadin zai samu waraka sosai.
Allah yasa mu dace.