05/03/2024
DAURAWA VS ABBA GIDA GIDA
ABINDA NA FAHIMTA :-
NI AL-HAFIZY
1 - MALAM IBRAHIM DAURAWA YA IYA MU'AMALA DA KOWA, DUK DA DAN IZALA NE AMMA BAYA DAGA CIKIN MASU CIN MUTUNCIN BAYIN ALLAH SABODA SABANIN FAHIMTA, NI DAI BAN TABA JI BA, KO DA YAKE BA KOWANE MALAMI NAKE SAURARON KARATUN SA SOSAI BA WATA KILA SABODA YAYI KARATUN ZAURE YA SAMU TARBIYYA TA MALAMAN ZAUREN.
2 - YA KWARE A HARKAR HISBAH DOMIN YAYI SHEKARU YANA SHUGABANCIN TA, DON HAKA, BA WAI BABU MALAMAN DA S**A FISHI BANE, A A KWAREWA A AIKIN HISBAH DA YANDA YAKE BADA GUDUNMAWA A HUKUMAR SABODA DADEWA DA YAYI, SHI YASA GWAMNATI BATA SAN RABUWA DA SHI, DOMIN (PRACTICE MAKE A PARFECT )
3 - YARON MADUGU NE, KAMAR YANDA ABBA YAKE YARON MADUGU, DON HAKA DOLE NE ABBA YA GIRMAMA WANNAN ALAQAR, DUKDA ABINDA YA FADA BA KUSKURE BANE, DOMIN SHI DA KANSA DAURAWA YACE : ZA SU YIWA YAN HISBAH TRAINING SABODA KURAKUREN DA AKE SAMU KUMA YACE : ZAMU KIYAYE DOKA,
4 - IDAN AKA BARI YAYI MURABUS YAN ADAWA ZA SUYI AMFANI DA WANNAN DAMAR SUYIWA GWAMNATI ME CI ILLA, BISA AL'ADAR YAN KWANKWASIYYA DA NA SANI, BASU CIKA BARI MASOYI YA ZAMA MAKIYI BA SE IN ABIN YA GAGARA,
5 - YAN IZALA SUN HADE KAN SU DOMIN SUNFI KOWA SANIN AMFANIN SA A HUKUMAR DOMIN MUNA DA MUTANE A HISBAH MUN SAN IRIN ROMON DEMOKORADIYYYAR DA AKE SHARBA, KUMA AKWAI DAMAMMAKI DA YAWA DA SUKE SAMU, DAN HAKA BAZA SU YARDA YAYI MURABUS BA, KUMA HAKAN DA S**AYI ABUNE ME KYAU, DA WASU NE DA MURNA ZA SUYI IDAN YACE YAYI MURABUS.
DARASIN DA NA KOYA:-
1 - MAFI YAWAN MASU YIN WA'AZI BA SA SO AYI MUSU WA'AZI.
2 - WASU YAN SIYASAR SUNFI FIFITA SIYASAR SU AKAN ADDININ SU
3 - IDAN GWAMNA YABA MUTUM MUKAMI KO DA YAGA KUSKURE KADA YAI MASA GYARA A BAINAR JAMA'A.
Allah ya gyara mana garin mu Allah ya taimaki gwamna da mukarraban sa, shi kuma DAURAWA Allah yayi ruqo da hannun sa yaci gaba da yin abinda ze kawo gyaruwa al'ummar mu.