AUREN SUNNA

AUREN SUNNA Muna karbar shawara domin samun mafita akan Rayuwar Aure. Muna hada Auren ma.

02/10/2023

Yadda Za Ki Koya wa Mijinki Ko Matarka Wasanni.

Wasannin ma’aurata Iri-iri ne. Suna ƙara danƙon soyayya da samun biyan bukata. Suna sa biyayya har ma da mallaka
Rashin su kuwa, na sa ɗaya daga cikin ma’aurata ya zauna cikin sha’awa, da kunci, da rashin natsuwa, har ma ya kai ga ƙiyayya. Ko ma rabuwar ma’aurata.

Ire-iren wasannin sun haɗa da shafa wasu sassan jiki a hankali. Yin sumba ( Kiss) na labba, da runguma , da yin amfani da baki/harshe a wasu sassan jiki. Da hura iska a kunne. Da dai sauransu.

Amma fa runguma da sumbata ba za su yiwu ba. Sai dai da wanka, wanke baki da fesa turare.

Idan miji/ ko mata ta ji kana wari. Za ka ga kawai tana ƙin kusantar ka, b***e wasanni.

Idan aka jarrabe ki da mijin da bai iya wasa ba. Ko matar da ba ta iya wasa ba. To yakan sa a ji an gaji da juna.

HANYOYIN KOYAR DA WASANNI
1- Ban da ɓata rai, da ƙorafi , da nunawa wanda ba ya wasan shi/ ita ‘yar ƙauye ce.

2- Kai/ke mai koyar da wasan zai fara ne da maganganu masu gayyato sha’awar mijinki. Da yaba masa yana burge ki a shimfiɗa ko da ba hakan ba ne kuwa.

3 – Mai koyarwar ya dinga ɗauko hannun miji/ mata yana sawa a inda yake so a jikinsa. Domin shafa…

4 – Ki kai abin da k**e so ga bakin mijinki. Kai ma ka kai abin da kake so ga bakinta..

5 – Ba da labarin irin daɗin da ake ji idan akai Miki/maka abu kaza.

6 – Bayar da umarni, amma fa cikin lumshe ido da sigar buguwa/maye na kalar wasan da ake so ga mijinki ko matarka. Kallon wannan yanayin naka, zai sa nan da nan a yi abin da aka umarta.

Zai fi kyau ga ma’aurata ma a kowanne lokaci za ku rabu, ko ku ka hadu. To a fara da sumbatar juna.
Nana Aisha ta ce: “Manzon Allah (S.A.W) yana sumbatar matarsa idan zai fita. (Abu-Dawud).

A ƙarshe ya zama tilas ga ma’aurata, su kula da gabatar da wasanni kafin shimfiɗa. Domin da yawa ma’aurata ba sa samun gamsuwa in babu wasanni. Hakan na haifar da matsaloli da yawa ga su Ma’aurata.

Wallahu A’alam

01/10/2023

Daga cikin abubuwan da ke hana jin daɗi da lalata zamantakewar aure akwai :-

💔 Qarancin tsoron Allah

💔 Qarancin yarda da qaddara mai kyau da marar kyau

💔 Rashi ko qarancin tawakkali.

💔 Qarancin sanin ilimin zamantakewar aure

💔 Rashin ingantaccen tattaunawa ( lack of communication)

💔 Financial problems

💔 Rashin ganin girma da mutuncin juna (Lack of mutual respect )

💔 Infidelity

💔 Lack of honesty ( rashin gaskiya)

💔 Lack of trust ( rashin yarda)

💔 Emotional negligence ( watsi da lura da buqatun juna)

💔 Emotional withdrawal ( banzatarwa, kyaliya)

💔 Physical and sexual withholding or negligence

💔 Lack of boundaries ( rashin sanya iyaka )

💔 Shishshigin wasu a cikin aure ( 3rd party interferance)

💔 Lack of compromise ( qaranci ko rashin sadaukarwa)

💔 Qarancin yabo da godiya ( lack of appreciation)

💔 Yawan qorafi

💔 Yawan Kushiya

💔 Qin karɓa da gyaran kuskure/laifi

💔 Riqo da yawan fushi

💔 Girman kai

💔 Taurin kai

💔 Too much negativity

Matuqar zamu bar wadannan suna tasiri a cikin rayuwar auren mu tabbas zaiyi wuya mu samu jin dadi da zaman lafiya a gidajen mu.

✍️ Fatimah Chikaire

KARIN BAYANI GA MASU NEMAN AUREJama'a barkanmu da wannan lokacin. Akwai mutane da yawa suna son su tura profile nasu dom...
17/09/2023

KARIN BAYANI GA MASU NEMAN AURE

Jama'a barkanmu da wannan lokacin. Akwai mutane da yawa suna son su tura profile nasu domin neman aure, toh amma suna jin kunya. Wasu mutanen kuma suna jin tsoron kada a tona musu asiri.

Toh Jama'a, gaskiyar magana dai shine babu zancen kunya wajen neman aure, muddin mai neman aure na da bukatan yin hakan.

Zancen sirri kuma ina mai tabbatar muku da cewa duk duniya babu mai karanta saƙonninku sai ni daya tilo. Ko iyalina basu da daman ganin saƙonninku, ballantana su karanta. Saƙonninku amana ne mai muhimmanci wadda dole na kare daidai iya karfina.

Jama'a inason ku fahimci wannan aikin lada ne mukeyi. Bamu da anniyan karban ko sisin kwabo daga masu neman auren. Ladanmu yana wajen Ubangiji Allah Madaukakin Sarki.

Toh Jama'a Allah Ya daafa mana. Tabbas, wannan aikin ya dau haske. Alhamdulillah 🙏

16/09/2023

Mata ku sani haramun ne da ayan Al’Qur’ani mai girma miji ya nemi matar sa ta dubura ko a yayin da take jinin al’ada. Ba’a yarda ki masa biyayya ba, ba’a yarda ki kyale shi yayi yadda yake so ba. Idan kuma kika yarda ke ma kunyi tarayya da shi a cikin sabon Allah. Wallahi zunubi ne mai girma kuma yana cutar da rayuwar mace tare da haddasa mata cututtukan da ba’asan kan su ko maganin su ba.

Allah ya mana tsari daga aikin nadama da da nasani.

BAFILATANAN PATASKUM MAI SON AUREAssalamu alaikum Jama'a. Sunana Aisha, kuma ni bazawara ce na taba aure. Ina zaune a po...
14/09/2023

BAFILATANAN PATASKUM MAI SON AURE

Assalamu alaikum Jama'a. Sunana Aisha, kuma ni bazawara ce na taba aure. Ina zaune a potiskum Jahar Yobe. Shekaru na 30. Ina da yara biyu. Shekarunsu 7 da 11.

Ina da diploma a Public Administration yanzu haka. Ina da ilimin addini daidai gwargwado. A siffa na ni baqa ce. Ina da tsawo kuma ina da dan jiki.

Reference Number: Aisha-1/14/09/24
First Name: Aisha
Gender: Female
Tribe: Fulani
Location: Potiskum
State of origin: Yobe State
Age: 30yrs
Blood group: O+
Genotype: AA
Health status: Healthy
Marital status: Divorced
No.of kids: Two kids
Height: Tall
Body size: Chubby
Complexion: Chocolate
Education status: Diploma in Public Administration administration
Occupation: Unemployed
Religious ideology/Akida: Muslimah

Ina son miji dogo me dan kiba daidai gwargwado. Kuma me shekaru ba yaro ba. Shekarunsa su kasance k**ar 40 - 50.

Ba ruwana da ko yanada mata ko babu. Amma ya zama me k**a hannuna zuwa Aljanna. Ban damu da kabilar sa ba. Muhimmancin shine ya kasance Musulmi, kuma sa,arsa bata sabawa Addinin Musulunci ba.

Domin samun karin bayani game da wannan advert, ku bimu a shafinmu na JAKAR MAGORI

https://www.facebook.com/cupshausa
Email: jakarmagori@outlook.com
WhatsApp: +44 7438798343

12/09/2023

Na zauna a Staff Room sai n ji an kaɗa ƙararrawar shiga Aji. Daidai wannan lokacin na zuba Shayi zan fara sha. Bisa ƙa'ida da dokar makaranta, in aka kaɗa ƙararrawa wajibi ne kowane Malami ya shiga Aji. Dole ta saka na haƙura da shayin saboda zafi.

Da na fito waje sai naga wani ma'aikacin shara, na yi masa murmushi na ɗauki shayi na ba shi. Sai ya zo bayan an tashi daga makaranta ya ce, shekarata biyar ina aiki a wajen nan, ba wanda ya taba yi mini murmushi b***e ya bani kofin shayi...!

Malami ya ce, babu komai, ai girmamawa ce ta sa na baka, mu muslumai muna girmama mutane da kuma mutunta su musamman a wajen nema Halal.

Wannan mai sharar sai ya ce, ko kasan digiri na 2! Wahalar rayuwa ce d kuma rashin aikin yi ta sanya na karbi aikin share-share na ke yi....!

Malami y yi mamaki, ya ce, tun da Juma'a ana tashi da wuri daga aiki; kazo gidana sai mu tattauna.

Da yazo, sai y ɗakko wasu mas'aloli a ilimin lissafi, abin mamaki ma'aikacin sharar nan ya amsa gaba ɗaya! Bayan gajeriyar tattaunawa ya fuskanci lalle wannan mutum y yi karatu amma yake aikin shara.

Ya ce, ban taba ganin wanda ya yi mini murmushi kuma ya bani abu a wajen aiki ba in ba kai ba, don kowa ya raina sana'ar da nake yi, yana ganina a wulaƙance, a ƙasƙance. Haƙiƙa addininku akwai tarbiyya a ciki da kuma tausayin al'umma. Ka sanar da ni yadda zan shiga addinin...!

"Murmushi da kuma Kofin Shayi" sun zama sanadiyyar musuluntarsa...

Ma'aiki Sallallahu alaihi wa Sallama ya ce: "Kar ku raina kyakkyawan aiki komai ƙanƙantarsa, ko da kuwa ka yi faran-faran ne ga ɗan uwanka"

11/09/2023

NEMAN AURE!

Assalamu Alaikum. My name is Fatima from Kaduna State Nigeria, a graduate. I am 30 years old.

Reference: Fatima-1/11/09/23
First Name: Fatima
Gender: Female
Tribe: Hausa/Fulani
Location: Abuja
State of origin: Kaduna
Age: 30yrs
Blood group: O+
Genotype : AS
Health status: Healthy
Marital status: Single and searching
No.of kids: No kids
Height: Tall
Body size: Chubby
Complexion: Chocolate
Educational status: BSc Political Science
Occupation: Unemployed
Religious ideology/Akida: A Muslimah

Interested in: A God fearing man, working or into business, caring, loving and ready to settle down anytime soon in Kaduna, Katsina, Sokoto or Abuja.

In zan samu wanda yake aiki a kasar waje ma Ina so. Mai addini ko yoruba ne. In dai zai kula dani tsakanin shi da Allah.

He should be 38 to 45 of age. I don’t have Hadda, but Ina aji 6 islamiyya zamuyi sauka February next year InshaAllah. Kuma Ina da Addini daidai gwargwado.

Nafito gidan mutunci gidan sarauta a Zazzau. Mahaifi na sa nanene a jahar mu. Sister dina duk sunyi aure harda kani nice dai na samu Jikiri. Nagode 🙏🙏🙏

Domin samun karin bayani game da wannan advert, ku bimu a shafinmu na JAKAR MAGORI

https://www.facebook.com/cupshausa
Email: jakarmagori@outlook.com
WhatsApp: +44 7438798343

Wannan shafin mun kirkiro shi ne domin tallafawa mata, da zawarawa, da marayunmu. Allah Ubangiji ka daafa mana. Amin Ya Rabbi.

A Tarbiyya ta Addini wajibi ne sai Mace ta samu izinin Mijinta kafin fita Unguwa, koda ace lekawa kofar Gida ne. Fatan z...
10/09/2023

A Tarbiyya ta Addini wajibi ne sai Mace ta samu izinin Mijinta kafin fita Unguwa, koda ace lekawa kofar Gida ne. Fatan zamu rinka bin dokokin Aure domin a zauna lafiya.
Amma wata mara kunya tana ganin hakan ma wai k**ar kauyanci ne, saboda karyar wayewa. Ina wayewa a wurin sabawa Allah, dakuma abokin zama?

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AUREN SUNNA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share