16/10/2023
ABINDA KE HANA MATASA CIGABA.
Rayuwar matashi tamkar rayuwar jinjirin farin wata ne wanda kullum haskensa kara haske yake har zuwa daren 14 wanda daga nan ne zai dinga raguwa.
Kamar yadda hasken farin wata ke haskakawa MATUKA a daren 14, to haka rayuwar mutum tafi haskaka a lokacin yana matashi.
Ka kula da kyau da zarar ka kai shekara 20 to ka shiga lokacin da tauraronka ke haskakawa don haka kana da wata shekara 20 din wanda ya yi daidai da shekara 40 idan an hada.
Sai dai mafi yawan mutane s**an kasa AMFANA da wannan LOKACIN sai bayan lokacin ya kare sai su dinga kokarin aikata abinda ya KAMATA .
Babban abinda ke hana matasa cigaba shine: KOKARIN BURGEWA MUTANE.
Kokarin Burge mutane YANAYI ne da ke sanya matashi aikata abinda bashi da FA'IDA ga rayuwarsa. Yanayi ne dake TUNZURA matashi ya bata lokaci akan aikata abinda zai CUTAR da rayuwarsa. Yanayi ne dake sanya matashi kokarin mallakar abinda ba zai masa AMFANI ba.
Mafi yawan matasa suna aikata wani abu koda abin ba zai amfane su ba indai zasu burge abokai ko yan mata to shikenan.
Kullum KOKARINSA yaga ya BURGE abokansa hakan yasa yana neman kudi amma bashi da tanadi. Kokarin burge yan mata yake hakan yasa ya kasa yin SANA'A duk da yana zaman banza. Kokarin burge kowa yake shiyasa yake rayuwa irinta CANDLE , yana kona kansa domin haskaka WANINSA .
Lokaci na tafiya, karfi na raguwa sannan RAYUWA na karewa amma shi kokarin burge mutane yake ya manta da ya gina rayuwarsa saboda gaba. Sai karfi ya kare, tsufa ya zo masa sannan hankalin dole yazo sai ya fara kokarin gina rayuwarsa.
Baka gina rayuwarka a daidai lokacin da kake da BLOCK kuma kake da CEMENT ba sai Ruwan kwaɓa yashi ya gagare ka sannan ka fara kokarin ganin ka gina rayuwarka.
Haba! Dan uwana tashi ka gina rayuwarka yanzu tun kafin ka rasa filin gina rayuwar ballantana Block da cement.
KA DAUKI BIRO DA TAKARDA KA LISSAFAWA KANKA ABUBUWA NAWA NE KAKE AIKATAWA YANZU DOMIN KASAN ZASU AMFANE KA
COPIED