30/12/2025
KOWANE TSUNTSU KUKAN GIDANSU YAKEYI
Rubutawa: Abdullahi Hassan, Potiskum
Waka baiwa ce da Allah ya horewa wasu, wadda ke nuna hikimar iya tsarawa da rerawa. Tsawon tarihi da zamani, waka tana tafiya daidai da kowane lokaci da irin salon da yanayi ya bukata.
A adabin Larabci, ana raba mawaƙa ta hanyoyi daban-daban, amma rarrabuwa mafi shahara da sauƙin fahimta ita ce rabe-rabe guda huɗu: zamanin Jahiliyya, zamanin Musulunci, zamanin Umawiyya, da zamanin Abbasiyya.
Wannan rarrabuwa ba wai kawai ta dogara da lokaci ba, har ma tana bayyana yanayin tunani, akida, da manufar waƙa a kowane zamani.
Mawakan zamanin Jahiliyya sun shahara wajen rera waƙoƙin alfahari, jarumta, soyayya da yaƙi, abin da ya dace da rayuwar wancan lokaci mai cike da ƙabilanci, faɗa da girman kai. Daga cikin fitattun mawakan wannan zamani akwai: Imru’ul-Qais, Antara bn Shaddad, da Zuhair bn Abi Sulma. Duk lokacin da aka ambaci waɗannan sunaye, abu na farko da ke zuwa zuciya shi ne duhun jahiliyya da rayuwar da ba ta da hasken shiriya.
Da zuwan Musulunci kuma, waƙa ta samu sauyi mai girma, musamman a zamanin Annabi s,a,w, Mawakan wannan zamani sun mayar da hankalinsu wajen kare Musulunci, inganta ɗabi’a da tabbatar da tauhidi. Ba a yin waƙa sai wadda take da alaƙa da sakon Annabi s,a,w, da gina al’umma bisa gaskiya da imani. Daga cikin fitattun mawakan wannan zamani akwai Hassan bn Thabit da Ka‘ab bn Zuhair.
A wannan lokaci, ba a yarda a wake wani mutum saboda matsayi ko suna ba, kuma babu wani sahabi da ya kai matsayin da za a rera masa waƙa don girmamawa ko kare shi daga maƙiyansa.
A zamanin Umawiyya kuwa, lokacin mulkin Banu Umayyah, an sake ganin dawowar wani salo na jahiliyya, inda waƙa ta koma zagi da martani (naqā’iḍ), siyasa da ƙabilanci. A wannan zamani ne aka ga yaƙin kalmomi tsakanin mawaka, tare da yabon sarakuna da zambo ga abokan gaba. Fitattun mawakan wannan zamani sun haɗa da Jarir, Farazdaq, da Akhtal, waɗanda s**a yi fice wajen rigingimun waƙoƙi da nuna fifikon ƙabila da siyasa.
Zamanin Abbasiyya kuma ya zo ne da bunƙasar ilimi da adabi, lamarin da ya sa waƙa ta faɗaɗa zuwa fannoni da dama. Mawakan wannan zamani sun fi karkata zuwa hikima, falsafa, nishadi da soyayya, tare da zurfin tunani da ingantaccen salo. Daga cikin shahararrun mawakan wannan zamani akwai Abu Nuwas, Al-Mutanabbi da Abu Tammam.
A ƙarshe, wannan bayani yana nuni da cewa ana iya gane mawaƙi ne ta abin da yake wakewa da manufar waƙoƙinsa. Akwai mawaƙan addini, kuma akwai mawaƙan jahiliyya, kuma kowane nau’i yana bayyana ne ta ayyukansa. Waƙa, a kowane zamani, madubi ce da ke nuna halin da al’umma ke ciki da alkiblar tunaninta.