MAGANIN CIWON KAI DA JIRI KO HAJIJIYA KO NA TURENE KO SIHIRI DA IZININ ALLAH...
Assalamu-Alaikum da fatan kuna lafiya.? Duk Wanda ya ke fama da ciwon kai mai tsanani
ko jiri
ko hajijiya
ko ciwon kan na bare daya
ko idan zai yi sujjada ya ji kansa kamar zai fado kasa
idan kuma hajijiya ce yaji kamar garin zai fado masa ya ji duk garin yana juya masa an sha maganin anyi na asibiti,
amma shiru ba a samu sauki ba
to don Allah a daure a jarraba wan-nan sirrin na ganyen tumfafiya na rantse da Allah ciwon kan ko na gado ne an rabu da shi kenan da izinin Allah
GA YADDA AKE WAN-NAN SIRRIN KAMAR HAKA...
Ana zuwa kowacce rana da safe ko da yamma aje gindin bishiyar tumfafiya a debo ganyenta amma ba a cirowa Wanda ya fado kasa ake dauka
kada a ciro ganyen san-nan Wanda ya bushe ya fado kasa da kansa shi ake dakkowa sai azo amarmasheshi da hannu ba a dakawa
da hannu ake marmashewa sai a kasa shi gida bakwai sai ayi alwala ayi hayakin sai abude baki da hanci hayakin ya shiga sosai ashakeshi ya shiga sosai, kwana bakwai a Jere
na rantse da Allah ciwon kai ko na aljanu ne wallahil-azim an rabu da shi kenan da izinin Allah wallahi wan-nan sirrin mujarrabunne don Allah Ku daure Ku jarraba Ku ga ikon ALLAH...
SHARADI. Ba a zuwa debowa da rana misalin sha biyu na rana ba a zuwa da kuma da daddare ana zuwa ne da safe da kuma yamma kafin sallar magriba san-nan ba a ciro ganyen kuma baa dakawa..Saboda shu-umar aba ce wallahi a kiyaye lokutan da muka fada da kuma abubuwan da muka ce.