11/09/2024
Akwai amfani da kuma zunzurutun muhimmanci ace mace tasan wani abu akan alimun koda yake k**ar yanda zakije shagon islamic medicine ki sayi al miski haka zakije wajen masu kayan koli ki Basu Naira 50 abaki to amma ba'a nan matsalar takeba yanda zakiyi aiki dashi ya amfane ki amatsayin ki na matar aure koma me shirin yin aure,
Idan kina ƙaiƙayin gaba bayan kinyi shaving wato bayan kin aske gashin gabanki to ki tafasa alimun kiyi tsarki da ruwan da ɗuminsa ko kuma bayan kin tafasa ruwan ki samu tsumma me tsafta ki saka a ruwan saiki rinƙa matsa ruwan a gabanki ko kuma ki dunduma wato kina dandannawa,
Alimun da lemon tsami suna kashe ƙwayoyin cuta Musamman a ban ɗaki idan aka jiƙa ruwan da lemon tsami aka wanke zai hana kamuwa da cututtukan da ake ɗauka a banɗaki,
Masu matsalar dandruff suyi Garin sa suna shafawa a wajen haka suma wadanda suke saɓa ajiki tabbas ya tabbata shafa Garin sa k**ar yanda ake shafawa powder zai temaka sosai wajen goge shi amma amfi amfani da jansa wajen magance mataalar dandruff,
Warin baki wanda ke fitowa daga ciki wanda asalinsa daga body odor yake ana haɗa alimun da gawayi ayi garin su a kwaɓa da ruwa ana goge baki dashi,
Domin tsaftar gaban mace lokacin data haifu kafin jini ya ɗauke ta rinƙa tafasa shi da lemon tsami tana tsarki dashi,
Koda yake alimun akwai fari akwai ja kowanne daga ciki aka samu anayi amma akwai ƙalubale guda ɗaya akan farinsa wanda yafin jan tasiri wanda hakan yasa wasu matan s**a haramtawa kansu aiki da alimun kwatakwata, matsalar shine yana ɗauke da sinadarin kashe duk wata ƙwayar cuta, to a ka'ida irin wannan maganin sakashi a gaba yana kashe ɗanɗanon da yake gaban mace,
Wannan dalilin ya ragewa alimun farin jini dukda amfani dayake dashi domin a bayyane yake duk abunda zai ragewa mace muhibba da matantaka ajikinta tana iya ƙaurace masa.