30/08/2018
DALILIN DA YA SA ANNABI (SAW) YA YI HU'DUBA A GHADEER KHUM!!!
LALLAI YA TABBATA ANNABI (SAW) YA TSAYA A WANI WURI DA AKE KIRANSA "GHADEER KHUM" A KAN HANYARSA TA KOMAWA GIDA MADINA DAGA MAKKA, BAYAN GAMA HAJJINSA NA BAN-KWANA, ANNABI (SAW) TARE DA SAHABBANSA, YA YI ZANGO NE A WANNAN WURI SABODA DOGUWAR TAFIYA IRIN TA WANCAN LOKACI TA GAJI YA DA ZANGO, SABODA TAFIYA CE DA AKE YINTA A CIKIN KWANAKI KO MAKONNI.
LALLAI MALAMAN HADISI SUN RUWAITO RIWAYOYI MASU YAWA GAME DA ABIN DA YA FARU A "GADEER KHUM", AMMA MAFI YAWA BA SU INGANTA BA, MUSAMMAN SABODA MAK'ARYATA DA 'YAN BIDI'A DA SON RAI SUN YI WASA DA WA'DANNAN RIWAYOYI DON CUSA MUNANAN AQIDUNSU DA BIDI'O'INSU, AMMA โ ALHAMDU LILLAHI -, CIKIN IKON ALLAH, ALLAH YA TANADI MALAMAN HADISI MASU TANKA'DE DA RERAYA, INDA S**A TANKA'DE ABIN DA YA INGANTA, DAGA RIWAYOYIN MAK'ARYATA DA GUR'BATATTUN MARUWAITA.
INGANTACCEN NASSIN HADISIN GADEER KHUM:
(1) IMAMU MUSLIM YA RUWAITO A CIKIN SAHIHINSA YA CE :
6378 - ุญุฏุซูู ุฒููุฑ ุจู ุญุฑุจ ูุดุฌุงุน ุจู ู
ุฎูุฏ ุฌู
ูุนุง ุนู ุงุจู ุนููุฉ ูุงู ุฒููุฑ ุญุฏุซูุง ุฅุณู
ุงุนูู ุจู ุฅุจุฑุงููู
ุญุฏุซูู ุฃุจู ุญูุงู ุญุฏุซูู ูุฒูุฏ ุจู ุญูุงู ูุงู ุงูุทููุช ุฃูุง ูุญุตูู ุจู ุณุจุฑุฉ ูุนู
ุฑ ุจู ู
ุณูู
ุฅูู ุฒูุฏ ุจู ุฃุฑูู
ููู
ุง ุฌูุณูุง ุฅููู ูุงู ูู ุญุตูู ููุฏ ูููุช ูุง ุฒูุฏ ุฎูุฑุง ูุซูุฑุง ุฑุฃูุช ุฑุณูู ุงููู -ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
- ูุณู
ุนุช ุญุฏูุซู ูุบุฒูุช ู
ุนู ูุตููุช ุฎููู ููุฏ ูููุช ูุง ุฒูุฏ ุฎูุฑุง ูุซูุฑุง ุญุฏุซูุง ูุง ุฒูุฏ ู
ุง ุณู
ุนุช ู
ู ุฑุณูู ุงููู -ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
- - ูุงู - ูุง ุงุจู ุฃุฎู ูุงููู ููุฏ ูุจุฑุช ุณูู ููุฏู
ุนูุฏู ููุณูุช ุจุนุถ ุงูุฐู ููุช ุฃุนู ู
ู ุฑุณูู ุงููู -ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
- ูู
ุง ุญุฏุซุชูู
ูุงูุจููุง ูู
ุง ูุง ููุง ุชููููููู.
ุซู
ูุงู ูุงู
ุฑุณูู ุงููู -ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
- ููู
ุง ูููุง ุฎุทูุจุง ุจู
ุงุก ูุฏุนู ุฎู
ุง ุจูู ู
ูุฉ ูุงูู
ุฏููุฉ ูุญู
ุฏ ุงููู ูุฃุซูู ุนููู ููุนุธ ูุฐูุฑ ุซู
ูุงู ยซ ุฃู
ุง ุจุนุฏ ุฃูุง ุฃููุง ุงููุงุณ ูุฅูู
ุง ุฃูุง ุจุดุฑ ููุดู ุฃู ูุฃุชู ุฑุณูู ุฑุจู ูุฃุฌูุจ ูุฃูุง ุชุงุฑู ูููู
ุซูููู ุฃูููู
ุง ูุชุงุจ ุงููู ููู ุงููุฏู ูุงูููุฑ ูุฎุฐูุง ุจูุชุงุจ ุงููู ูุงุณุชู
ุณููุง ุจู ยป. ูุญุซ ุนูู ูุชุงุจ ุงููู ูุฑุบุจ ููู ุซู
ูุงู ยซ ูุฃูู ุจูุชู ุฃุฐูุฑูู
ุงููู ูู ุฃูู ุจูุชู ุฃุฐูุฑูู
ุงููู ูู ุฃูู ุจูุชู ุฃุฐูุฑูู
ุงููู ูู ุฃูู ุจูุชู ยป. ููุงู ูู ุญุตูู ูู
ู ุฃูู ุจูุชู ูุง ุฒูุฏ ุฃููุณ ูุณุงุคู ู
ู ุฃูู ุจูุชู ูุงู ูุณุงุคู ู
ู ุฃูู ุจูุชู ูููู ุฃูู ุจูุชู ู
ู ุญุฑู
ุงูุตุฏูุฉ ุจุนุฏู. ูุงู ูู
ู ูู
ูุงู ูู
ุขู ุนูู ูุขู ุนููู ูุขู ุฌุนูุฑ ูุขู ุนุจุงุณ . ูุงู ูู ูุคูุงุก ุญุฑู
ุงูุตุฏูุฉ ูุงู ูุนู
MUSLIM YA RUWAITO DAGA ZAIDU BN ARQAM (RA) YA CE:
"WATA RANA ANNABI (SAW) YA TSAYA A CIKINMU YANA MAI HU'DUBA A WANI RUWA (KWARIN RUWA), ANA KIRANSA "KHUMMUN", WANDA YAKE TSAKANIN MAKKA DA MADINA, SAI YA YI GODIYA MA ALLAH, YA YI MASA YABO, SAI YA YI WA'AZI YA TUNATAR DA MUTANE, SA'ANNAN SAI YA CE:
"BAYAN HAKA: KU SAURARA YA KU MUTANE, LALLAI NI MUTUM NE, KUMA 'DAN AIKEN UBANGIJINKU YA YI KUSA YA ZO GARE NI, NI KUMA IN AMSA MASA, LALLAI ZAN BAR WASU ABUBUWA MASU NAUYI GUDA BIYU A CIKINKU, NA FARKONSU SHI NE LITTAFIN ALLAH, LALLAI AKWAI SHIRIYA DA HASKE A CIKINSA, DON HAKA KU K**A LITTAFIN ALLAH, KUMA KU YI RIK'O DA SHI".
SAI YA ZABURAR A KAN LITTAFIN ALLAH, KUMA KWA'DAITAR A KANSA, SAI YA CE:
"SAI KUMA IYALAN GIDANA, INA TUNA MUKU ALLAH A KAN IYALAN GIDANA, INA TUNA MUKU ALLAH A KAN IYALAN GIDANA, INA TUNA MUKU ALLAH A KAN IYALAN GIDANA".
SAI HUSWAIN YA CE: SU WANENE IYALAN GIDAN NASA YA ZAID, SHIN MATANSA BA IYALAN GIDANSA BA NE?
SAI YA CE: MATANSA SUNA CIKIN IYALAN GIDANSA, AMMA IYALAN GIDANSA (DA AKE NUFI A NAN) SU NE WA'DANDA AKA HARAMTA MASU CIN SADAKA A BAYANSA.
SAI YA CE: SU WANENE SU?
SAI YA CE: SU NE; IYALAN ALIYU, DA IYALAN AQILU, DA IYALAN JA'AFAR, DA IYALAN ABBAS.
SAI YA CE: DUKA WA'DANNAN AN HARAMTA MUSU CIN SADAKA?
SAI YA CE: EH".
(2) AL- IMAMU AHMAD YA RUWAITO A CIKIN AL- MUSNAD:
641 - ุญุฏุซูุง ุงุจู ูู
ูุฑุ ุญุฏุซูุง ุนุจุฏ ุงูู
ููุ ุนู ุฃุจู ุนุจุฏ ุงูุฑุญูู
ุงูููุฏูุ ุนู ุฒุงุฐุงู ุฃุจู ุนู
ุฑุ ูุงู: ุณู
ุนุช ุนููุงุ ูู ุงูุฑุญุจุฉ ููู ููุดุฏ ุงููุงุณ: ู
ู ุดูุฏ ุฑุณูู ุงููู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ููู
ุบุฏูุฑ ุฎู
ุ ููู ูููู ู
ุง ูุงู ุ ููุงู
ุซูุงุซุฉ ุนุดุฑ ุฑุฌูุงุ ูุดูุฏูุง ุฃููู
ุณู
ุนูุง ุฑุณูู ุงููู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ููู ูููู: " ู
ู ููุช ู
ููุงู ูุนูู ู
ููุงู "
IMAMU AHMAD YA RUWAITO TA HANYAR ZAZAN YA CE: NA JI ALIYU (RA) A RAHABA (WANI WURI NE A GARIN KUFA), YANA MAGIYA WA MUTANE:
"WANENE YA HALARCI LOKACIN DA MANZON ALLAH YAKE FA'DIN ABIN DA YA FA'DA A RANAR GADEER KHUM?
SAI MUTANE GOMA SHA UKU (13) S**A TASHI, SAI S**A BA DA SHAIDAN CEWA; SUN JI MANZON ALLAH (SAW) YANA CEWA:
"DUK WANDA NA KASANCE MASOYINSA NE, TO ALIYU MA MASOYINSA NE".
WANNAN HADISIN HASAN NE.
(3) AL- IMAMU AL - TIRMIZIY YA RUWAITO A CIKIN SUNAN NASA, DA 'DABARANIY A CIKIN AL- KABEER:
3713- ุญุฏุซูุง ู
ุญู
ุฏ ุจู ุจุดุงุฑ ุ ูุงู : ุญุฏุซูุง ู
ุญู
ุฏ ุจู ุฌุนูุฑ ุ ูุงู : ุญุฏุซูุง ุดุนุจุฉ ุ ุนู ุณูู
ุฉ ุจู ูููู ุ ูุงู : ุณู
ุนุช ุฃุจุง ุงูุทููู ูุญุฏุซ ุ ุนู ุฃุจู ุณุฑูุญุฉ ุ ุฃู ุฒูุฏ ุจู ุฃุฑูู
ุ ุดู ุดุนุจุฉ ุ ุนู ุงููุจู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ูุงู : ู
ู ููุช ู
ููุงู ูุนูู ู
ููุงู.
ูุฐุง ุญุฏูุซ ุญุณู ุบุฑูุจ.
ููุฏ ุฑูู ุดุนุจุฉ ุ ูุฐุง ุงูุญุฏูุซ ุ ุนู ู
ูู
ูู ุฃุจู ุนุจุฏ ุงููู ุ ุนู ุฒูุฏ ุจู ุฃุฑูู
ุ ุนู ุงููุจู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ูุญูู.
ูุฃุจู ุณุฑูุญุฉ ูู : ุญุฐููุฉ ุจู ุฃุณูุฏ ุตุงุญุจ ุงููุจู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
.
DAGA ZAIDU BN ARQAM (RA), DAGA ANNABI (SAW) YA CE:
"DUK WANDA NA KASANCE MASOYINSA NE, TO ALIYU MA MASOYINSA NE".
WANNAN HADISIN INGANTACCE NE.
* WANNAN KAWAI SHI NE ABIN DA YA INGANTA NA HADISIN GADEER. ANNABI (SAW) YA YI HU'DUBA A WANI KWARIN RUWA, WANDA AKE KIRA DA "KHUMMUN", WANDA YAKE TSAKANIN MAKKA DA MADINA. SAI YA YI YABO DA GODIYA WA ALLAH, YA YI WA'AZI YA TUNATAR, SA'ANNAN YA YI ISHARA ZUWA GA KUSANTOWAN LOKACIN RASUWARSA, SAI YA YI WASIYYA DA RIK'O DA LITTAFIN ALLAH, DA KIYAYE HAKKOKIN IYALAN GIDANSA.
* SA'ANNAN A CIKIN WANNAR KHU'DUBA DA YA YI, YA YI BAYANIN MATSAYIN ALIYU (RA) A WAJENSA, SABODA K'IYAYYA DA WASU SUKE NUNA MASA, SAI YA CE:
" ู
ู ููุช ู
ููุงู ูุนูู ู
ููุงู "
"DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA TO ALIYU MASOYINSA NE".
K**AR YADDA IMAMU AHMAD YA RUWAITO DA ISNADI MAI KYAU DAGA ALIYU (RA), HAKAN NAN TIRMIZIY DA 'DABARANIY S**A RUWAITO DAGA ZAIDU BIN ARK'AM (RA) CEWA; ANNABI (SAW) YA FA'DI HAKAN. SHI KUMA ZAIDU BIN ARQAM (RA) SHI NE WANDA YA RUWAITO WANCAN HADISIN DA MUSLIM YA FITAR DA SHI, WANDA YA YI BAYANIN HU'DUBAR ANNABI (SAW) A GADEER KHUM.
TO ABIN TAMBAYA A NAN SHI NE; MENENE DALILIN DA YA SA ANNABI (SAW) FA'DI WANNAR MAGANA, DA TAKE WAJABTA SON ALIYU (RA), DA NISANTAR K'INSA DA ADAWA DA SHI??
LALLAI DALILIN DA YA SA ANNABI (SAW) YA YI WANNAR HU'DUBA, HAR YA FA'DI WANNAR MAGANA A GAME DA ALIYU (RA) A GADEER KHUM, SHI NE; KASANCEWAR TUN KAFIN ANNABI (SAW) YA FITO AIKIN HAJJI DAGA MADINA, YA AIKA ALIYU (RA) A CIKIN WATA TAWAGA A MATSAYIN SHUGABANTA ZUWA YAMAN, TARE DA WASU SAHABBAI, HAR ANNABI (SAW) YA TAFI HAJJI BA SU DAWO MADINA BA, A KAN ZA SU WUCE MAKKA SU HA'DU DA ANNABI (SAW) A CAN WAJEN AIKIN HAJJI.
SAI ALIYU (RA) DA WA'DANDA SUKE TARE DA SHI, S**A RISKI ANNABI (SAW) DA SAHABBANSA A WAJEN AIKIN HAJJI, SAI BURAIDA BIN HUSAIB (RA) YA JE WAJEN ANNABI (SAW) YANA GAYA MASA ABIN DA YA GANI A WAJEN ALIYU (RA) NA TSANANI DA KUMA 'DAUKAR BAIWA DA ALIYU (RA) YA YI DAGA CIKIN KHUMUSI, A LOKACIN SUNA TARE A YAMAN, SAI YA NAK'ASA ALIYU (RA), SAI ANNABI (SAW) YA YI FUSHI, SAI YA CE MA BURAIDA (RA):
ู
ู ููุช ู
ููุงู ูุนูู ู
ููุงู
"DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA, TO ALIYU (RA) MA MASOYINSA NE".
TO, BAYAN AN GAMA AIKIN HAJJI ANA DAWOWA SAI AKA ISO "GADEER KHUM", SAI AKA YA DA ZANGO DON A SAUKA A HUTA, SAI ANNABI (SAW) YA TASHI YA YI HU'DUBA WA MUTANE DA SUKE TARE DA SHI, A CIKI SAI YA FA'DI WANNAN HADISI:
ู
ู ููุช ู
ููุงู ูุนูู ู
ููุงู
"DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA, TO ALIYU (RA) MA MASOYINSA NE".
(1) IMAMU AHMAD YA RUWAITO YA CE:
ุญุฏุซูุง ุงููุถู ุจู ุฏูููุ ุญุฏุซูุง ุงุจู ุฃุจู ุบููุฉุ ุนู ุงูุญูู
ุ ุนู ุณุนูุฏ ุจู ุฌุจูุฑุ ุนู ุงุจู ุนุจุงุณุ ุนู ุจุฑูุฏุฉ ูุงู: ุบุฒูุช ู
ุน ุนูู ุงููู
ู ูุฑุฃูุช ู
ูู ุฌููุฉุ ููู
ุง ูุฏู
ุช ุนูู ุฑุณูู ุงููู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ุฐูุฑุช ุนููุง ูุชููุตุชูุ ูุฑุฃูุช ูุฌู ุฑุณูู ุงููู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ูุชุบูุฑ ููุงู: " ูุง ุจุฑูุฏุฉ ุฃูุณุช ุฃููู ุจุงูู
ุคู
ููู ู
ู ุฃููุณูู
ุ " ููุช: ุจูู ูุง ุฑุณูู ุงููู . ูุงู: " ู
ู ููุช ู
ููุงู ูุนูู ู
ููุงู "
DAGA BURAIDA (RA) YA CE:
"NA JE YAK'I TARE DA ALIYU (RA) A YAMAN, SAI NA GA KAUSHIN HALI A TARE DA SHI, TO A LOKACIN DA MUKA ISA WAJEN ANNABI (SAW) NA AMBACI ABIN DA ALIYU (RA) YA YI, SAI NA K'ASK'ANTA SHI (AIBANTAWA), SAI NA GA FISKAR ANNABI (SAW) TANA CANZAWA, SAI YA CE:
"YA BURAIDA, SHIN BA NI NE NA FI CANCANTA GA MUMINAI FIYE DA KAWUKANSU BA?".
SAI NA CE: EH, HAKA NE YA MANZON ALLAH.
SAI YA CE:
"DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA, TO ALIYU (RA) MA MASOYINSA NE".
WANNAN HADISIN INGANTACCE NE.
(2) KUMA IMAMU AHMAD DA HAKIM SUN RUWAITO:
ุญุฏุซูุง ูููุนุ ุญุฏุซูุง ุงูุฃุนู
ุดุ ุนู ุณุนุฏ ุจู ุนุจูุฏุฉุ ุนู ุงุจู ุจุฑูุฏุฉุ ุนู ุฃุจูู ุฃูู: ู
ุฑ ุนูู ู
ุฌูุณุ ููู
ูุชูุงูููู ู
ู ุนูู ูููู ุนูููู
ููุงู: ุฅูู ูุฏ ูุงู ูู ููุณู ุนูู ุนูู ุดูุกุ ููุงู ุฎุงูุฏ ุจู ุงููููุฏ ูุฐูู ูุจุนุซูู ุฑุณูู ุงููู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ูู ุณุฑูุฉ ุนูููุง ุนููุ ูุฃุตุจูุง ุณุจูุง ูุงู: ูุฃุฎุฐ ุนูู ุฌุงุฑูุฉ ู
ู ุงูุฎู
ุณ ูููุณู . ููุงู ุฎุงูุฏ ุจู ุงููููุฏ: ุฏููู . ูุงู: ููู
ุง ูุฏู
ูุง ุนูู ุงููุจู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ุฌุนูุช ุฃุญุฏุซู ุจู
ุง ูุงูุ ุซู
ููุช: ุฅู ุนููุง ุฃุฎุฐ ุฌุงุฑูุฉ ู
ู ุงูุฎู
ุณ . ูุงู: ูููุช ุฑุฌูุง ู
ูุจุงุจุง ูุงู: ูุฑูุนุช ุฑุฃุณูุ ูุฅุฐุง ูุฌู ุฑุณูู ุงููู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ูุฏ ุชุบูุฑ ููุงู: " ู
ู ููุช ููููุ ูุนูู ูููู "
DAGA BURAIDA YA CE:
"YA KASANCE AKWAI WANI ABU A ZUCIYATA A GAME DA ALIYU (RA), KHALID MA YA KASANCE HAKA, SAI MANZON ALLAH (SAW) YA AIKANI A CIKIN TAWAGA WACCE SHUGABANTA SHI NE ALIYU (RA), SAI MUKA SAMU BAYI, SAI ALIYU (RA) YA 'DAUKI WATA BAIWA DAGA CIKIN KHUMUSI MA KANSA, SAI KHALID YA CE: TO KA K**A SHI DA WANNAN LAIFIN.
SAI YA CE: A LOKACIN DA MUKA ZO WAJEN ANNABI (SAW) SAI NA FARA GAYA MASA ABIN DA YA FARU, SAI NA CE: ALIYU (RA) YA 'DAUKI BAIWA DAGA KHUMUSI.
TO NA KASANCE NI MUTUM NE MAI SUNKUYAR DA KAI, TO SAI NA 'DAGA KAINA, SAI NA GA FISKAR MANZON ALLAH (SAW) TA CANZA, SAI YA CE:
"DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA, TO ALIYU (RA) MA MASOYINSA NE".
WANNAN HADISIN INGANTACCE NE.
(3) WANNAN HADISIN KUWA, BUKHARI MA YA RUWAITO SHI K**AR HAKA:
ุญุฏุซูู ู
ุญู
ุฏ ุจู ุจุดุงุฑ ุญุฏุซูุง ุฑูุญ ุจู ุนุจุงุฏุฉ ุญุฏุซูุง ุนูู ุจู ุณููุฏ ุจู ู
ูุฌูู ุนู ุนุจุฏ ุงููู ุจู ุจุฑูุฏุฉ ุนู ุฃุจูู ุฑุถู ุงููู ุนูู ูุงู ุจุนุซ ุงููุจู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ุนููุง ุฅูู ุฎุงูุฏ ูููุจุถ ุงูุฎู
ุณ ูููุช ุฃุจุบุถ ุนููุง ููุฏ ุงุบุชุณู ูููุช ูุฎุงูุฏ ุฃูุง ุชุฑู ุฅูู ูุฐุง ููู
ุง ูุฏู
ูุง ุนูู ุงููุจู ุตูู ุงููู ุนููู ูุณูู
ุฐูุฑุช ุฐูู ูู ููุงู ูุง ุจุฑูุฏุฉ ุฃุชุจุบุถ ุนููุง ูููุช ูุนู
ูุงู ูุง ุชุจุบุถู ูุฅู ูู ูู ุงูุฎู
ุณ ุฃูุซุฑ ู
ู ุฐูู
DAGA BURAIDA YA CE:
ANNABI (SAW) YA AIKA ALIYU (RA) ZUWA WAJEN KHALID (RA) DON YA KAR'BI KHUMUSI, NI KUMA NA KASANCE INA K'IN ALIYU (RA), KAWAI SAI GA SHI YA YI WANKA (NA JANABA), SAI NA CE MA KHALID: SHIN BA KA GA ABIN DA WANNAN MUTUMI YA YI BA?!
TO LOKACIN DA MUKA ZO WAJEN ANNABI (SAW) SAI NA GAYA MASA ABIN DA YA FARU, SAI YA CE:
"YA BURAIDA, SHIN KANA K'IN ALIYU (RA) NE?
SAI NA CE: EH.
SAI YA CE:
"TO KADA KA K'I SHI, SABODA YANA DA RABO A CIKIN KHUMUSI FIYE DA DA BAIWAR DA YA 'DAUKA".
TO, WANNAN K'IYAYYA DA WASU DAGA CIKIN SAHABBAI SUKE YI WA ALIYU (RA) ITA CE DALILIN DA YA SA DA ANNABI (SAW) YA ZO GADEER KHUM A KAN HANYARSA TA KOMAWA MADINA, SAI YA YI HU'DUBA A CIKIN MUTANE, DON SAURAN SAHABBAI MASU ADAWA DA ALIYU (RA) SU NISANCI HAKAN, BAYAN TUN A FARKO YA KWA'BI SHI BURAIDA (RA).
SABODA HAKA WANNAN A FILI YAKE, BA WANI DALILI NE YA SA ANNABI (SAW) YA YI HU'DUBA A GADEER KHUM BA, FACE DON YA KAWAR DA K'IYAYYAR ALIYU (RA) DA WASU SAHABBAI SUKE YI MASA, DON HAKA KWATA โ KWATA BABU MAGANAR SHUGABANCI, KO KHALIFANCI, KO IMAMANCI A CIKIN HU'DUBAR DA ANNABI (SAW) YA YI A GHADEER KHUM.
WANNAN YA SA YA YI AMFANI DA KALMAR "MAULA", WACCE TAKE DADAI DA KALMAR "WALIYYI" WACCE TAKE 'DAUKE DA MA'ANAR MASOYI MAI TAIMAKO, BAI YI AMFANI DA KALMAR "WAALIY" BA, WACCE TAKE 'DAUKE DA MA'ANAR SHUGABA.
SHI YA SA YA CE:
ู
ู ููุช ู
ููุงู ูุนูู ู
ููุงู "
"DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA, TO ALIYU (RA) MA MASOYINSA NE."
BAI CE:
ู
ู ููุช ูุงููู ูุนูู ูุงููู
"DUK WANDA NA KASANCE SHUGABANSA, TO ALIYU MA SHUGABANSA NE" BA.
BAI FA'DI HAKA BA.
SABODA HAKA KWATA - KWATA HADISIN BA YANA MAGANA A KAN SHUGABANCI BA NE, ANNABI (SAW) YANA MAI DA MARTANI NE, SABODA K'ARAN ALIYU (RA) DA AKA KAWO MASA, WANDA YA K'UNSHI AIBANTA SHI DA NUNA MASA ADAWA DA K'IYAYYA.
** DON HAKA A TAK'AICE, DUK ABIN DA BA WANNAN BA, BA INGANTACCE BA NE A HADISIN GADEER, IMMA YA ZAMA K'ARIN 'YAN SHI'A NE, KO KUMA K'ARIN DA'IFAN MARUWAITA MARASA KIYAYE HADISI K**AR YADDA YAKE.