Asad Yelwa Hub

Asad Yelwa Hub PharmD student💊🩺 //Content creator📷// football lover⚽// Business man💪
(1)

‎ZUBAR RUWAN MAMA BA LOKACIN SHAYARWA BA‎-----------------------------------------------------‎‎Abin da wasu ke kira “sa...
10/05/2026

‎ZUBAR RUWAN MAMA BA LOKACIN SHAYARWA BA
‎-----------------------------------------------------

‎Abin da wasu ke kira “sanyin mama” yawanci infection ne da ke shiga breast ko hormonal problem wanda zai iya sa:

‎• Zubar ruwa daga mama
‎• Kaikayi
‎• Ciwo ko kumburi
‎• Wani lokaci wari ko zafi

‎------------------------------------------------------------

‎➡️ ALAMOMIN SANYIN MAMA

‎✔️ Zubar ruwa daga mama ba tare da shayarwa ba
‎✔️ Kaikayi a mama ko kusa da kan mama
‎✔️ Jin zafi ko nauyi a mama
‎✔️ Kumburi ko ja
‎✔️ Wani lokacin zazzaɓi idan infection ɗin ya yi tsanani

‎Wasu lokutan zubar ruwa daga mama na iya kasancewa saboda:
‎• Hormonal imbalance
‎• Infection
‎• Wasu magunguna
‎• Ko wata matsala a breast da ke buƙatar a duba sosai

‎--------------------------------------------------------

‎➡️ MAGANIN SA

‎Magani yana danganta da abin da ya jawo matsalar:
‎• Idan infection ne, ana iya bada antibiotics ko antifungal
‎• Idan hormonal problem ne, ana duba hormones
‎• A guji matsa nono akai-akai
‎• A kula da tsafta
‎---------------------------------------------------------

‎❌ Kada a riƙa amfani da magani kawai daga ji ba gani.

‎🩺 Idan kina fama da:
‎• Zubar jini daga mama
‎• Tsananin ciwo
‎• Kumburi mai tsanani
‎• Ko matsalar ta daɗe

‎Yana da kyau ki ga likita domin a gano ainihin matsalar.

‎Lafiya uwar jiki ❤️



‎ZA KA IYA AUREN MAI CUTAR HIV?‎----------------------------------------------‎‎Eh, zaka/ki iya aure, kuma zaka iya rayu...
09/05/2026

‎ZA KA IYA AUREN MAI CUTAR HIV?
‎----------------------------------------------

‎Eh, zaka/ki iya aure, kuma zaka iya rayuwa lafiya ba tare da ka kamu ba idan an dauki matakan kariya da s**a dace.

‎ABUBUWAN DA YA KAMATA AYI:

‎• Mai HIV ya rika shan magani yadda likita ya tsara (ARVs)
‎ • A dinga yin gwaji akai-akai
‎• Amfani da kariya yayin saduwa idan likita ya bada shawara
‎• Negative partner zai iya amfani da PrEP domin kariya daga HIV
‎• A bi shawarar likita kafin samun ciki ko haihuwa

Idan mai HIV yana shan magani sosai har virus din ya koma “undetectable”, yiwuwar yadawa tana raguwa sosai.
‎HIV ba karshen rayuwa bane. Ilimi da kariya sune mabuɗin zaman lafiya da lafiya a aure ❤️


‎CIWON AL’ADA‎----------------------‎‎Ciwon al’ada, wanda ake kira menstrual cramps, abu ne da ya zama ruwan dare ga mat...
08/05/2026

‎CIWON AL’ADA
‎----------------------

‎Ciwon al’ada, wanda ake kira menstrual cramps, abu ne da ya zama ruwan dare ga mata kuma yana iya hana gudanar da ayyukan yau da kullum. Yawanci ana jin ciwon a ƙasan ciki, kuma yana iya bazuwa zuwa baya ko cinyoyi.

‎Ku koyi yadda za ku rage wannan matsala a sharhina da ke ƙasa 👇🏾


‎🔑 HANYOYIN RAGE ZAFIN AL'ADA
‎-------------------------------------------------

‎1- Yin amfani da warm compress ko hot water bottle a ƙasan ciki na taimakawa wajen sassauta tsokoki da rage ciwo.

‎2- Motsa jiki mai sauƙi k**ar tafiya ko stretching na taimakawa wajen inganta zagayawar jini da rage ciwon.

‎3- Shan ruwa sosai da cin abinci mai gina jiki na taimakawa jiki ya fi jurewa lokacin al’ada.

‎5- Ana iya amfani da magungunan rage ciwo da ake samu ba tare da prescription ba idan ciwon ya yi matsakaici ko tsanani, amma a yi amfani da su yadda aka bada shawara.

‎5- Wasu hanyoyin gida da mata da yawa suke ganin suna taimakawa sun haɗa da shan abubuwan sha masu ɗumi k**ar ginger tea, rage caffeine, da samun isasshen hutu.

‎6- Yin tausa a ƙasan ciki a hankali na iya taimakawa rage rashin jin daɗi.

‎Idan ciwon yana da tsanani sosai, yana ƙaruwa lokaci zuwa lokaci, ko yana hana gudanar da rayuwa ta yau da kullum duk wata, yana da muhimmanci a ga ƙwararren ma’aikacin lafiya domin bincika ko akwai wata matsala ta daban.

‎Ciwon al’ada abu ne da ya zama ruwan dare, amma bai k**ata a yi watsi da shi ba idan yana da tsanani. Da kulawa mai kyau da wasu sauƙaƙan hanyoyi, mata da yawa za su iya rage ciwon cikin sauƙi.

‎Ku tura domin ilimantar da wasu.



Good morning my fellow followers How may i help you ?
06/05/2026

Good morning my fellow followers

How may i help you ?

05/05/2026

Wannan maganar Video taqi ci taqi cinyewa tun jiya

Ko ba kuda lbrn Nigeria isnt OK

Da wace kalma zaku iya bayyana ni idan kuka ji labarin rasuwa ta ?
05/05/2026

Da wace kalma zaku iya bayyana ni idan kuka ji labarin rasuwa ta ?

‎Wata rana wata mata ta kira ni da wata tambaya mai sauƙi…‎‎Amma wannan tambayar ta rikide zuwa wata muhimmiyar tattauna...
04/05/2026

‎Wata rana wata mata ta kira ni da wata tambaya mai sauƙi…

‎Amma wannan tambayar ta rikide zuwa wata muhimmiyar tattaunawa da nake ganin ya k**ata mutane da yawa su ji.

‎Yawancin mutane suna tunanin “hormonal imbalance” ne kawai idan al’ada (period) ta rikice.

‎Amma a gaskiya, matsalar hormones ta fi haka yawa.

‎Bari na yi maka bayani 👇

‎-----------------------------------------------------------


‎➡️ MENENE HORMONAL IMBALANCE?

‎Hormonal imbalance na nufin lokacin da matakin hormones a jiki ya yi yawa ko ya yi ƙasa fiye da yadda jiki ke bukata.

‎Idan hakan ta faru, mace na iya fara ganin wasu canje-canje marasa dadi a jikinta.

‎-----------------------------------------------------------

‎➡️ ALAMOMI

‎1• Rikicewar al’ada (period), ko yawan jini ko ƙarancinsa
‎2• Rashin haihuwa
‎3• Sauyin yanayi (mood swings)
‎4• Bushewar farji
‎5• Rage sha’awar jima’i
‎6• Gajiya da rashin kuzari
‎7• Matsalar barci k**ar rashin bacci (insomnia)
‎8• Matsalolin thyroid
‎9• Ƙara kiba ko rage kiba
‎10• Yawan gashi a jiki (hirsutism)
‎11• Kuraje (acne)
‎12• Zubar gashi

‎----------------------------------------------------------


‎➡️ ABUBUWAN DA KE IYA JAWO SHI

‎1• Damuwa mai tsanani (chronic stress)
‎2• PCOS
‎3• Magungunan hana daukar ciki (hormonal contraceptives)
‎4• Menopause
‎5• Amfani da steroids
‎6• Cututtukan garkuwar jiki (autoimmune diseases)

‎➡️ MUHIMMIN BAYANI

‎Wasu mata na iya samun matsala mai tsanani, wasu kuma ƙanana ne kawai.

‎Amma idan ka lura da alamomin hormonal imbalance, ka garzaya wurin ƙwararren ma’aikacin lafiya domin a duba ka.

‎Za a yi gwaje-gwaje a ba da magani yadda ya dace, sannan canjin rayuwa (lifestyle) yana da muhimmanci.

-------------------------------------------------------


Ka guji amfani da supplements ba tare da shawarar likita ba domin gyaran hormones.

‎Idan ka koyi wani abu daga nan, ka tura wa wasu su ma su amfana 🙏


➡️ MENENE GALACTORRHEA?‎-------------------------------------------‎Wata irin fita ce ta madara daga mama ba tare da mac...
03/05/2026

➡️ MENENE GALACTORRHEA?
‎-------------------------------------------

‎Wata irin fita ce ta madara daga mama ba tare da mace tana da ciki ko tana shayarwa ba.

‎Zai iya faruwa da kansa ko kuma idan an taɓa mama.

‎Yakan fi faruwa ga mata masu haihuwa, musamman waɗanda s**a taɓa haihuwa a baya.

‎----------------------------------------------------------

‎ABUBUWAN DA KA IYA JAWO SHI

‎Yawanci yana faruwa ne saboda wani ƙurji (tumor) mara haɗari a gland ɗin pituitary.

‎Wannan ƙurji yana sa gland ɗin ya fitar da hormone prolactin da yawa (wanda ke haifar da hyperprolactinemia).

‎Yawan prolactin yana sa jiki ya yi tunanin akwai madara da yawa, sai ya fara fitar da ita madara.

‎------------------------------------------------------

‎➡️ SAURAN DALILAI

‎1• Yawan taba mama ko motsa mama
‎2• Amfani da wasu magunguna k**ar: magungunan hana ɗaukar ciki, magungunan hawan jini, da antidepressants
‎3• Matsalolin thyroid
‎4• Amfani da wasu ganyayyaki k**ar fenugreek.

‎--------------------------------------------------

‎➡️ ALAMOMI SA

‎Babban alama ita ce fita madara daga mama ba tare da ciki ko shayarwa ba.

‎Sauran alamomi sun haɗa da:

‎- Bushewar mara
‎- Rashin zuwan al’ada ko tsayawarta (amenorrhea)
‎- Rage bukatuwa ga abokin aure
‎- Kuraje (acne)
‎- Fitowar gashin fuska
‎- Ciwon kai
‎---------------------------------------------------------

‎➡️ ME YA KAMATA A YI?

‎1• Je asibiti: likita zai iya ba da magungunan da za su rage wannan matsala

‎2• Guji yawan taɓa mama

‎3• Nemi shawara kan sauya ko dakatar da wasu magunguna

‎4• A magance duk wata cuta da ke haddasa hakan

‎5• Sanya tufafi masu laushi da sassauƙa don rage gogayya a mma

‎6• Amfani da breast pads don shan madarar yayin da ake jiran magani

‎Idan kana fuskantar wannan matsala, ka je asibiti don samun kulawa.

‎Ka guji shan magunguna ba tare da shawarar likita ba don kauce wa matsaloli.

‎Ka tura wannan saƙo domin ilmantar da sauran mutane.


‎ME YA KAMATA KA YI IDAN ULCER BA YA WARKA‎-------------------------------------------------------‎‎Kana fama da ciwon c...
02/05/2026

‎ME YA KAMATA KA YI IDAN ULCER BA YA WARKA
‎-------------------------------------------------------

‎Kana fama da ciwon ciki da baya daina? Kana shan magani akai-akai amma babu sauƙi?
‎Tsoron abinci, rashin jin daɗi da dare, da damuwa kullum…
‎Kana maganin ulcer amma babu wani canji?
‎Idan ulcer ya ƙi warkewa, sau da yawa saboda ba a gano ainihin dalilin ba.

‎Mutane da yawa suna maganin ulcer, amma ciwon yana dawowa.
‎Idan ulcer ya ƙi warkewa, galibi saboda abin da ke haddasa shi yana nan har yanzu.

‎--------------------------------------------------------

‎🔑 Ulcer ba zai warke ba idan ƙwayar cutar H. pylori tana nan a ciki.
‎Wannan ƙwayar cuta tana lalata bangon ciki.
‎Idan ba a kashe ta gaba ɗaya ba, ulcer zai ci gaba da dawowa.
‎🔑 Shan magungunan rage zafi k**ar ibuprofen, diclofenac, ko aspirin na hana warkewa.
‎Waɗannan magunguna suna rage kariyar cikin ciki.
‎Ko da kaɗan-kaɗan kana sha kullum, suna iya hana ulcer warkewa.
‎🔑 Tsallake ko dakatar da maganin ulcer da wuri yana da haɗari.
‎Ulcer yana buƙatar makonni kafin ya warke gaba ɗaya.
‎Idan ka daina magani da wuri, zai dawo da ƙarfi.
‎🔑 Shan taba yana jinkirta warkewa.
‎Nicotine yana rage jini zuwa bangon ciki.
‎Hakan yana hana gyara da warkewa yadda ya k**ata.
‎🔑 Shan giya yana ƙara tsananta ulcer.
‎Yana ƙara acid a ciki kuma yana lalata wurin da ke warkewa.
‎Shan giya akai-akai yana hana ulcer rufewa.
‎🔑 Halayen abinci mara kyau suna da tasiri.
‎Cin abinci da dare sosai, abinci mai yaji ko mai mai yana ƙara acid da zafi.
‎🔑 Tsananin damuwa (stress) yana shafar acid da hormones na warkewa.
‎Dogon damuwa yana iya hana warkewa ko da kana shan magani daidai.
‎🔑 Wani lokaci ba ulcer ba ne.
‎Wasu cututtuka k**ar na gallbladder ko reflux suna k**a da ulcer.
‎🔑 A wasu lokuta kaɗan, ulcer da baya warkewa na iya zama alamar kansar ciki.
‎Yana fi faruwa ga manya, musamman idan akwai rage kiba ko amai da jini.

‎-------------------------------------------------------

‎ME YA KAMATA KA YI IDAN ULCER BA YA WARKA

‎Ka kammala duk maganin da aka baka
‎A gwada ka don H. pylori kuma a yi magani yadda ya k**ata
‎Ka daina amfani da painkillers ba tare da buƙata ba
‎Ka guji taba da giya
‎Ka rika cin abinci kaɗan-kaɗan amma akai-akai
‎Ka ga likita idan ciwon ya wuce makonni 4–8
‎Ulcer da baya warkewa gargadi ne — ba abin wasa ba ne.

‎Ka tura wa wasu don su amfana 👍



‎CUTUTTUKAN DA SUMBATA KE JAWOWA‎--------------------------------------------------------‎‎Kafin mu fara, Barka da ranar...
01/05/2026

‎CUTUTTUKAN DA SUMBATA KE JAWOWA
‎--------------------------------------------------------

‎Kafin mu fara, Barka da ranar jumaa🎄 Kar ku manta da yiwa Annabi SAW salati 😁

‎Bari mu tunatar daku kafin wani ya je ya sumbaci wanda bai k**ata ba 🙂👇

‎Cutar sumbata wata cuta ce mai yaɗuwa wadda aka fi samu a matasa da samari.

‎A fannin likitanci, ana kiranta Mononucleosis.

‎Mononucleosis cuta ce ta ƙwayar cuta (virus), galibi tana faruwa ne saboda ƙwayar Epstein–Barr virus (EBV).

‎- Yawancin mutane suna iya kamuwa da wannan ƙwayar a wani lokaci a rayuwarsu, sau da yawa tun suna yara ba tare da sun sani ba.
‎-------------------------------------------------------

‎🏷️ YADDA TAKE YAƊUWA

‎Cutar mono tana yaduwa ne ta yahu (saliva), saboda haka tana iya watsuwa ta:

‎1- Sumbatar wanda ya kamu da cutar (ko wanda ya warke ba jimawa )
‎2- Amfani da abubuwan da s**a taɓa baki k**ar cokali, kofuna, buroshi, lip balm
‎3- Wani lokaci ta hanyar tari ko atishawa
‎4- Haka kuma tana iya yaduwa ta jini ko ruwan jima’! (amma ba kasafai ba)
‎5- Ko bayan alamomi sun tafi, ƙwayar na iya ci gaba da zama a baki har tsawon watanni, kana iya watsawa ba tare da ka sani ba.

‎--------------------------------------------------------

‎🏷️ ALAMOMIN CUTAR

‎Alamomi na iya bayyana bayan makonni 4–6 bayan kamuwa:

‎A- Ciwon makogwaro mai tsanani (wahalar hadiya)
‎B- Zazzabi
‎C- Kumburin ƙwayoyin lymph (a wuya, ƙirji, ƙugu)
‎D- Tonsils masu kumburi tare da farin ko rawaya a kai
‎E- Gajiya mai tsanani sosai
‎F- Ciwon kai, ciwon jiki, rashin sha’awar abinci
‎G- Wani lokaci: kuraje, kumburin saifa (spleen) ko hanta

‎-----------------------------------------------------
‎🏷️ MAGANI

‎Saboda virus ne, antibiotics ba sa aiki (sai idan akwai wata cutar bacteria tare da ita)

‎Magani ya haɗa da:

‎- Hutu sosai
‎- Shan ruwa da yawa
‎- Amfani da maganin rage zafi/zazzabi k**ar paracetamol ko ibuprofen (da shawarar likita)
‎- Gujewa aspirin ga matasa (saboda haɗarin Reye’s syndrome)
‎- Gargaɗi da ruwan gishiri don sauƙaƙa makogwaro
‎- Gujewa wasanni masu ƙarfi saboda kumburin saifa na iya haifar da matsala

‎🏷️ HANYOYIN KARIYA

‎- Kada a raba kayan baki (kofuna, cokali, buroshi, lip balm)
‎- Gujewa sumbatar wanda aka sani yana da cutar
‎- A yi hattara ko bayan ya warke saboda har yanzu yana iya watsawa


‎Shin ka amfana da wannan rubutun ?
‎idan ka amfana kayi sharing domin wasu su amfana.


‎‎CUTUTTUKAN DA SUMBATA KE JAWOWA
‎--------------------------------------------------------

‎Kafin mu fara, Barka da ranar jumaa🎄 Kar ku manta da yiwa Annabi SAW salati 😁

‎Bari mu tunatar daku kafin wani ya je ya sumbaci wanda bai k**ata ba 🙂👇

‎Cutar sumbata wata cuta ce mai yaɗuwa wadda aka fi samu a matasa da samari.

‎A fannin likitanci, ana kiranta Mononucleosis.

‎Mononucleosis cuta ce ta ƙwayar cuta (virus), galibi tana faruwa ne saboda ƙwayar Epstein–Barr virus (EBV).

‎- Yawancin mutane suna iya kamuwa da wannan ƙwayar a wani lokaci a rayuwarsu, sau da yawa tun suna yara ba tare da sun sani ba.
‎-------------------------------------------------------

‎🏷️ YADDA TAKE YAƊUWA

‎Cutar mono tana yaduwa ne ta yahu (saliva), saboda haka tana iya watsuwa ta:

‎1- Sumbatar wanda ya kamu da cutar (ko wanda ya warke ba jimawa )
‎2- Amfani da abubuwan da s**a taɓa baki k**ar cokali, kofuna, buroshi, lip balm
‎3- Wani lokaci ta hanyar tari ko atishawa
‎4- Haka kuma tana iya yaduwa ta jini ko ruwan jima’! (amma ba kasafai ba)
‎5- Ko bayan alamomi sun tafi, ƙwayar na iya ci gaba da zama a baki har tsawon watanni, kana iya watsawa ba tare da ka sani ba.

‎--------------------------------------------------------

‎🏷️ ALAMOMIN CUTAR

‎Alamomi na iya bayyana bayan makonni 4–6 bayan kamuwa:

‎A- Ciwon makogwaro mai tsanani (wahalar hadiya)
‎B- Zazzabi
‎C- Kumburin ƙwayoyin lymph (a wuya, ƙirji, ƙugu)
‎D- Tonsils masu kumburi tare da farin ko rawaya a kai
‎E- Gajiya mai tsanani sosai
‎F- Ciwon kai, ciwon jiki, rashin sha’awar abinci
‎G- Wani lokaci: kuraje, kumburin saifa (spleen) ko hanta

‎-----------------------------------------------------
‎🏷️ MAGANI

‎Saboda virus ne, antibiotics ba sa aiki (sai idan akwai wata cutar bacteria tare da ita)

‎Magani ya haɗa da:

‎- Hutu sosai
‎- Shan ruwa da yawa
‎- Amfani da maganin rage zafi/zazzabi k**ar paracetamol ko ibuprofen (da shawarar likita)
‎- Gujewa aspirin ga matasa (saboda haɗarin Reye’s syndrome)
‎- Gargaɗi da ruwan gishiri don sauƙaƙa makogwaro‎
- Gujewa wasanni masu ƙarfi saboda kumburin saifa na iya haifar da matsala

‎🏷️ HANYOYIN KARIYA

‎- Kada a raba kayan baki (kofuna, cokali, buroshi, lip balm)
‎- Gujewa sumbatar wanda aka sani yana da cutar
‎- A yi hattara ko bayan ya warke saboda har yanzu yana iya watsawa


‎Shin ka amfana da wannan rubutun ?
‎idan ka amfana kayi sharing domin wasu su amfana.





‎MAGANIN CIWON ULCER ‎-------------------------------------‎‎Na san wani mutum da yake fama da ciwon ulcer tun ina ƙaram...
30/04/2026

‎MAGANIN CIWON ULCER
‎-------------------------------------

‎Na san wani mutum da yake fama da ciwon ulcer tun ina ƙarami.
‎Ba wai saboda ulcer ɗin ba ya warkewa ba ne, sai dai saboda yana da wahala a ci gaba da bin ƙa’idojin rayuwa masu kyau akai-akai.

‎Warkewa na buƙatar haƙuri, jajircewa, da ƙananan zaɓuɓɓuka na yau da kullum. Wannan ɓangaren shi ne mafi wahala ga mutane da yawa.

‎A yau, mutane da dama suna rayuwa da ciwon ƙirji (heartburn), ciwon ciki, da rashin narkewar abinci. Wasu ma sun daina fatan samun sauƙi, suna tunanin wannan ciwo ya zama wani ɓangare na rayuwarsu.

‎Amma ciwon ulcer ba wai yana da taurin kai ba ne, illa dai yana lalata jin daɗin rayuwa ne a hankali idan ba a fahimce shi ko sarrafa shi yadda ya k**ata ba.

‎A yau, muna son mu fahimci wannan cuta da yadda za mu kula da kanmu da kyau.
‎------------------------------------------------------

‎🏷️ MENENE CIWON ULCER ?
‎Ciwon ulcer yana faruwa ne lokacin da aka samu buɗaɗɗun raunuka (ulcers) a cikin:
‎Ciki (stomach)

‎Farkon ɓangaren hanji (duodenum)
‎Wani lokaci kuma yana iya shafar esophagus da jejunum
‎Wadannan raunuka suna samuwa ne idan ruwan narkewar abinci ya lalata kariyar mucous (garkuwar ciki).


‎-------------------------------------------------------

‎🏷️ ABUBUWAN DAKE KAWO ULCER

‎Akwai manyan dalilai guda biyu da ke haddasa yawancin ulcer:

‎1- Kwayar cuta H. pylori
‎Wannan ƙwayar cuta tana rayuwa a bangon ciki, tana fitar da enzymes da ke lalata mucous (garkuwar ciki).
‎Hakan yana barin acid ya lalata bangon ciki. Duk da acidity na ciki, tana iya rayuwa saboda tana samar da wani enzyme da ke rage tasirin acid ɗin.

‎2- Yawan amfani da magungunan kashe zafi (NSAIDs)
‎Misalai sun haɗa da: Ibuprofen, Diclofenac, Felvin, Aspirin, da sauransu.
‎Waɗannan magunguna suna rage samar da prostaglandins, waɗanda ke:
‎Samar da mucus da bicarbonate
‎Inganta jinin da ke zuwa bangon ciki
‎Kare ciki daga lalacewa
‎Idan prostaglandins sun ragu, ciki zai zama mai sauƙin kamuwa da ulcer.

‎------------------------------------------------

‎ALAMOMIN CIWON ULCER

‎Wasu mutane ba sa nuna alamomi, amma mafi yawanci sun haɗa da:
‎Ciwon saman ciki (mai k**a da ƙonewa ko cizo)
‎- Rashin narkewar abinci
‎- Cunkoson ciki (bloating)
‎-Ciwon ƙirji (heartburn)
‎- Jin tashin zuciya ko amai
‎- Rashin sha’awar abinci
‎- Yawan yin gyambon ciki (belching)
‎- Ciwon dare da ke sauƙi idan an ci abinci



Address

Dala
Kano
0001

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Asad Yelwa Hub posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share