31/01/2025
*GORON JUMA’AH.*
Assalamu Alaikum Warahamutullah inaso na kara tunasar damu Ƴan-Uwa yana da kyau duk rashin lafiyar da kake fama da ita kadaina tunanin wai kai ba zaka warke ba, Zaka warke Dan-Uwa duk kuwa da irin girman jinyar da kuma karfin ta, da izinin Allah.
Wallahi ina mamakin musulmin da za'a ce masa gaskiya wannan rashin lafiyar da kake fama da ita, da wuya ka tashi.
Ko ace masa wannan cutar taka ai ba'a warkewa.
Kuma ya yarda da hakan, ya karaya kawai ya tsaya yana jiran lokacin mutuwa yayi, Subhanallahi 😪 Dan’Uwa karka yarda ka tsorata, zaka warke da izinin Allah.
Sau nawa ake samun marasa lafiyar da an debe musu tsammani, a samu wani baki mai albarka yayi masa addua, yace Allah ya baka lafiya, Allah ya basulafiya.
Watakila wani ma basa tare amma sai kaga wannan addu’ar tazo ta bige shi, kaga yazo ya warke anata mamaki.
Sau nawa ake samun wanda ya debe tsammani, duk wani maganin daya k**ata yayi, yayi amma bai samu sauki ba.
Sai yazo ya sha ruwan zamzam da niyyar Allah Madaukakin Sarki ya bashi lafiya, kuma yazo ya warke.
Marubucin nan Dale Carnegie, Yace”
Akwai wani mara lafiya da ake kira hanny, yana fama da gyambon mai tsanani a cikin hanjin sa.
Tsananin ciwon yasa likitoci s**a cewa hanny ga iya tsawon lokacin da zaka iya rayuwa daga nan kuma zaka mutu.
Hanny yana jin wannan sai ya tsaya yayi tunani yace, indai ba abinda ya rage min a duniya sai lokaci kadan.
To me zai hana na dan more wannan lokacin daya ragemin koma ta yayane.
Daman gashi na jima ina son in zagaye duniya in tafi yawon bude ido, lalle wannan shine lokacin daya k**ata inyi hakan.
Kawai sai hanny ya siyo ticket.
Likitoci s**a nemi hanny s**a bashi shawara, su kace masa hanny kabi a hankali, zaka mutu a hanya fa.
Yace musu haba ba abinda zai faru, ni nariga na cewa dan uwana koda na mutu a kawo ni a binne ni a makabartar family saboda haka duk a inda na mutu za'a dawo dani gida.
Kawai sai ya dauki hanya cikin murna cikin farin ciki ko tina rashin lafiyar ma baya yi.
Kawai sai dai ya turowa matarsa sako cikin murna, gamu a waje kaza muna cikin jin dadi muna morewa, gamu a gidan zoo muna kallon namun daji, gamu a teku kaza muna kallon kifaye kala kala, gamu a wajen cin abinci kaza, gamu a wajen tarihi kaza.
Yace mata kai, tunda nake ban taba jindadi irin wannan a rayuwata ba.
Daga karshe dai hanny ya cigaba da rayuwa cikin murna, cikin farin ciki ya mantama da yanada wata rashin lafiya, ita ma kuma rashin lafiyar ta manta dashi.
A karshe dai hanny wannan shine sanadiyyar warakar sa, rashin lafiyar bai sake juyo masa ba.
Masana lafiya, masana jikin dan Adam dayawa, suna ganin cewa wannan hanyar da hanny yabi itace babbar hanya da zakayi amfani da ita wajen shawo kan rashin lafiyar da kake fama da ita komai girman ta.
To masu fama da rashin lafiya, bayan wannan har yanzu kuna tunanin bazaku warke ba?
Kuna tunanin cewa likita shi yasan ranar da zaku mutu, shiyasan cutar da zata iya kashe ka, Allah shi bai sani ba?
Ko kana munana zato ga Allah Madaukaki ne, kana ganin cewa bazai iya warkar maka da wannan cutar taka ba.
Ko ka manta shine ya kawota a lokacin da babu ita, ka taba yin tunanin zaka kamu da wannan rashin lafiyar?
Amma ba gashi ta k**aka ba, kuma zaka warke da izinin Allah.
Ko k**anta cewa akwai bayin Allah salihai a sassa daban-daban na wannan duniyar nan kullum suna yiwa marasa lafiya addua, suna cewa Allah ka warkar da marasa lafiya gaba daya.
Ko kana debe tsammanin cewa wata addua daga adduoin wadannan bayin Allah bazata iya fadowa kanka ba.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
Ku karbi maganin ku Jarraba karkuce kun gwada-kun gwada baku sami waraka ba, wlh wata-rana za’a dace.
Natural Herbal Remedy, Cibiyar bada magunguna.
Munq Taimakawq da maganin Hepatitis, Hawan Jini, Ulcer, Basir mai tsiro duk yadda yakai, in sha Allah muna Taimakawa da maganin kuma da Izinin Allah za’a samu waraka.
Ai mana magana a WhatsApp ko’a Kiramu a wannan lambar k**ar haka:- 07075875299