Kula Da Lafiya

Kula Da Lafiya Maraba izuwa shafin KIWON LAFIYA. Inshaallah wannan Shafi zai dunga kawo muku abubuwan fadakarwa Dan gane da lafiya.

24/02/2025

Assalamu alaikum.
Sunana Dr Abdurrahman Dambazau (MBBS BUK/AKTH).
Shekaru biyu baya, nakasan ce ina ilimantar da mu ta wannan shafin nawa (Dr Dambazau TV) akan abubuwan da ya shafi lafiyar mu, wanda sak**akon yanayi na ayyuka da kuma karatu, na dakata Kuma shafin (page) ya bar hannu na.
Insha Allahu daga yau ragamar wannan shafi ya dawo hannu na, kuma insha Allahu zan cigaba da kawo muku abubuwa na ilimantar wa da za su amfane mu.
Ƙofa ta a buɗe take domin shawarwari da kuma gudun mawan ku, wajen cigaba wannan shafin nawa.
Nagode.
Dr. Dambazau TV Dambazau Health TV

29/02/2024

***HAWAN JINI / HYPERTENSION***

Rubutawa✍️✍️✍️
RCHP Atiku Tafida Karaye
(Jchew, Chew)

GABATARWA:
Ciwon hawan jini cuta ce babba wadda ke yawan haddasa ciwon zuciya. Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ƙiyasta cewa mutane da dama waɗanda ke tsakanin shekara talatin zuwa saba'in da tara suna fama da wannan cutar ta hawan jini. Fiye da kashi biyu cikin uku na mutanen suna zaune ne a ƙasashen da ke da ƙarancin cigaba ta hanyar tattalin arziki.

MENENE HAWAN JINI?
Hawan jini ciwone dayake samuwa sak**akon karuwa ko hawa da bugun jinin mutum kayi fiye da kima.

RABE-RABEN HAWAN JINI
Dangane da abubuwan da ke kawo ciwon hawan jini, masana sun kasa ciwon hawan jini zuwa kashi biyu (2) k**ar haka:
1. Kashi na farko (primary hypertension) shi ne hawan jinin da babu wanda yasan tak**ammen abin da ke kawo shi. Hawan jinin yana faruwa ne kawai ba tare da wata cuta ta kawo shi ba. Likitoci zasuyi iya binciken su amma baza su gano asalin hawan jinin ba, abu ɗaya za'a iya alaƙanta shi dashi, wanda shi ne gado.
2. Hawan jini kashi na biyu ( Secondary hypertension) wannan shi ne akan iya gane tak**ammen abinda ya kawo hawan jinin. Wannan hawan jinin ya kan zo ne sak**akon wata cuta ko dalili da tayi wa mutum illa a jiki.

ABUBUWAN DA KE KAWO CIWON HAWAN JINI
Likitoci masana zuciya da jijiyoyin jini sun raba abubuwan da ke kawo hawan jini zuwa gida biyu.
1. ABUBUWAN DA MUTUM ZAI IYA CHANAZAWA
A. Yawan cin gishiri
B. Yawan cin kitse
C. Rashin motsa jiki
D. Shan sigari
E. Shan giya
F. Yawan ƙiba (taiɓa)
G. Shan miyagun ƙwayoyi
H. Yawan shan wasu magunguna k**ar su:
I. Magungunan bada tazarar iyali.
2. ABUBUWAN DA MUTUM BA ZAI IYA CHANZAWA BA
A. Zama baƙi (Ɗan Africa)
B. Zama mace ko namiji
C. Gadon hawan jini
D. Yawancin shekaru (shekara 65 zuwa sama).

ALAMOMIN CIWON HAWAN JINI
Ciwon hawan jini baya da wani alama da yake nunawa a lokacin da yake matashi. Shi yasa bature yakan yiwa cutar laƙabi da 'silent killer' ma'ana mai yin kisa a ɓoye. Mafi yawancin mutanen da ke fama da hawan jini baza su san suna da shi ba har sai yayi musu wata illa, wannan shi yasa ake son mutane su dinga auna matsin lambar jinin su (blood pressure) akai-akai. Wasu alamomi da mutum yakan iya gani a wani lokaci masu nuna hawan jini sun haɗa da.
1. Yawan ciwon kai
2. Yawan ganin jiri.
3. Rashin gani da kyau.
4. Yawan kasala
5. Ciwon ƙirji
6. Yawan bugawar zuciya.
7. Rashin bacci

RIGAKAFIN KAUCEWA KAMUWA DA HAWAN JINI
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da shawarar:
1. inganta salon rayuwa mai kyau da abinci mai kyau
2. kauce wa shan barasa
3. motsa jiki akai-akai da kula da nauyin jiki na yau da kullum
4. Kaucewa shan taba
5. koyi sarrafa damuwa
6. Rage chin gishiri
7. Rage ƙiba (taiɓa)
8. Rage chin kitse
9. Yawan chin ƴaƴan itace da kayan lambu.
10. Samun isasshen bacci.

SHARSHI / RUFEWA
Hawan jini cuta ce babba dake damuwar al'umma. Acikin wannan rubutu munga abubuwan da ke kawo ciwon hawan jini, Rabe-raben sa, alamomin sa da kuma yanda ake rigakafin sa. A lura cewa, damuwa da yawan baƙin ciki basune suke kawo ciwon hawan jini ba, saɓanin yadda mafi yawan mutane ke ɗauka.
Amma damuwa da baƙin ciki suna sanya hawan jinin ya ta'azzara ko kuma ya tashi. Wannan yana faruwa ne sak**akon fitar da sinadarin adrenaline da noradrenaline dake faruwa a lokacin damuwa da baƙin ciki.
Allah ya tsaremu ya inganta mana lafiyarmu.

Author:
RCHP. Atiku Tafida
{Jchew, Chew}

*Hawan Jini*Cutar hanwan jini cuta ce wacce tazama Ruwan dare a kasarmu ta gado, cuta ce wacce tayi yawa tsakanin mutane...
31/10/2023

*Hawan Jini*

Cutar hanwan jini cuta ce wacce tazama Ruwan dare a kasarmu ta gado, cuta ce wacce tayi yawa tsakanin mutane maza da mata.

Hawan jini nadaya daga cikin cutukan da ake samu ko da yaushe musamman ga manyan mutane da mata masu juna 2.

Ya zuwa yanzu dai, kashi 95% Na hawan jinin da ake dashi Ba a San abinda ke haddasa shiba sauran kashi 5% shine Wanda wasu ababe kan haddasa daga baya k**ar firgita, tsoro dakuma Wanda ake gado daga Uwaye da kakanni.

Wasu da dama basusan sunada hawan jini Ba wasu kuma sun sani amma suna ko inkuli da yin maganinsa.

Hawan jini yakan janyo illoli da dama ajiki musamman ga mata da mutane masu rauni.

Matukar hawan jini yai yawa yakan haifar da
1, Bugawar zuciya
2, Rashin jini
3, Zubar ciki
4, Ciwon sashe
5, Jijjiga

Kadan daga cikin abinda ake la'akari agane mutum Nada hawan jini
1, Ciwon kai
2, Rashin wadataccen barci
3, Ciwon hakarkari
4, Kunburin kafafu da hannaye,
5, Juwa
6, Hauhawan bugun zuciya

Wadannan kadai bazai isa agane hawan jini batare da daukan bp Ba nan take, hawan jini nada magani, akanyi anfani da magunguna

Taimakon Farko Ga Wanda Maciji Ya SaraWane taimakon farko ake ba wanda maciji ya sara kafin a kai shi asibiti?To da yake...
17/07/2023

Taimakon Farko Ga Wanda Maciji Ya Sara

Wane taimakon farko ake ba wanda maciji ya sara kafin a kai shi asibiti?

To da yake an fi samun wannan matsala ne a daji ko a gona yana da wuya a ba wanda maciji ya sara taimakon farko ko taimakon gaggawa nan take, sai dai idan akwai mutane a tare da shi a lokacin.

Bugu da kari, k**ata ya yi a ce akwai layukan kar-ta-kwana na ma’aikatan agaji na hukumomi da masu zaman kansu wadanda mutum ko shi kadai ne zai buga ya yi bayani a kai masa agaji nan take.

A ’yan kwanakin nan a makarantu da gidajenmu a yanzu akan ji wannan hadari na sarar macizai yana faruwa.

Da an ga wanda maciji ya sara sai a kwantar da shi a sa ya natsu, a kuma tabbatar yana cikin hankalinsa yana magana, don kada ya tsorata ya rikice ya shide.

Wannan yana da muhimmanci don kada rikicewar ta sa guba saurin bin jini.

Daga nan sai a daure wurin da dafin ya shiga (ba saman ba) da tsumma mai tsabta ko yankin tufafin marar lafiyar, don rage zubar jini da kiyaye hawansa zuwa zuciya.

Wadansu s**an ce a kafa kai a tsotse wurin, amma a likitance babu wannan. Sannan sai a garzaya da shi babban asibiti.

An ce babban asibiti saboda can ne ake tunanin za a samu allurar karya dafi, ba a kananan asibitoci ba.

Dokta Auwal Bala

Daga Jaridar Aminiya ta 19 ga Satumba, 2021.

Adadi Da Amfanin Sanya Harza (fibres) A Cimaka Dr. Naziru Bashir Mukhtar PhDA kullum, ana bukatar a abincin da mutum zai...
10/07/2023

Adadi Da Amfanin Sanya Harza (fibres) A Cimaka

Dr. Naziru Bashir Mukhtar PhD

A kullum, ana bukatar a abincin da mutum zai ci ya hada da dangin abinci mai harza (fibres). Harza na da matukar amfani ga jiki, tana taimakawa wajen saukaka nika abinci bayan an ci da kuma taimakawa wajen yawon abincin da kuma tattara abincin da baa yi amfani da shi ba gami da aika shi zuwa ga dubura domin kasayarwa. Tana saukaka wahalar yin bayan gida da kuma gajarta lokacin yin tsuguno. Ma'ana, harza dai na taimakawa wajen inganta lafiyar ciki, hanji da dubura. Hakan ne ma ya sa harza na taimakawa wajen hana samuwar ciwon basir ko kuma saukaka cutar.

A wani bangaren kuma, harza na taimakawa wajen rage kiba domin tana sawa ciki ya cika a ji an koshi da wuri ba tare da an ci sinadaran kuzari da yawa ba (calories).

Ga masu ciwon suga, harza na taimaka musu matuka wajen su dinga samun koshi ba tare da sugansu ya wuce misali a cikin jini ba.

Ana samun harza a abinci da yawa, musamman ganyayyaki da yayan itace da s**a hada da; yalo, data, karas, salad, gurji, dafaffiyar/gasasshiyar masara, lemo, goruba, tuffa da sauransu. Ana son a kullum a ci harza da ta kai kimanin giram (gram) 25-40.

Allah Ya kara mana lafiya.

09/07/2023

Wacce matsala ya k**ata muyi bayani a rubutu na gaba?

10/04/2023

BARKANMU DA YAMMA

23/03/2023

*PNEUMONIA* (Cutar Sanyin Kuhu, ko Kumburin Kuhu).

Rubutawa✍️✍️✍️
RCHP ATIKU TAFIDA KARAYE

*GABATARWA*
Cutar pneumonia na daga cikin muggan cututtakan da ke yiwa mutane illa, Musamman yara a duniya, kasancewar tana halaka yara sosai a kowacce shekara.
wannan cuta tana samuwa ne sanadiyyar shigar wasu kwayoyin cuta wanda ke haifar da abubuwa guda uku, na farko idan cutar ta shiga za'a ga kuhun ya kumbura, na biyu kuma yakan canza kala yayi ja, abu na uku kuma sai ya kasance yana yawan ciwo.
Najeriya dai na daga cikin kasashenda aka fi fama da wannan cuta ta Pneumonia a duniya.

*MECECE PNEUMONIA (Cutar Sanyin Huhu).*
Pneumonia wata cuta ce, da take k**a hanyoyin shakar iska (numfashi) wacce take K**a kuhun mutum.

*ABUBUWAN DA SUKE HADDASA CUTAR PNEUMONIA*
1). Matsanancin Sanyi
2). Kwayoyin halittar BACTERIA, VIRUS da FUNGI.

*NAU'IKAN CUTAR PNEUMONIA*
A lokutta da yawa mutane kan zauna da wasu cututtuka, batare da sun san abubuwan da s**a haddasa musu cutar ba, da kuma daukar matakin da s**a k**ata don magance cutar. Bincike ya bayyanar da nau’o’in cutar “Pneumonia” wadda akafi sani da Nimoniya, wata cutace da mutane kan dauke ta a dalilin aikata wasu abubuwa.

*Nau’i na farko shine “Bacteria Pneumonia” itace nau’i da akan sameta a jikin kowa, babu babba babu yaro, akan kamu da ita ne a sanadiyar wasu cututtuka da s**an shiga cikin jikin mutun, ta hanyar kura, kusantar waje da bashi da tsafta, haka idan mutun na dauke da mura takan rikide ta koma cutar nimoniya idan ba'a dauki mataki cikin gaggawa ba.

*Ta biyu kuwa itace “Mycoplasma Pneumonia” itace cutar nimomiya da akafi samun ta a jikin yara kanana da matasa, a sanadiyar wasan ruwa, ko kusantar wuri mai danshi, ko wasa a wajen da ba iska nagartacciya. Zama cikin daki mai dauke da zafi, ko inda mutane su kayi yawa, duk suna haddasa wannan nau’in na nimoniya.

*Ta uku kuwa itace “Viral Pneumonia” tana samuwa ne a sanadiyar yadda mutane, kanyi mu’amala da masu dauke da cutar, wanda takan fara a matakin farko sannu a hankali, sai ta kai wani matakin da maganin ta na iya zama da wuya.

*ALAMOMIN CUTAR PNEUMONIA*
1). Tari mai wahala
2). Tari mai jini
3). Numfashi sama-sama

*HANYOYIN KARIYA DAGA CUTAR PNEUMONIA*
*Ana allurar rigakafin shi
*Kiyayewa daga shan abu mai sanyi
*Kiyaye shiga sanyi musamman yara

*JAN HANKALI GA IYAYE"
Ku kiyaye yaranku daga shiga sanyi da kuma basu abu mai sanyi, a yayinda kuma yaran s**a kamu da wannan cuta yana da Kyau iyaye su kula da mai da hankali da zuwa wajen likita da wuri sannan in anje a kula kwarai ainun da bawa yaran magani a kai a kai.

Muna Adduar, marasa lafiya Allah y basu lafiya, masu lafiya Allah y qara mana lafiya.
Ameen.

Wa'inda s**a rigamu gidan gaskiya Allah yaji qansu Yayi musu rahama.


WhatsApp/Tel: 07036193147

07/03/2023

CALENDAR METHOD OF FAMILY PLANNING

Jiya wani member Yayi tambaya akan ta Yaya za a samu hanya Mafi sauki ta yin tazarar haihuwa, ba tareda shan kwayoyin contraceptives ba, duba da yadda ya fahimci suna da yawan side effects. To ga bayanin a bayyane!

WANNAN AMSA TA KUNSHI:-

1-Dalilin da ke jawowa 'yan mata yawan ciwon ciki ko ciwon mara musamman bayan Haila.
2-Yanda ma'aurata zasu yi 'family planning' ba tareda shan magani ba.
3-Abinda ke fitowa wasu mata mai k**ar majina, da sauransu.

Da farko, zan yi amfani da kalmomin Hausa domin samun sauqin fahimta, kalmomin turancin da ban san ma'anar su da Hausa ba don haka zanyi kwatancen da za'a gane!

Idan nazo kan FAMILY PLANNING zan yi bayani akan abinda bincike ya tabbatar, amma ba sai na maimaita ba, Allah Ya kan iya canja ikon sa koda anyi hakan kuma a samu haihuwa, amma Insha Allah ba'a cika samun haihuwa ba idan akayi hakan.

Da farko; a jikin mahaifar mace, (Uterus in female reproductive system) idan muka lura, zamu ga wasu abubuwa k**ar hannaye guda biyu, daya gefen dama dayan kuma gefen hagu, a bakin ko wanne, akwai wani abu qullutu wanda a cikin sa akwai wasu kwayaye.

Duk sanda Mace tayi Jinin ta na Haila, bayan jinin ya dauke da kwanaki 14, wancan abu dana ambata yana sakin wadancan kwayayen(eggs) wadanda sune sinadarin da ake hadawa a samu da' (yaro).

Wadannan kwayaye idan aka sake su s**an shiga cikin mahaifar mace suyi kwanaki 2 (48hours) daga nan idan babu abinda yazo ya ta6asu, wato na daga sperm(maniyin Namiji) to zasu mutu.

Kafin a saki wadannan kwayayen akwai abinda Allah Ya halitta a cikin mahaifar mace wanda zai zo ya share mahaifar ta sosai, domin mahaifar zatayi baqo(stranger), wanda shine wannan kwan kenan. Sannan, Akwai wasu jijiyoyi guda biyu na jini, a gefen dama da hagu na mahaifar mace, idan akazo aka share mahaifar, to wadannan jijiyoyin zasu cika da jini sosai, saisu koma ja-ja- wur, suna jiran wannan baqon da zai shigo mahaifa idan ya girma bai mutu ba sai su rika bashi wannan jinin a matsayin abinci.

Shi kuma maniyyin 'da Namiji yana yin kwanaki 3(72hours) a cikin mahaifar mace kafin ya mutu, sa6anin na mace dake kwana 2 (48hrs).
!
!
!
!
!
Idan mun fahimci wadancan bayanan da s**a gabata, to yanzu sai mu hada su waje daya muga yadda abin yake;

Idan Mace ta gama haila da kwanaki 14 to wancan abun mai k**ar tiyo (follopian tube) na jikin mahaifar ta yakan saki wadannan kwayayen, zasu shigo cikin mahaifarta suna jiran Maniyyin Namiji yazo ya same su, idan s**a hadu komai qarancin Maniyyin nan, to Maniyyin zai zamo musu k**ar taki(fertilizer) don haka zasu hadu su girma, da hakane kuma Allah zai yita sarrafa shi cikin iko da buwayar Sa har ya maida shi mutum! SUBHANALLAH!!

To idan kuwa babu wani Maniyyi da ya shigo wurin a dalilin rashin saduwa da macen, to wadannan kwayayen zasu mutu bayan sunyi awa 48 (kwanaki 2), idan kuma s**a mutu to zasu biyo cikin al'aurar mace sai su fito, sai kaji mata na tambayar s**an ga wani abu mai k**ar majina-majina yana fito musu a al'aura, wannan shine abinda ke fitowar! Wannan ya sa malamai s**a ce babu komai akan wannan kawai ta wanke shi ba shida wani hukunci.

In the same boat;

A dalilin rashin shigar Maniyyi da zai girmar da wancan kwan, sai wadancan jijiyoyi da s**a tara jini a cikinsu, sai suyi wani abu da ake kira fushi,(watau basu ji dadi ba)a dalilin haka sai su rinka kartar jikin mahaifar mace, sai kaji mace tace maka tana yawan fama da ciwon mara (lower abdominal pain) musamman idan ta gama Haila.

Idan karce jijiyoyin nan yayi yawa kuma aka yi rashin sa'a sai su fashe, idan kuma s**a fashe sai jini yayita fita ba tsayawa, wannan shine ake qira da jinin Istihada, daman Manzon Allah (s.a.w) ya taba gayawa wata mata cewar ai wannan jinin na jijiya ne.

FAMILY PLANNING:-

Idan Matar aure ce kuma tana son yin FAMILY PLANNING da Mijinta, to hanya mafi sauqi itace;

K**ar yadda muka ji cewa bayan gama hailar mace da kwanaki 14 ake sakin wadancan kwayayen, kuma s**an yi kwanaki 2 kafin su mutu, shi kuma maniyyin namijin yakan yi kwanaki 3 kafin ya mutu, to su ma'auratan kada su sadu tun ranar 12 da gama hailar ta, har sai bayan ranar 16 da gama hailar ta.

Mu dan tsaya kadan anan kafin muci gaba muyi tunanin meyasa akace haka?

Dalilin hakan kuwa shine,ranar 14 kwai ke zuwa, to idan s**a sadu ranar 12, kada mu manta Maniyyi sai yayi kwanaki 3 kafin ya mutu, to kunga idan s**a sadu ranar 12, maniyyin nan yananan a mahaifar yana jiran ranar 14 a saki kwan, zai zauna na tsawon kwanakin 12,13,14 kafin ya mutu, to kunga zasu ci karo ranar 14, kuma babu abinda zai hanashi sarrafa wannan kwan,saidai wani hukunci na ubangiji!,har sai bayan ranar 16 ne saboda shi kuma kwai yakan yi kwanaki 2 kafin ya mutu!

To wadannan kwanaki 5 din, watau 12,13,14,15 da 16 da gama Hailar mace, su ake kira da DANGER PERIODS(k**ar yadda dakta Kabir Yusuf Danwurin Dutsi ya taba yin takaitaccen bayani kwanaki), ma'ana kwanaki masu hatsari, an kira su da hakane saboda idan dai aka sadu da Mace a wadannan kwanakin to kuwa tabbas zata samu ciki, sai dai idan Mulkin Ubangiji ya shigo ciki, kuma idan ma'aurata na son yin FAMILY PLANNING,to wadannan kwanakin
zasu kaucewa saduwa aciki, ba sai sun sha magani ba, sai dai idan Mulkin Ubangiji ya shigo ciki.

NOTE:-

Gameda danger period da akayi magana,akan samu variation daga mace zuwa mace(Wajen farawa da gama al'ada)for that,wannan zai zama as a guideline ne kawai!

Bissalam✋

07/03/2023

Copied from Lafiya uwar jiki
~ Kina fama da kaikayin gaba, kuraje, fitar da ruwa mai wari?

~ Kashi tamanin (80%) cikin dari (100%) na sanyin gaba bashi da alaka da jima'i.

~ K**ar yadda mutum yake wanke bakin sa (brushing) haka ya k**ata mace kullum ta canza under wear nata.

~ Barin under wear a jiki fiye da kwana daya yana haifar da:
- Kaikayi gaba
- Warin gaba
- Fitar da ruwa
- Kuraje

~ kada a hada wankekken under wear da kaya masu datti.

~ Ayi kokorin siyan under wear wanda akayi shi da auduga (cotton), a kiyaye amfani da na roba (nylon).

~ Gaban mace baya bukatar a wanke shi da sabulu, ayi amfani da ruwan dumi ( ba mai zafi sosai ba).

~ Lokocin al'ada a dinga canza auduga (pad) akai akai (a kalla so biyar a wuni).

~ A dinga shan ruwa akai akai domin yana taimaka wajen bada kariya.

Lafiya uwar jiki

Ƙasar Jamus Ta Kirkiro Injin Kyankyasa JariraiKasar Jamus ta kirkiro wani inji da zai rika raino tare da kuma kyankyasar...
26/12/2022

Ƙasar Jamus Ta Kirkiro Injin Kyankyasa Jarirai

Kasar Jamus ta kirkiro wani inji da zai rika raino tare da kuma kyankyasar jarirai irinsa na farko a duniya.

Sunan injin ‘Ecto Life’ kuma zai samar da duk wani abu da jariri yake bukatar a cikin mahaifiyarsa har ma da kari.

An shafe sama da shekara 50 ana kirkirar wannan injin, wanda manyan likitoci da masana s**a yi dafifi wajen tabbatuwarsa.

Injin zai iya kyankyasar jarirai 30,000 a cikin shekara guda.

A cewar wanda ya kirkiri injin a birnin Berlin na Kasar Jamus, Hashem Al-Ghaili, y ace injin zai kawo karshen matsaloli da mata ke fuskanta yayin daukar ciki, musamman masu fama da ciwon daji wanda likitoci s**a ce ba za su sake haihuwa ba.

Kazalika, injin zai kawo mafita ga matan da ke mutuwa wajen haihuwa, matan da ake yi wa tiyata yayin haihuwa, matan da ke yawan barin juna biyu da sauransu.

Injin Ecto Life da zai ke kyankyasar jarirai
Injin zai taimaka wa kasashen da yawansu ke raguwa; Japan da Bulgeria da kuma Koriya Ta Kudu ta hanyar haifa musu yara masu yawa.

Ecto Life zai bayar da dama ga iyaye su koyawa jaririnsu irin yaren da suke so ya tashi da shi tun yana ciki.

Babban abin da ya fi daukar hankalin duniya game da ‘Ecto Life’ shi ne za a iya zabar wa jariri yanayin hallitar da ake so ya zo duniya da shi, misali za a zabar launin fata, yanayin ido, gashi da sauran yadda ake so sassan jikinsa su kasance.

Har wa yau, za a iya amfani da injin wajen kara kaifin basirar jariri.

A cewar Al-Ghalil, Ecto Life zai bai wa jarirai kariya daga kamuwa da cututtuka da suke kamuwa a lokacin da suke cikin iyayensu mata.

Sai dai abin tambaya a nan shi ne, duniya za ta karbi wannan injin ta rika amfani da shi, idan har hakan ta kasance, mece ce makomar iyaye ke nan wajen haihuwa?

ZUBAR DA JINI GA MACCE MAI K**A DANA AL'ADA (Abnormal va**nal bleeding)dukkanin jinin da baya da tsayyen lokaci yana zub...
09/12/2022

ZUBAR DA JINI GA MACCE MAI K**A DANA AL'ADA (Abnormal va**nal bleeding)

dukkanin jinin da baya da tsayyen lokaci yana zuba duk lokacin da yaga dama to na matsalane (Irregular Vaginal Bleeding? )akwai wanda xai zowa mace lokacin datake period , wato idan tana al,ada amma kwanakin data saba yi ya zarcesu , yaci gaba da xuba har zuwa wasu kwanaki koma daya tafi yadawo

akan samu wasu lokuta mace taga jini sau biyu sannan kuma idan jinin yazo yakan xuba sosai tareda daukar kwanaki yana zuba. SBD haka dukkanin jinin da xaizowa mace haka to na zuwan wata matsala ne ko kuma wani yanayin wanda yafaru ba'a sani ba kuma ya haddasa bleeding

Iya adadin kwanakin da muke gani wanda mace sai ta cikasu kafin al'adar ta kara tsagayowa sune kwanaki 28. Sannan bayan haka tayi kwana biyu zuwa kwana bakwai (2-7) tana zubar da jininta

sannan kuma koda wannan jinin yazo bazai zuba dayawa ba wato zuba mai tsanani wacce xata kawo matsala

Jinin da bana lafiya ba shine

jinin da mace zata gani yana yi mata zuba maitsanani

jininda mace zata ga ya 6ata kayan baccinta

jinin da mace zata ga yana yawan lalata pad wato da zarar ta saka pad dasauri zata ga yajiqe

jinin da mace zata ga yanayi mata zuba musamman wajen yin fitsari taga ya lalata gurin

Haka kuma dukkanin jinin da zai fitowa mace duk bayan sati daya baza'a ta6a kiransa na lafiya ba, jinine na wata rashin lafiya wato matsalace wacce zata iya faruwa a wasu Sassan jikinta na haihuwa.

ABUBUWAN DAKE HADDASA IRIN WANNAN ZUBAR JININ SUNE

1. nafarko shine macen da ta karato lokacin tsufanta wato lokacin da take gab data daina al'ada (menopause).

2. cututtukan dake k**a Sassan haihuwa na mace (Diseases of the Female Reproductive Organs )

3. ciwon dajin dake k**a farjin mace, ko kuma wannan matsatstsen guri a bakin mahaifar mace, koma mahaifar gabaki dayanta (Cancer of the va**na, cervix, uterus, and ovaries)

4. akwai kuma kumburin kwan mace wato (Ovarian cysts) itama wannan matsalace dakan faru a wasu matana

5. karin mahaifa (fibroid)

6. Akwai kuma wasu kwayoyin hallitta masu k**a dana cikin mahaifa wadanda ke tsirowa a wani 6angare na jikin mace wato (Endometriosis) wadannan kwayoyin hallitar suna kwaikwayon abubuwan da kwayoyin halittar dake taimaka wa mata wajen zubar da jinin haila ako wane wata, ta yadda suma zasu fashe su saka mace tariqa zubar da jini.

7. karancin sinadarin estrogen

8. Amfani da wasu magunguna k**ar na tsarin iyali ko kuma allura

9. Matanda basa da wasu sinadarai na protein masu tsaida zubar jini wato Clotting factors wanda wannan matsalar ana gadontane Iherrited bleeding disorder wato (hemophilia)

Akwai abubuwa masu dan dama bazamu iya lissafo suba Sai dai mufadi wasu , shawara dai itace duk maifama da irin wannan matsalar maganar gaskiya tana buqatar ganin likita

Address

Torankawa Karaye
Karaye

Telephone

+2347036193147

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kula Da Lafiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Kula Da Lafiya:

Share