09/05/2023
Gaskiya ne wannan haka yake
KISSA!!!
A zamanin khalifa Umar dan Khattaab, wasu mutane uku s**a zo masa suna rike da wani saurayi s**a ce, Ya Amiral muminina! Wannan mutum ya kashe mana mahaifinmu.
Umar: kai donme ka kashe musu uba?
Saurayi: Ni makiyayi ne, rakumata ce ta ci itaciyar gonar mahaifinsu, sai mahaifinsu ya bugi rakumin da dutsi, rakuma ta mutu, ni kuma na dauki dutsin na buge shi
ya mutu.
Umar: saboda haka zan tsaida haddi akanka.
SAURAYI: ka saurara mini kwana uku, mahaifina ya mutu ya barni da kanwata da kuma dukiya, idan ka kasheni dukiyar da yar uwata zasu tozarta Kamini Uzuri naje na raba Dukiyar.
Umar: wa zai lamunceka?
Saurayi ya duba cikin mutane sai ya nuna Sahabi "Abu Dhar".
Umar: ka lamunce masa Ya Aba Dharr?
Abu Dharri: na'am
Umar: ba ka san mutum ba ka lamunce, to idan ya gudu haddi zai koma kanka.
Abu Dharr: na yarda.
Saurayi ya tafi, aka kwana biyu, an shiga na so uku, saurayi bai zo ba,
Hankalin kowa ya tashi akan Abu Dharri kar haddi ya koma kansa.
Kafin sallar magariba sai ga saurayi ya zo a gajiye, ya tsaya a gaban khalifa Umar.
Saurayi: na mika dukiyar ga kawuna yanzu ina hanunka, ka tsaida haddi
akaina.
Cikin mamaki Umar ya ce: me ya dawo da kai bayan ka sami dama da za ka
iya gudu abinka?
Saurayi: na ji tsoro, Kar a ce cika alkawari ya Kare
cikin mutane.
Umar ya juya ga Abu Dharr: me ya sa ka lamunce
masa?
Abu Dharr: na ji tsoro, kar a ce alheri ya Kare cikin
mutane.
Wannan jawabi ya yi tasiri ga masu Neman jinin ubansu, s**a ce sun yafewa
saurayi.
Umar: don me?
S**a ce: muna tsoro, kar a ce afuwa ta Kare a cikin mutane.
Ni ma na isar muku da wannan labari ne don ina tsoron kar a ce kira/tunatarwa zuwaga aikata alkhairi (wato da'awa) ya Kare cikin mutane. Don Allah kai ma ka tura kar ace yada alheri ya qare cikin mutane.
Allah Kaji Kan Malamanmu da sauran yan uwanmu das**a Rigamu Gidan Gsky
Allah yasa aljannah ce mahadar mu 🤲
Kamal lawal masanawa.