
13/12/2024
Gobe Asabar Za'a Fara SHAYI a Katsina,
Sashen Lafiya Na Harkar Musulunchi (ISMA) Daliban Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na farin cikin sanar da al'umma shirin fara gudanar da SHAYI / KACIYA kamar yanda aka saba gabatar wa a kowace shekara a gobe Asabar - Lahadi 12th -13th Jimadal Thany, 1446 (14th - 15th December, 2024) insha Allah!
Ana bukatar a kawo yaran👬da za'a yiwa KACIYAR da karfe 6 na safe. Za'a fara Screening da tantance yaran @6:30am,
Za'a dauki sunayen yara (30) a kullum a tsarin wanda ya fara halartar muhallin gabatar da KACIYAR @ Markaz Katsina
Akwai tsarin DRESSING 🧻a ranakun Litinin da Talata ga yaran da aka yiwa KACIYA , insha Allah,
Iyayen yaran da za'a yiwa KACIYA su bincika su nemi ADDU'AR🤲🏻 da ake karantawa yara a 📚 Addu'o'i Ma'asurai daga A'immah🕋(SA) kafin da bayan gabatar da SHAYI domin samun tsari daga dukkan sharri da karin albarka ga 'ya'yan mu,
Ana iya tuntubar wadannan Numbers domin karin bayani:
+234 706 326 8186
+234 803 654 3231
✍🏼 ismakatsinamedia