
27/03/2025
AWA NAWA KO KWANA NAWA MACE KE OVULATION?
-------
Ovulation shine lokacin da mace take fitar da kwai sai kwan ya shiga hannun mahaifa domin ya haɗu da kwan namiji. Idan s**a haɗu lokacin ne ciki ya shiga.
Fitar da wannan kwan na mace yana faruwa ne kuma ya kare a duk wata sau ɗaya kuma yana lasting daga awa 12 zuwa awa 24.
Idan kafin ovulation da kwana biyu ko uku a ka samu mace ta sadu da mai gidan ta, kwan maigidan (s***m) zai tafi zuwa hannun mahaifa ya jira kwan mace sai ciki ya shiga.
Idan kuma mace ta yi ovulation sai kuma a ka yi dace kwan namiji ya shigo kuma s**a haɗu tsakanin awa 12 ko 24, nan ma ciki na iya shiga da ikon Allah.
Wani lokacin rashin fahimtar yaushe ne ya dace a sadu idan ana buƙatar haihuwa yana sa a dade ba'a samu juna biyu ba.
Dafatan kun fahimci wannan bayanin.
Na yi bidiyo akan wannan kuma iya kalla a profile ɗina.
Kuna iya ajiye tambayoyin ku a koment in sha Allah zamu amsa.
Allah Ya sa mu dace.