Gidauniya Tv

Gidauniya Tv Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gidauniya Tv, Medical and health, Katsina.

Babban Kuskuren Da Matasa Zasu Yi Shine, A 2023, Zabar Shuwagabanni, Marasa Amfani,Daga Muhammadiyyah, Mai Matasa, Shin ...
28/11/2021

Babban Kuskuren Da Matasa Zasu Yi Shine, A 2023, Zabar Shuwagabanni, Marasa Amfani,

Daga Muhammadiyyah, Mai Matasa,

Shin Menene Makomar Matasa a siysance kuma wace irin gudunmuwa zasu iya bayarwa domin cigaban al'umma, hausawa na cewa da ruwan ciki ake jan na rijiya, Siyasa 6anda wawa shin kasan menene ake cema Siyasa?

Fasali na farko sharhi akan siyasar Najeriya, siyasa wata abuce, wadda ake takawa tsakanin jarumai, da jarumai, domin su fuskanci, yadda lamarin al'umma da kuma duk da yake Siyasa macece amman kuma sunanta jarunta a haka ake yawan kiranta dashi, hakan yasa masana harkokin Siyasa, ke kiranta da mace mai ciki ba'a san mai zata haifa ba, haka zalika tana da danbarwa da rikice-rikice k**a daga uwayen jam'iyu har zuwa ga yan takara, da masu zaben su, waton al'umma,

Hasali na biyu shine danbarwa dan Siyasa da aka zabe ya hau kan karakar mulki, zai iya zama dan Siyasa, ko dan takara zai iya fitowa ko zai iya yin Siyasa, don Allah domin ya kawo cigaba acikin al'ummar da yake wakilta,

Zai iya zama dan Siyasa ko dan takara zai iya fitowa ko zai iya yin Siyasa, domin kasuwanci ya zuba jarinsa domin ya sha romon ribarsa,

Danbarwar farko kana daga jam'iyyar ka har zuwa ga al'ummar kasa ba kowa ne yake marhaban lale da zuwan ga ba amatsayin dan takara, ba idan har a kasan noma ne a gonar rogo, waton ummace zata gaida aisha ba taro ba sisin kobuba balantana, ahu duk da cewa kowa yasan nagartarsa, da amanarsa, da kuma mu'amalar sa da halayensa, da tausayin sa da kyautatawar sa duk hakan zai zama ansha wakar shata, ne agun jama'a sai ayi birissi da nagartarsa domin son abin duniya da kwadayin abin hannunsa shine ke jafe matasan mu da nasani,

Danbarwar ta gaba kuma shine da zaran an zabe dan takara mai sun cigaban al'umma koda baya da abin ungo karba zai ga bari ya ramawa al'ummar da s**a zabeshi, adalci da s**a yi masa zai sa aiki a gabansa ba tunanin kudin da ya kashe a yayin kamfen saba zai tausayawa Mutane fiyeda yadda aka tausaya masa zai samar da ruwan sha da inganta makarantu daukar matasa aiki da dai sauransu,

Ga kuma wani kalubale da matasa suke ciki shine rashin amfanin bin cancanta wajen zaben dan takara domin darhami da sulallai da yake dasu duk da ansan rashin nagartarsa da rashin amanarsa da rashin taimakon al'umma da rashin tausayin su, wanda jalla wa azza ya cire masa zaka ga dan takara sun garzayo suna cinikayya da mutanen gari,

Rago yaja baya sai dai gyara shirin fada sai yace a shirya yake gobe za'a fita gaishe gashe sai ka ga matasa ido ba kwalli sun nufi hanyar kuwace kuwace suna shelar ai wani ne domin Mutane basu ko san shi ba, bayan yazo ya nemi kwastomomin sa kuma ai kuwa anan ne gizo ke saka sai idan baka hau a yanar gizo ba, wannan yace lado yayi kaza wancen yace mati yayi kaza, waccen tace Muhammadiyyah yayi kaza wayancen kaji suna fadin ai baba dan audu ya turoshi, yayi takara kuma duk da baya wa'dannan abubuwan sai yanzu da yake da bukata da jami'a yazo yana yin wa'dannan abubuwan shi kuwa kwadayyi rufe ido yake ka tura mota ta tafi ta barka a dajin kwadayayyun kuraye,

Sai kaga yan social media har fada suke a tsakanin su da cin zarafin junansu akan wani can wanda baya iya azurtasu domin kwadayi kaga suna cima junansu zarafi kuma yan takarar nan suna can kansu a hade yake ku kuma kuzo kuna cima kanku tuwo a kwarya wannan shine ake kira danbarwar Siyasa bazamu taba samun sahihin wakilci ba, idan har bamu cire kwadayin abin duniya ba,

Bayan cin zabensa zai fara tunanin taya zai mayarda kudinsa da ya kashe muku a wajen yankin neman zabe zai yi birissi daku domin ya fahimci ba aiki ne a gabanku, ba daman ba t**i tuka tuka makarantu ilimi samarwa matasa abin dogaro da kai daukar dawainiyyar Mutane duk basu a gabansa, domin dan Kasuwa kuka zabo kasuwanci kuma baya son faduwa sai dai riba zancen karba wayarku domin baku da amfani a kare shi,

Yaku matasan mu na Najeriya baki daya Siyasa fa yanci ce kowa nada ra'ayoyin yayi wanda yake so amman ku sani babu wani dan takara wanda bai san halinmu ba, kowa jiran yake yaga dan takara ya fito ya wasa wugarsa to dahaka muke son mu samu sauyin Shugabanci muna sayar da kimarmu da Mutuncin mu agun wasu wadanda basu iya azurtamu ko su Allah ne ya azurtasu to suma me zai hana mu fuskanci gaskiya mu koma ga wanda ke azurtawa kowa kowa ku duba a duk fadin jihar kebbi babu inda ake kashe kashe k**ar yankin Zuru, bamu da tsaro Ingantacce, makarantu suna bukatar gyara ba, Ingantaccen limi matasa basu da aikin yi babu hanyoyin kasuwanci

Tambayata anan shin akwai wanda aka bata kashe dan uwansa a wannan hare-haren,? Shin akwai wanda ya taba bin hanya sanadiyar rashin hanya yayi hadari har ya rasa kafarsa ku hannunsa,

Shin akwai wanda ya kare Makaranta wani nason yaje gaba bai da hali wani kuma yana son yaje sami aiki bai samu ba,

Shin akwai wanda ya taba kai mahaifiyarsa ko dan uwansa aka Bashi magani kyauta ace inji wani mai wakiltar ku,

Shin akwai wani acikin ku da aka baiwa aikin gwamanati ko aka baiwa abokin ka ace inji wani mai wakiltar ku sai ta faru a kanka,

Adalci a Siyasa ya k**ata masu wakilcinmu ku sani kowa yasan akwai kudaden da ake baiwa kowane mai wakili domin ya yiwa Mazabunsa aiki tun daga dan majalisar jiha har majalisar tarayya da majalisar dattawa

Amman kawo yanzu banda wani yunkurie da masu wakilcinmu a Zuru s**a yi ba, duba da yadda mai wakiltar Kontagora da wasu mazamu keyima al'ummar sa goma ta arziki ga aiki ga samarwa matasa aikin gwamnati waton mai solar kuma akwai takwaransa a jihar kebbi waton wanban koko ya raba motoci masu yawan gaske

Kuma ya samarwa matasa aiki bila adadi tambayarmu ana shin kaima ba dan majalisar tarayya bane haka zalika idan ka koma a yankin Sanata ka duba irin aikin da sanatoci ke yi a yankin katsina har mukabula s**ai da juna samarwa matasan su aikin yi gwamnatocin mai girma Sanata bala na Allah kai waye ka samarwa aiki haka zalika a yankin suru Aleiro da wasu wajajen a jihar kebbi yan majalisun jiha suna aiki kala kala,

Address

Katsina

Telephone

+2349066113052

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gidauniya Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Gidauniya Tv:

Share