14/04/2025
ƘISSAR AS'HABUL UKHDUD (MA'ABOTA RAMIN WUTA)
Daga shafin Bashir Halilu.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya faɗi ƙissar waɗannan mutane a Alkur'ani mai girma, cikin suratul Buruwj, ayah ta huɗu, Allah Ya ce:
قُتِلَ أَصْحَابُ الْأُخْدُودِ • النَّارِ ذَاتِ الْوَقُودِ • إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ • وَهُمْ عَلَى مَا يَفْعَلُونَ بِالْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ • وَمَا نَقَمُوا مِنْهُمْ إِلَّا أَن يُؤْمِنُوا بِاللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ • الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ •
Ma'ana
4. An la'anci ma'abota rami (na azabtar da muminai).
5. Na wuta mai ruruwa.
6. Yayin da suke zaune a gefenta.
7. Alhali su suna kallon abin da suke aikata wa muminai.
8. Babu kuwa abin da suke tuhumar su da shi sai don kawai sun yi imani da Allah Mabuwayi, Sha-yabo.
9. Wanda Yake da mulkin sammai da kasa. Allah kuma Mai ganin komai ne.
Acikin wannan Ƙissa, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya la'anci ma'abota wani wawakeken rami, wanda s**a haƙa s**a hura wuta a cikinsa ganga-ganga, s**a riƙa jefa muminai a cikinsa da ransu, yayin da suke zaune a gefen ramin suna kallon yadda suke azabtar da muminai. Ba don wani laifi da suke tuhumar su da aikatawa ba, sai don kawai sun yi imani da Allah Mabuwayi, Sha-yabo, wanda shi ne kadai mai mulkin sammai da kasa, kuma mai ganin komai.
Annabi (SAW) ya ba da labarin waɗannan muminai da aka yi wa wannan azaba ta jefa su cikin ramin wuta, kamar yadda ya zo a hadisin da Muslim [ #3005] ya ruwaito daga Suhaibu dan Sinan (Allah ya kara masa yarda).
A taƙaice, hadisin ya bayyana cewa: "A da can an yi wani sarki kafiri, yana da mai yi masa aikin sihiri. To lokacin da mai sihirin ya tsufa sai ya bukaci Sarki ya zabo wani matashi daga jama'arsa don ya koya masa sihiri, domin ya ci gaba da wannan aiki nasa ko bayan mutuwarsa. Sarki ya amsa masa, ya tura masa wani saurayi wanda zai rika koyon sihiri a wurinsa.
A hanyar saurayin ta zuwa wurin malaminsa mai sihiri, sai yake gamuwa da