12/04/2025
TAKAITACCEN TARIHINHABBATUS SAUDA
Ita Habbatus sauda wata kwayace baqa, girmanta kamar na kankanen gero. Wannan kwaya cike take da albarka da kuma tasiri mai ban mamaki.
Tarihi ya nuna cewa, hakika Habbatus sauda dadadden magani ne wanda aka san amfaninsa da dadewa, a kasashen gabas da kuma Asia. Wadannan kasashe sun dade suna amfani da habbatus sauda tun fiye da shekaru 2000 da s**a gabata.
Babu shakka musulunci yazo ya iske ana amfani da habbatus sauda ya kuma tabbatar da tasirinsa ga dan adam. Don haka ma sai ya sanya shi cikin jerin shara'antattun magunguna.
Sai dai baa samu nasara game da fitar da man habbatus sauda ba sai a shekarar shekarar shekarar 1959. Kamar yadda baa gano matsayin tasirinta dangane da kwayoyi masu garkuwa ga jikin dan adam ba sai shekarar 1986. An kuwa samu wannan gagarumar nasara ne sakamakon tsattsauran bincike da kuma gwaje gwaje na musamman dangane da hakan.