08/01/2025
Wannan abune da yazama k**ar canfi, a duk lokacinda yaro yafara hakori, sai ya rika zawo, iyaye da dama na ayyana cewa hakoran ne ke janyo yin zawon. Shin ko hakanne?
Acikin wannan rubutu zamusan hakan
American Academy Of Paediatrics ta ayyana cewa fitowar hakori bashida wata alaka ka tsaye wajen janyo zawo ga yara, da ake sanya ran cewa hakora ke janyo shi.
Hakora na fara fitowa yara akalla wata 6 bayan haihuwa, wanda a wannan lokacin ne mafi yawancin iyaye ke fara ba yaransu abinci. Kasancewa yana daukan tsawon lokaci kafin masarrafar abincisu ta saba da wani sabon abinci (bayan nono da suke sha) kan janyo canji akan yadda suke kashi izuwa zawo.
Bugu da kari a wannan lokacin ne yara ke rasa garkuwar jiki da s**a samu daga iyaye mata lokacin haihuwa, dalilin raguwar garkuwar jikin, gashi kuma sun fara rarrafe, s**an iya taba wani abu susa bakinsu sannan su iya cin kwayoyin cuta da zaisa su zawo.
Ba iya wannan kadai ba, akwai wasu ababen dake taka rawar gani wajen janyo wannan gudawar
1. Kwayoyin cuta irinsu bacteria da virus, samun damar shiga cikin yaro daga daya daga cikinsu na kaiwa ga yin zawo, kuma ana iya daukansa daga wani zuwa wani, yanada muhimmanci akara himma wajen tsafta domin magance zawon yara.
2. Rashin dacewar jiki da abincin,
Wasu nauikan abinci na zamowa abun wahala ga yaran su iya nikasu, hanya daya ta nuna hakan ita ce yin zawo, Idan kika ba yaro abinci kikaga yai zawo ki canza masa wani.
3. Wasu nauikan magungunan irinsu antibiotics
4. Wani kuma zawon na faruwa hakanan.