Khadijatu Maggie

Khadijatu Maggie Health

🍼 Kula da Kai Bayan Haihuwa (Postnatal Care)Bayan haihuwa, jikin mace yana bukatar kulawa ta musamman domin ya koma yadd...
04/03/2026

🍼 Kula da Kai Bayan Haihuwa (Postnatal Care)

Bayan haihuwa, jikin mace yana bukatar kulawa ta musamman domin ya koma yadda yake, kuma don kare lafiya ta da ta jariri. Ga muhimman abubuwan da ya kamata a kula da su:

1️⃣ Hutu da Barci

Ki samu isasshen hutu.

Ki kwanta idan jariri yana barci.

Guji yin aiki mai nauyi a makonni 6 na farko.

2️⃣ Cin Abinci Mai Gina Jiki

Ki ci abinci mai dauke da:

Kayan lambu da 'ya'yan itatuwa

Abinci mai gina jini (kamar nama, wake, kifi)

Madara da kwai

Ki sha ruwa sosai, musamman idan kina shayarwa.

3️⃣ Tsaftar Jiki

Ki rika wanke gabanki da ruwa mai tsafta.

Ki canza pad akai-akai idan jini (lochia) yana fita.

Idan an yi miki dinki (episiotomy ko CS), ki kiyaye wurin ya kasance a tsaftace.

4️⃣ Shayar da Jariri

Ki fara shayarwa cikin awa daya bayan haihuwa.

Ki shayar da jariri nono kadai na tsawon watanni 6.

Nono yana taimakawa mahaifa ta matse da wuri.

5️⃣ Zuwa Awo Bayan Haihuwa

Yana da muhimmanci ki je awo bayan haihuwa a asibiti ko cibiyar lafiya.

Awo na farko yawanci cikin kwanaki 3–7, sannan mako 6 bayan haihuwa.

Wannan yana taimakawa gano matsala da wuri.

6️⃣ Alamomin Hadari (Ki Gaggauta Asibiti Idan:)

Zubar jini mai yawa sosai

Zazzabi

Warin jini mara dadi

Ciwon ciki mai tsanani

Jin bakin ciki ko kuka ba dalili (postpartum depression)

7️⃣ Tsarin Iyali

Ki tattauna da ma’aikacin lafiya kan hanyoyin tsarin iyali domin ba jiki damar hutawa kafin wani ciki.

Share, like, comment and follow for more

Khadijatu Maggie

04/03/2026

Astagfirullah!!!😭
Allah yasa muna daga cikin 'yantattun bayinka.🙏

Mahimmancin Zuwa Awo (ANC – Antenatal Care)Zuwa awo (ANC) yana nufin zuwa asibiti akai-akai yayin da mace ke da ciki dom...
04/03/2026

Mahimmancin Zuwa Awo (ANC – Antenatal Care)

Zuwa awo (ANC) yana nufin zuwa asibiti akai-akai yayin da mace ke da ciki domin a duba lafiyarta da ta jariri. A cewar World Health Organization, ana bada shawarar mace mai ciki ta je awo akalla sau 8 kafin haihuwa domin kula da lafiya yadda ya kamata.

Muhimmancin Zuwa ANC

1️⃣ Gano matsala da wuri
Ana gano cututtuka kamar hawan jini, ciwon suga na ciki, anemia, ko infection tun da wuri domin a fara magani.

2️⃣ Kare lafiyar uwa da jariri
Awo yana rage hadarin mutuwar uwa da jariri yayin ciki ko haihuwa.

3️⃣ Samun allurai da kariya
Ana ba da allurar rigakafin tetanus da sauran kariya masu muhimmanci.

4️⃣ Shawara kan abinci mai gina jiki
Likita ko jami’in lafiya zai ba da shawara kan irin abincin da ya kamata a ci domin girman jariri.

5️⃣ Shan magungunan kariya
Ana ba da iron da folic acid domin hana karancin jini da wasu nakasu ga jariri.

6️⃣ Bibiyar girman jariri
Ana duba bugun zuciyar jariri da girman ciki domin tabbatar da komai yana tafiya daidai.

7️⃣ Shiri don haihuwa lafiya
Za a koya miki alamomin haihuwa da kuma lokacin da ya kamata ki je asibiti.

Lokacin Fara ANC

Da zarar mace ta tabbatar da ciki (ko ta yi zaton tana da ciki), yana da kyau ta fara zuwa awo tun cikin watanni 3 na farko (first trimester).

03/03/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Salisu Suleiman, Ashiru Iliya, Ruqaiyat Usman Abubakar, Zahra Ajmal, Sadiya Muhammad Noor, Abdullahi Musa, Abubakar Ayuba Al'araby, Amina Shettima Nur, Atiku Mashkur Ingade, Ibrahim Ibn Abubakar, Maryam Maryam, Muhammad Sulaiman Durr Dass, Comr A A Suleiman, Abbas Aliyu, Sulaiman Muhammad, Abdu-Aziz Adam Umar, Ayeesha Kalallawa, Khadeeja Bello, Mustapah Babagans, Maymunah Muhd, Modu Kyari Kolo, Ahmadu Umar, Abubakar Abdullahi Yindiski, Fatima S. Maga, Fatima Abdurrahim, Hassan Wanka, Ameera Musa, Okasha Muhammad Usman Guda, Nura A M Muhammad, Fatima Abubakar, Ummu Khalil, Abdurrahaman Yakubu, Mmn Hanan, Ser'eiid Yunus, Queen Butter, S Aisha Idrees, Grace Lumi, Amatullah Muhammad, Adam Shehu Maigayya, Amatullah Mohammed, Waheed Usman Ibraheem, Sariyyatu Abba Sani, Rukayya Musa, Ummi Usman, Fateemah S Aleeyou, Sadeeya Rabee U Abba, Jaasetse Aminu, Zarah Abdullahi, Da Ud Abdulhamid, Rauda Marwan

Yadda ya kamata ki kula da kanki idan kina da ciki (juna biyu) 🤰Ciki lokaci ne mai muhimmanci sosai, don haka kula da la...
03/03/2026

Yadda ya kamata ki kula da kanki idan kina da ciki (juna biyu) 🤰

Ciki lokaci ne mai muhimmanci sosai, don haka kula da lafiya yana taimaka miki da jaririnki ku kasance cikin koshin lafiya.

1️⃣ Ziyartar asibiti akai-akai

Ki rika zuwa antenatal clinic (ANC) tun daga farkon ciki. Likita ko jami’in lafiya zai:

Duba lafiyarki

Auna jini da fitsari

Ba da shawarwari da magungunan da s**a dace

2️⃣ Cin abinci mai gina jiki

Ki ci abinci mai:

Furotin (kwai, wake, nama, kifi)

Ganye da ‘ya’yan itatuwa

Hatsi kamar shinkafa, dawa, alkama

Shan ruwa mai yawa

Ki rage:

Abinci mai yawan mai da s**ari

Gishiri fiye da kima

3️⃣ Shan magungunan da aka baki kawai

Ki sha Folic Acid da Iron kamar yadda likita ya bada shawara.

Kada ki sha magani ba tare da shawarar ma’aikacin lafiya ba.

4️⃣ Hutu da isasshen barci

Ki samu hutu sosai.

Ki guji daukar kaya masu nauyi.

Ki kwanta a gefe (musamman gefen hagu) domin saukaka gudan jini.

5️⃣ Tsafta

Ki kula da tsaftar jikinki da tufafinki.

Ki rika wanke hannu akai-akai.

Ki kula da tsaftar farji amma kada ki sa wani abu a ciki ba tare da shawara ba.

6️⃣ Gujewa abubuwa masu illa

Kada ki sha taba ko barasa.

Ki guji zama kusa da hayaki ko sinadarai masu cutarwa.

7️⃣ Kula da motsa jiki mai sauki

Motsa jiki kamar tafiya a hankali yana da anfani, amma ki guji wahala sosai.

8️⃣ Alamomin haɗari da ya kamata ki je asibiti nan take

Zubar jini

Matsanancin ciwon ciki

Ciwon kai mai tsanani da kumburin kafa

Raguwa ko daina motsin jariri (idan ciki ya kai watanni masu yawa)

Khadijatu Maggie

🤰 Alamomin Shigar Ciki (Early Signs of Pregnancy)Ga wasu daga cikin alamomin da mace za ta iya gani idan ciki ya shiga:1...
03/03/2026

🤰 Alamomin Shigar Ciki (Early Signs of Pregnancy)

Ga wasu daga cikin alamomin da mace za ta iya gani idan ciki ya shiga:

1️⃣ Tsayawar Al’ada (Period bai zo ba)
Wannan shi ne alama mafi yawan gani, musamman idan kina da al’ada mai zuwa a kai a kai.

2️⃣ Tashin Zuciya da Amai (Morning Sickness)
Yakan fara daga mako na 4–6 na ciki, wasu lokuta da safe ko duk lokacin rana.

3️⃣ Ciwon Nono ko Taushinsa
Nono na iya yin zafi, kumburi, ko yin duhu a gefensa (ar**la).

4️⃣ Yawan Fitsari
Saboda canjin hormone, mace na iya fara yawan zuwa bayan gida.

5️⃣ Gajiya Mai Yawa
Jiki na iya yin kasala da saurin gajiya ba tare da wani dalili ba.

6️⃣ Canjin Sha’awar Abinci
– Kin iya jin son wasu abinci sosai
– Ko kuma kin fara jin ƙyamar wasu abubuwa (musamman ƙamshi)

7️⃣ Ciwon Mara Kaɗan
Wani irin ɗan ciwon mara kamar na al’ada.

8️⃣ Ɗan Zubar Jini Kaɗan (Implantation Bleeding)
Wasu mata na iya ganin ɗan jini mai sauƙi kafin lokacin al’ada.

🧪 Yadda Zaki Tabbatar:

Yi gwajin ciki (Pregnancy Test) bayan kwanaki 3–7 da al’ada ta wuce.

Ko ki je asibiti a yi miki gwajin jini ko na fitsari.

⚠️ Lura: Ba kowace mace ke ganin dukkan alamomin ba. Idan kina da shakku, gwaji shi ne mafi inganci.🌸

Khadijatu Maggie

03/03/2026

Bar ganin kin yi aure, ki kiyayi laulayi😭😭

Khadijatu Maggie
03/03/2026

Khadijatu Maggie

01/03/2026
Khadijatu Maggie
28/02/2026

Khadijatu Maggie

🏥 HEALTH PYRAMID READINGHealthy Habits – Short Sentences🧼 1. WashWashWash handsWash hands with soapWash hands with soap ...
28/02/2026

🏥 HEALTH PYRAMID READING

Healthy Habits – Short Sentences

🧼 1. Wash

Wash
Wash hands
Wash hands with soap
Wash hands with soap and water.

💧 2. Drink

Drink
Drink water
Drink clean water
Drink clean water every day.

🥗 3. Eat

Eat
Eat fruits
Eat fruits and vegetables
Eat fruits and vegetables daily.

🏃 4. Move

Move
Move your body
Move your body every day
Move your body to stay strong.

😴 5. Sleep

Sleep
Sleep well
Sleep well at night
Sleep well for good health.

🩺 6. Check

Check
Check your health
Check your health often
Check your health at the clinic.

Share and follow:
Khadijatu Maggie

Pelvic Inflammatory Disease (PID)🩺 MENENE PID?Pelvic Inflammatory Disease (PID)Cuta ce ta kumburi da kamuwa da ƙwayoyin ...
28/02/2026

Pelvic Inflammatory Disease (PID)

🩺 MENENE PID?

Pelvic Inflammatory Disease (PID)
Cuta ce ta kumburi da kamuwa da ƙwayoyin cuta a:

Mahaifa (Uterus)

Bututun haihuwa (Fallopian tubes)

Ovaries

Yawanci tana faruwa ne saboda kamuwa da cuta ta hanyar jima’i ba tare da kariya ba.

⚠️ ALAMOMI

✅ Ciwon ƙasan ciki
✅ Zubar ruwa mai wari daga farji
✅ Zazzabi
✅ Ciwon lokacin jima’i
✅ Rikicewar al’ada
✅ Jin zafi lokacin fitsari

🚨 ME YAKE FARUWA IDAN BA A YI MAGANI BA?

❌ Toshewar bututun haihuwa
❌ Rashin samun ciki
❌ Ciwon ciki mai tsanani na dindindin
❌ Ciki a wajen mahaifa (Ectopic pregnancy)

💊 MAGANI

✔️Magani sai dai likita ya rubuta, yawanci ana bada:
▪️Ceftriaxone allura (sau ɗaya)
▪️Doxycycline (kwanaki 14)
▪️ Metronidazole (kwanaki 14)
✔️ Gama shan magani gaba ɗaya
✔️ Abokin jima’i ma ya sha magani
✔️ Guji jima’i har sai an warke

🛡️ HANYOYIN KARE KAI

✔️ Amfani da kariya (Condom)
✔️ Gwajin cututtukan jima’i akai-akai
✔️ Gaggawar zuwa asibiti idan an ga alamomi

📍 Sakon Muhimmi:
PID cuta ce mai warkewa idan an gano ta da wuri. Kada ki ji kunya – ki nemi taimakon likita da wuri

Khadijatu Maggie

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Khadijatu Maggie posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share