19/01/2026
Ba kowanne ciwon kai ba ne Malaria ko Typhoid 🗣
Ga wasu manyan dalilan ciwon kai da mutane da yawa ke fama da su 👇
1️⃣ Damuwa (Stress)
Tunanin da ya yi yawa, damuwar zuciya, da matsin lamba na rayuwa na iya janyo tsukewar tsokoki a kai da wuya, wanda ke haifar da ciwon kai{ɗan uwa kabar ajiye damuwa aranka please rayuwace kafii wanii wlh what ever the situation..😎
2️⃣ Yawan kallon waya/paper(Excessive screen time)
Dogon zama kana kallon waya, laptop ko TV yana gajiyar da ido da kwakwalwa, har ya janyo ciwon kai. Har da zafin ido..
🫵 Ni kaina ina ciki 😅 gaskiya na fiye latsa waya wlh.
3️⃣ Rashin barci mai kyau
Idan kana kwana kana amfani da waya, barci zai rikice. Rashin isasshen barci yana daga cikin manyan abubuwan da ke kawo ciwon kai.
4️⃣ Rashin shan ruwa (Dehydration)
Karancin ruwa a jiki na iya janyo ciwon kai.
👉 Bari nane-mo ruwa nasha🗣
5️⃣ Wasu magungunan hawan jini (BP drugs)
Wasu magungunan BP na iya janyo ciwon kai, musamman a farkon fara shansu ko idan an ƙara dose for reminder nasan a pharmacy anfada muku.
6️⃣ Karancin sugar / tsallake abinci
Rashin cin abinci a lokaci yana rage sugar a jini, wanda ke kawo ciwon kai, jiri da kasala. {Glucose is single most important source of energy for all tissue}
7️⃣ Sinus infection
Toshewa ko kamuwa da cuta a sinus na haifar da matsin lamba a goshi, idanu da hanci, wanda ke janyo ciwon kai.{kayi Google sinus😎}
8️⃣ Hawan jini mai tsanani
Hawan jini sosai na iya janyo ciwon kai mai tsanani, yawanci ana jin sa a bayan kai.
9️⃣ Migraine
Migraine nau’in ciwon kai ne mai tsanani,{Allah yaraba mutum da Migraine kace Amiin wlh🤦
🔟 Yawan amfani da painkiller
Yawan shan maganin rage zafi na dogon lokaci na iya haifar da rebound headache – wato magani yana ƙara kawo ciwon kai maimakon ya rage. Ƴan amanar painkiller akula...
1️⃣1️⃣ Canjin hormones
Canjin hormones lokacin al’ada, ciki ko menopause na iya janyo ciwon kai ga wasu mata.
1️⃣2️⃣ Matsalar haƙori (Dental problems)
Ciwon haƙori, kamuwa da cuta, matsal