Abu Husam Herbal Medicine

Abu Husam Herbal Medicine Herbal Medicine

24/09/2022

DAGA ABINDA MUKA JARRABA AKAN CUTAR FATA.
___________________________________________
Hadin maganin dake magance cutar fata,kowacce iri!
******************************************

Wannan haɗin yana bukatar waɗannan abubuwan kamar haka:

Ammafa wannan bayani koda kuɗi wani kam baya yimaka shiba,koda zaka biya shi!

Wannan domin kune masoya addu'ar ku kawai muke buƙata ta ishe mu, mungode.

Zaku samo wadannan magunguna kamar haka:
(1)Man (Zubda)
(2)Garin habbatusauda
(3)Sassaken itacen wurshi
(3)Man gelu
(3)Turaren miski
(4)Lakan mai ko man shafawa.

Farko za'a fara kona wannan bawon itacen wurshi idan ya kusa ƙonewa sai akashe wutar,abusar dashi,idan yabushe sai adaka yayi gari atankade,sai asami kamar cokali biyu zuwa uku idan man shafawan ko lakan man dan kaɗanne.

Na biyu sai asami kwano ko tukunya sai azuba wannan lakan man aciki,ko kuma man shafawa basilin,sai adora awuta mara karfi sosai,ba wanda keci balbalba,ko kuma garwashi,idan wannan lakan man yanarke,sai kakawo garin habbatusauda cokali biyu kazuba kana jujuyawa,sai kazuba garin gawayi da kadaka na wannan bawon wurshi.

Sai kazuba wannan man juda ɗin aciki,kamar kwara 4-7 bayan kanarka shi.

Sai kazuba wannan turaren almiski din,sai kazuba man gelo cokali biyu amma kanyi kana gauraya shi da cokali ko wani abu daban na kayan aikin kicin.

Idan kagama zuba komai acikin wannan lakan mai ɗin sai kabar shi yayi minti 3-5

Sai kasauke kada aaje kusa da yara sai a kula sosai, za'a barshi sai yafara hucewa yafara kauri sai kasamo wajen da zaka juye, domin idan yasha iska zai koma yadaskare ya koma kamar man shafawa.

Don haka zaka zuba shi a wani mazubi bayan yasha iska,daganan zai daskare,to kasami man shafawa dake maganin cutar fata.

Harma yana ta'asiri bangaran shafar aljani da muggan mafalkayya.

Yana maganin kuraje kowadanne iri insha Allah.
Yana maganin kumburi.
Sannan yakan warkar da ciwo da sauri, kuma yakan fasa maruru batare da anyi masa wani aiki ba,zai fashe da kansa,yakan saukaka radadi na maruru kowanne.

Ina sanar daku cewa mazauna garin Kano masu bukatar ganina yanzu zaku riƙa samuna a kwanar goda bayan kasuwar kurmi insha Allah.

Dafatan Allah yabamu dacewa allahumma ameen.

Aljerian Islamic Chemist

22/09/2022
17/04/2022
22/02/2022
08/02/2022

AMFANIN ALBASA GA LAFIYAR DAN'ADAM

Ga kadan daga cikin amfanin ta:

1. Albasa tana taimakawa ga mutumin da yasuma idan aka fere ta aka sanya masa a kafar hancin sa yana shaka, in shaaAllah zai samu tashi in ba ta ajali bace.

2. Albasa na taimakawa wajen warware ko magance matsaloli irin su farfadiya, ciwon zuciya, ciwon ciki, ciwon suger, asthma, ulcer ta kirji, shock musamman idan aka hada ta da tafarnuwa.

3. Albasa na taimakawa masu matsalar bugawar zuciya heart attack idan suna yanka ta danya suna ci a abinci.

4. Albasa tana maganin daskerewar Jijiyoyin jini na zuciya.

5. Albasa tana taimakawa masu ciwon sugar wajen warkarwa musamman a samu babbar albasa ayi kwadon lansir da ita aci kullum.

6. Albasa tana taimakawa masu Hawan jini da masu matsalar zagayawar jini.

7. Albasa idan aka saka ta cikin Zuma amma sai an yanka ta kullum aci su a haka tana maganin zazzabi, mura, ko ciwon makogwaro, masu ulcer da matsalar urinary tracts infection ma suna iya chi kullum in shaaAllah za a samu lafiya.

8. Albasa na maganin ko taimakawa wajen maganin ciwon Kai na gefe ko daga goshi, idan aka kirba ta ko ita kadai ko da tafarnuwa aka sanya a inda kan yake ciwon.

9. Wanda Zuma, ko cinnaka, ko kunama ta harbe shi shima za a sama sa wannan a daure da bandage in shaaAllah za a samu lafiya.

10. Albasa tana tsaida habo a rika shakar garin ta ko haka nan a sanya ta a hanci arika shakarta.

11. Albasa na taimakawa wajen narkar da abinci.

12. Albasa na taimakawa wajen warkar da kunar wuta idan aka kirba ta aka dora akan kunar akwai zafi amma za ta bushe ba za ta tashi ba kuma za ta warke cikin kankanin lokaci da yardar Allah.

13. Albasa tana zama rigakafi ga mata wajen Cancer nono, hanji, da cututtukan mahaifa.

14. Albasa tana magance matsalar Jijiyoyi.

15. Albasa na taimakawa wajen magance matsalar amosanin kashi.

16. Albasa na magance yawan ciwon ciki na yara, musamman yellow din idan aka yanka ta slices aka tafasa ta sai a tsame idan ruwan ya huce aba yaro cokali daya karami duk bayan hour daya.

16. Albasa na taimakawa wajen magance matsalar cunkushewar kirji idan aka kirba ta aka hada ta da man kwakwa aka juye a cikin towel aka daure kirji da shi aka sanya t-shirts da za ta matse kirjin zuwa wani dan lokaci a cire ayi wanka.

17. Albasa tana taimakawa wajen magance matsalar tari, idan aka samu babbar albasa sai a raba ta biyu a sanya brown sugar akan ko wace sai a bar su zuwa hour daya sai a cinye duka sau biyu za ayi a rana.

18. Albasa tana taimakawa wajen magance matsalar ciwon kunne, idan aka kirba ta aka samu kamar safa ko tsumma ko towel aka saka a ciki aka daure sai a dora akan kunne din da ke ciwon, an samun lafiya in shaaAllah.

19. Albasa tana tsayar da jini idan aka samu yankewa kuma za ta zama kamar antiseptic za ta kare fata daga kamuwa da wasu cututtuka a dalilin raunin. Kokuma ayanka albasa daya cikin container a zuba zuma a rufe kamar da daddare zuwa safe a tace sai a rika shan 5ml sau uku a rana idan babba ne.

20. Albasa tana fitar da guba daga jiki misali ko zazzabi ko mutum yaji jikin sa ya kasa gane masa ko in kana so ma kaji canji a jikin ka to ka jaraba wannan.

21. A samu albasa daya a yayyanka ta slices amma kanana sai a hada man kwakwa Mai kyau sai a jera a kasan tafin kafa sai a samu farin kyalle ko bandage fari saboda ina son aga irin dattin jiki da za a fitar sai a daure kafar sai asa safa sai a kwanta da safe idan aka tashi sai a cire za a ga abubuwa ayi haka kamar kwana bakwai za aga dattin na raguwa kuma jikin ana kara samun lafiya ko kuma ana kara jin dadin sa. Adaure a jaraba wannan kowa ma yana iya yayi.

22. Albasa na taimakawa wajen magance matsalar amai, asamu farar albasa ko yellow sai a matseta wato ayi juice din ta sai a zuba cikin tea na na'a na'a cupi daya amma a bari sai tea din ya huce sai asha cokali biyu kanana na tea din na'a na'a bayan minti 5-10 sai asha juice din albasa din Shima cokali biyu kanana sai kuma bayan minti 5-10 asha tea din na'a na'a din haka dai har a daina aman in shaaAllah, don yana daukar kamar minti 20 kafin aman ya tafi duka.

23. Albasa tana tsaftace Gurbataccen iskan da muke shaka, idan aka yanka ta slices sai a ajiye a kusurwar daki ko gida duk wata bacteria ko virus da iskan ya kwaso zata cire ta da yardar Allah.

24. Albasa tana maganin ko hana cizon kwari idan aka sata a jiki.

25.Albasa tana hana zubewar gashi idan aka kirba ta aka kara ruwa kadan a rika wanke kai da shi duk sati sau daya.

26. Albasa tana hana kwari cin shuka ko flowers idan akayi feshin ta.

27. Albasa tana hana gara cin kaya.

28. Sanya albasa a jiki na hana fata kuraje.

29. WHO hukumar lafiya ta duniya ta amince da amfani da albasa wajen jinyar matsalar tari, ciwon huhu, ciwon na kirji, cunkushewar kirji, mura dasauran wasu matsaloli.

Allah ya kara muna Lafiya.

06/02/2022

YADDA ZA KA GANE AL-JANA TA AURE KA.

Da kuma yadda mace za ta gane Aljani ya aureta.

Idan aka ce Jinnul Ashiq ana nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji.

Daga shafin Albishir Islamic Medicine, masu yin rukiyyah da harhada magunguna na musulunci. Lambar waya 08162600700.

(1) Yadda namiji zai gane Aljana ta aure shi.

1-rashin sha‘awar aure ko jima'i sam-sam.
2-‘kin mikewar gaba sanda kai nufin yin jima‘i, alhali kuma haka kawai ma yana tashi.
3-‘kin fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana
iya zama a cikin marainan mutum.
4-saurin gajiya, yayin jima‘i da rashin iya komawa
5-jin motsi kamar tafiyar wani abu a ga6o6in
haihuwa yayin jima‘i.
6-rashin cimma bukatar jima,i.
7- in ka yi nufin yin jima‘i sai bacci ya dauke ka.
8- da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo
tun kafin ka fara.
9- komawar gaba da maraina su shige ciki.
10- yawan ciwon kai, 6acin rai mara dalili, faduwar
gaba, da dai sauran su.
11- haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka.
12- Yawan mafarki kana saduwa da wata mata.
13- Yawan samun matsaloli aduk inda ka je neman aure, sai maganar ta lalace.
14- Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai.
15- Matsananciyar sha'awa da tsoron mata.
Da dai sauransu.

Muna bayar da magunguna da addu'o'i kuma muna yin Ruq'yah ga masu irin wannan lalura. Lambar wayarmu 08162600700.

(2) YADDA MACE ZATA GANE AL-JANI YA AURETA

1- yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi acikin.
2- a duk lokacin da s**ai nufin saduwa kawai sa ta
ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al'adarta bane.
3- jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata fa‘ida.
4- suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba
ma ta ya dinga dawowa, ba zai shiga mahaifar ta
ba.
5- matsanancin ciwon baya ko kwankwaso.
6-‘kin yarda da jima‘i.
7- Za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban.
8- yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da
taron suna.
9- ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa
a cikinki ta ya fizgo wani abu, musamman idan kina da ciki.
10- yawan yin 6arin ciki ba tare da wani sanannen
dalili ba.
11- yawan mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke.
12- jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma har yana
dada girma, amma in likitoci s**a auna za su ce ba
su ga komai ba.
13- rashin son yin magana da kowa da jin haushin
mutane haka kawai.
14- tsanar mai gida haka kawai, alhali za ki ji kina sha'awar wasu mazan.
15- Jin wari mara dadi yana fito miki ko ‘kai‘kayin gaba da ‘kurajen
gaba.
16- Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba.
17- Idan mutum ya dage yana so ya aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi.
18- In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so suy mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fadar cewa wance kwarjini take musu.
19- Za ta dinga yawan zaman a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane.
20- Idan yarinya tana zuwa makaranta za a ga kokarinta yana raguwa kuma tana ramewa.
21- Yawan ciwon kai da yin jiri.
22- Faduwar gaba, musamman idan Magriba ta kusa.
25- Iadan mace ta fara barci sai ta ji an zungureta ta farka.

Da dai alamomi da yawa.

Muna bayar da magunguna da addu'o'i kuma muna yin Ruq'yah ga masu irin wannan lalura. Lambar wayarmu 08162600700.

Daga shafin ALBISHIR ISLAMIC MEDICINE.
08162600700.

Address

Bakin Kusuwa Kwaya Kusar
Kwaya

Telephone

+2348087196759

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abu Husam Herbal Medicine posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Abu Husam Herbal Medicine:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram