NANA Aisha Herbal Medicine center maradun

NANA Aisha Herbal Medicine center maradun Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from NANA Aisha Herbal Medicine center maradun, Medical and health, Opposite Alh Abubakar Aliyu maradun, Maradun.

21/10/2022

ABU SAƘAR ya ce: Gidajenmu a zamanin da sun kasance suna k**a sosai, sai ka nutsu sosai in ba haka ba sai ka afka gidan maƙocinka.

Wata rana Abu Saƙar ya gayawa matarsa ta haɗa abinci akwai baƙi da zasu zo bayan sallar Isha'i. Shi kuma ya fita don siyo ƴaƴan itace.

Bayan Magrib ya dawo gida, sai ya afka gidan maƙocinsa a bisa rashin sa ni. Ko da shigarsa, sai ya samu matar gidan a kwance tana shaƙar barci abinta. Da ya fusata sai ya ɗakko bulala ya zage ƙarfinsa y tsula mata har sau 3, ya fita yana cewa malalaciya bakya son aiki...!

Da fitarsa waje, sai ya lura ashe gidan maƙocinsa ya afka duk jikinsa sai ya mutu. Yana shiga gidansa ya tarar baƙi har sun ƙaraso ga matarsa ta haɗa abinci k**ar yadda ya umarta. Aka ci abinci, aka yi ta hira amma Abu Saƙar babu nutsuwa a tattare da shi.

Bayan kwana uku, Abu Saƙar yana sauraran maƙocinsa yazo ya tuhume shi da laifin dukan matarsa amma yaji shiru. Sai ya yanke shawarar yaje kasuwa ya sayo zinare ya bata don rarrashinta akan laifin da ya aikata ba bisa sani ba.

Abu Saƙar ya yi sallama da maƙocinsa, ya gaya masa duk abin da ya faru kuma ya bashi haƙuri.

Sai maƙocin yace: riƙe zinaranka kar ka lalata kyakkyawan aikin da ka aikata, tun kwana uku baya na ga canji a gidana, har abin da ban saka matata ba ma yi take, ina ma duk sati zaka lallaɓo ka zuga mata bulalar nan, tabbas ka taimake ni sosai....!

Address

Opposite Alh Abubakar Aliyu Maradun
Maradun

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NANA Aisha Herbal Medicine center maradun posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share