Mu'assasatuz Zãhiratul Islãmiyya

Mu'assasatuz Zãhiratul Islãmiyya Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mu'assasatuz Zãhiratul Islãmiyya, Safety & first aid service, Potiskum.

Az-zahiratul Islamiyya: makarantace, mu'assasace, tahada kan al-ummar musulmai, tareda taimakamusu, da bayyana ainihin addinin musulunci kamar yadda ALLAH ya aiko annabinshi da ita.

20/03/2026
Adalci kan Tsare Sheikh Sani Khalifa Ba Bisa Ka’ida Ba na Tsawon Kwanaki 23, Ba Tare da Bayyana Inda Yake Ko Barin Sa Ta...
03/01/2026

Adalci kan Tsare Sheikh Sani Khalifa Ba Bisa Ka’ida Ba na Tsawon Kwanaki 23, Ba Tare da Bayyana Inda Yake Ko Barin Sa Tattaunawa da Kowa Ba

An tsare Sheikh Sani Khalifa tsawon kwanaki 23 ba tare da bayyana inda yake, ba tare da sanar da iyalansa takamaiman laifi, kuma ba a barin sa magana da kowa ba, abin da ya saba wa ka’idojin doka da hakkin dan Adam.

Da farko, an rufe asusun bankinsa ba tare da wata sanarwa a rubuce ba. Lokacin da aka tuntubi bankinsa da ke Zaria, aka bayyana cewa ba za a iya bude asusun ba, sai dai ya je babban reshen bankin da ke Abuja. Bayan zuwansa Abuja ne jami’an tsaro s**a zo s**a tafi da shi, bisa zargin cewa wani soja da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki ya taba tura masa kudin naira miliyan biyu.

Sheikh Sani Khalifa ba shi da wata hulda kai tsaye ta kasuwanci ko sadarwa da wannan sojan. Abin da ya faru kawai shi ne wani almajirinsa ya san sojan, kuma ya taba hada su ta waya inda s**a gaisa kawai. Daga bisani, sojan ya karbi lambar asusun Mallam ta hannun almajirinsa, sannan ya tura Naira miliyan biyu domin neman albarka da addu’a, kamar yadda mutane da dama ke yi wa malamai, ba tare da wata alaka ta siyasa ko laifi ba. Koda ance duk wanda ya taba transaction da wannan sojan ne ake bi ake kamawa.

Hukumomi sun bayanna cewa list din wadanda ake zargin ma ba sunansa, kuma an tabattar da bayada lafin kome amma har yanzu ana tsare shi. Wannan hakan tayar da tambayoyi game da sahihanci da adalci na ci gaba da tsare shi.

Muna kira ga hukumomin da abin ya shafa da su bayyana inda Sheikh Sani Khalifa yake nan take, ko kuma a sake shi ba tare da bata lokaci ba, domin tsare mutum ba tare da cikakken dalili ba zalunci ne kuma sabawa dokane. Duba da cewa shi Kansa yunkurin juyin mulkin gomnatin nigeria ta karyatasa.

Senator Senator Uba SaniUba Sani
Asiwaju Bola Ahmed TinubuTinubu
Kashim ShettimaShettima

Fadar mai alfarma sarkin musulmi ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar 1 ga watan Rajab 1447AH
21/12/2025

Fadar mai alfarma sarkin musulmi ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar 1 ga watan Rajab 1447AH

Shugaba Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya Ta Tarayya Dake Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauch...
20/12/2025

Shugaba Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya Ta Tarayya Dake Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da sauya sunan Federal University of Medical Sciences, Azare zuwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi University of Medical Sciences, Azare, domin girmama marigayi fitaccen malami kuma dattijo a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Sanarwar sauya sunan jami’ar ta zo ne a matsayin girmamawa ga irin rawar da marigayin ya taka wajen yaɗa ilimin addini, tarbiyya da zaman lafiya a Najeriya da ma ƙasashen waje.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shahara wajen koyar da ilimi, da’awa da kuma tsayawa kan gaskiya da hadin kan al’umma.

A cewar Shugaban Ƙasa, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na karrama manyan ’yan Najeriya da s**a sadaukar da rayuwarsu wajen hidimar al’umma da ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ilimi da tarbiyya.

Shugaba Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin wani ginshiƙi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin kira ga Allah tare da koyar da addini.

Ya yi fatan zuri'arsa za su cigaba da ɗabbaƙa ayyukan alheri da babban malamin ya aiwatar a lokacin da yake raye.

27/11/2025

Ana gabatat da Addu'a wa shiekh Dahiru Usman Bauchi a majalisar Dokokin Jihar Bauchi

JANA'IZAR SHEHUSanarwa!   Sanarwa!!   Sanarwa!!!.Munasar Da Al'umma Cewa Gobe Juma'ah 28-11-2025 Sallan Janazan Maulana ...
27/11/2025

JANA'IZAR SHEHU
Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!.
Munasar Da Al'umma Cewa Gobe Juma'ah 28-11-2025 Sallan Janazan Maulana Sheik Dahir Bauchi.

Gobe juma'a bayan sallar juma'a za'a gudanar da jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a Masallacin gidansa dake kusa da kasuwar Central Market Bauchi

Wannan shine hoton gurin da za'a bunne gawarsa a wani bangare na Masallacin dake jikin gidansa, tun kafin rasuwarsa an tanadar da gurin da za'a bunneshi idan rayuwa tayi halinta

Muna sonka Shehu fiyeda Soyayyar dake Tsakanin Jiki da Ruhi Amma Ubangijinka yafimu Sonka. Innalillahi wa inna'ilaihirra...
27/11/2025

Muna sonka Shehu fiyeda Soyayyar dake Tsakanin Jiki da Ruhi Amma Ubangijinka yafimu Sonka.

Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un

Fitacccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi (RTA) ya rasu a cikin daren da ya gabata, za a sanar da lokacin gudanar da jana'izar Shehun Malamin nan kusa.

Ya Allah (SWT) ya yi masa rahama ya yafe masa dukkan zunubansa.

Madina ce Ta hadaDaga Amb Sheik Nasir Sheik Ado Musa
30/05/2025

Madina ce Ta hada

Daga Amb Sheik Nasir Sheik Ado Musa

Ana gwada ƙarfi akan raunana, a lokacin da ake buƙatar tanadar wannan ƙarfin don fuskantar miyagun da s**a addabi Ƙasa, ...
22/04/2024

Ana gwada ƙarfi akan raunana, a lokacin da ake buƙatar tanadar wannan ƙarfin don fuskantar miyagun da s**a addabi Ƙasa, s**a hana zaman lafiya.
Allah Ka shaida, bamu gani mun yi shiru ba ! Bamu amince ba !!
kuma mun barranta daga abinda aka yi !!!
Allah mun tuba Ka yafe mana

10/12/2023

Qafilatul Mahabbah

ALHAMDULILLAH

*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ALLAH Madaukakin Sarki*
*Tsira da Aminci Su Tabbata Ga Shugaban mu S.A.W.W*

*Jiya Asabar 9/12/2023 wanda yayi daidai da 25 Jumada II, 1445.*

*Cikin yardar ALLAH mun samu damar gabatar da Ziyarar jajantawa Ƴan uwa Mazauna TUDUN BIRI waɗannda Ibtila'in Bam ya faɗa masu, mun gabatar da ta'aziyya da jajanta masu akan wannan Ibtila'in, wanda Qadilatul Mahabbah ta gabatar Ƙarƙashin jagorancin Maulana Prof. Ibrahim Maqari, bisa wakilcin Jagororin Qafilah.

Bayan gabatar masu da Nasihohi, da jajanta wa Da Jawabi Mai Ɗauke Saqon Shugaban Qafilatul Muhabbah Prof. Ibrahim Maqari sai kuma aka hannanta masu tallafin kayan abinci a madadin Qafilatul Mahabbah.

Daga cikin abubuwan da aka hannanta masu sun hada da:-
*Buhun Wake guda 103
*Buhun Shikafa guda 107
*Taliya katan 105
*Omo catton 15
*Sabulu catton 20.

Shuwagabannin su da Jagororin su sunyi farin ciki da wannan Ziyarar. Da ga cikin abunda su ke cewa shine, irin wannan tallafin shi ne na farko da ya zo garesu daga Wata Ƙungiya ta Musulmi.

Kuma sunyi addu'ar fatan alkhairi ga Maulanmu Sheikh Prof. Ibrahim Maqari da sauran Shugabannin Qafilatul Mahabbah.

Daga karshe mun Samu rakiyar Jami'an tsaro kamar.
*Yan Sanda (Police) Mota 1
*Civil Defence Mota 1
Sai CJTF guda takwas 8.
AlhamdulilLahi.

QAFILA NATIONAL MEDIA TEAM
Yakubu Ibrahim Adam

Address

Potiskum

Telephone

+2349036363679

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mu'assasatuz Zãhiratul Islãmiyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Mu'assasatuz Zãhiratul Islãmiyya:

Share