23/02/2023
LARURAR BASIR (PILE/HEMORRHOIDS)
Basir (pile) yana nufin kumburin hanyoyin jini na ciki ko wajen dubura (a**s); sakamakon taruwar jini, damewar tsokokin dake rike dasu,.. Yana bayyana a siffa kamar wacce muke iya gani a hoton dake kasa. Ana kasa basir gida biyu: akwai na waje, sannan da na ciki, kamar dai yanda zamu iya gani a hoton dake kasa
Basir gama-garin larura ne da kan shafi mafi yawan mutane a lokuta daban-daban na rayuwarsu. Yana iya sake dawowa koda bayan magani
ABUBUWAN DAKE HADDASA BASIR
1. Yawan daga kayan nauyi
2. Yinkuri hade da ninshi yayin tsugunno a bayan gida
3. Dadewar gudawa
4. Rashin shan ruwa akai-akai yanda ya kamata
5. Dabi'ar matse bayan gida ko kin yinsa yanda ya dace
6. Dadewa a tsugunnon bayan gida
7. Dadewa a zaune
8. Juna biyu (Ciki)
WASU DAGA CIKIN ALAMOMIN BASIR
1. Fitar (jan) jini a bayan gida
2. Kaikayin dubura ko ciwonta
3. Jin alamun kurji a dubura
4. Fitar majina daga dubura
ABUBUWAN DAKE KARA YIWUWAR SAMUN BASIR
1. Rashin cin abinci mai zare-zare: kamar kabeji, cinye harzar lemo, alayyahu,...
2. Yawan shan Coffee ko lemukan kwalba/roba(dake dauke da sinadarin Caffeine)
3. Shan wasu magungunan kamar Codeine
4. Kiba
5. Shan barasa
MATAKAN KARIYA
Babban abin lura yayin gujewa basir shine; kaucewa duk wani abu da zai jawo taurin bayan gida, ninshi yayin bayan gidan ko matse su wadannan hanyoyin jinin
1. Guji dadewa a zaune
2. Shan ruwa akai-akai: yana saukaka yin bayan gida
3. Gujewa shan giya/barasa, yawan shan lemukan zamani
5. Cin abinci hade da gayayyaki
6. Gujewa dabi'ar ki yin bayan gida yanda ya dace
7. Motsa jiki, rage kiba
8. Kaucewa shan magunguna da ka
9. Tuntubar kwararru da zarar an fuskanci alamominsa
(Pharm.M.A.Bichi)
Allah bamu dacewa, amin
Domin karin bayani ko neman magani ko shawara za'a iya tuntubarmu a ofishinmu a shago na biyu (No2 Rogo Agro plaza akan titin Rogo-Karaye/ Rogo-Makarfi)
Ko kuma a number waya kamar haka
08145513979