02/01/2024
NAU'O'AN ALJANU:
An karbo daga Tha'alabatu Al-Khushanni R.A. yace: Manzon Allah S.A.W. yace:
"Aljanu kala uku ne:
1- Masu fikafikai suna fira a sararin sama.
2- Da wadan da suke macizai
3- Da karnuka.
4- Da wadanda suke tsayuwa"
Buhari: 2038. Muslim: 2174.
Larabawa tun a lokacin jahiliyya suna kasa Aljanu, ko suna basu sunaye gwargwadon irin yada suke gittoma mutane.
Kamar yadda Abi Usamatu Al-Jahiz ya fada a cikin Littafin:
"Fiqhulluga Wa Asrarrul Arbiyya"
Na Imamu Tha'alabi, a Babi na 17, Faslu Tartibul Jinn, S/108-109.
Ga yadda s**a zo:
1- Al-Jinnu: Suna nufin na asali.
2- Amiru: Mai zama tare da mutane.
3- Shaitan: Idan ya lalace ya zama masharranci
4- Arwahu: Mai gittoma qananan yara.
5- Malaku: Idan ya tsalkaka, ya kasance mai alkhairi.
6- Ifritu: Idan sharrin sa ya wuce wuri, sha'anin sa ya munana, cutar sa ta girma.
Ga wasu qarin Nau'o'an Aljanu da s**a shahara a bakin malam Bahaushe:
1- Aljanu Masharuwa, tabbas akwai su, idan sun shafi mutun s**an yawan sanya shi Ta'ammuli da ruwa, da yawan wanka da ya saba hankali, da wasa da ruwa, kuma s**an iya tsotsema mutun ruwan jikin sa.
2- Aljana Doguwa: Tabbas akwai su, akwai Maza akwai mata.
Hatsabibai ne miyagu masharranta.
Manya-Manyan bokaye ke aiki da su, da manyan attajirai da sarakuna da 'yan siyasa, duka dai karkatattu daga cikin su suna amfani da su.
Haka 'yan gungiyar asiri suna aiki da su sosai, da matsafa, da 'yan bori.
Su aikin su kawai shine yin "KISA" galiban, sune masu shanye jinin mutun da ruwan jikin sa, ko gora nawa aka qarawa wanda s**a shafa, nan take zasu shanye shi.
3-Akwai Aljanu Fitillu: masu yawan Ta'ammuli da wuta, da wasa da ita.
Idan s**a zo ga wuri suna yawan cinnama wurin wuta, da tayar da gobara marar Mafari a kasuwanni da gidajen mutane, da wuraren aiki (offices)
4- Akwai Aljanu Sa'idai.
Sun kasu zuwa:
* Sahihai.
*'Yan dagizgi. Da sauran su.
Suna yawan zama a wuraren da keda tuddai, da shararren wurin da kake wucewa a saman hanya ko a daji, haka suna zama a wurin S