17/04/2025
Allah ya gafartamar ya sa aljanna Firdausi ce makomarta Don darajjar manzo Allah Saw Amin ya Rabbi
Yau Shekaru 51 Da Kisan Aissa Diori Matar Shugaban Kasar Nijar (Diori Hamani) 1974.
A Rana mai Kamar Ta Yau 15 Ga Watan Afrilu 1974, akayi Juyin mulkin soja na farko a Kasar Niger, wanda Ya Kawo Karshen Gwamnatin Dior Hamani Tare Da Muguwar Aika-Aika Na Kashe Uwargidansa Hajja Aissa Diori Hamani.
Aissa Diori wanda aka fi sani da Aïchatou Diori matar Hamani Diori ce, kuma uwargidan shugaban kasar Nijar. An kashe ta a juyin mulkin Nijar a 1974.
Tarihin Rayuwa
An haifi Aissa Diori a Dogondutsi a shekarar 1928. Ta fito daga kabilar Fulani, ta auri malam Hamani Diori a ranar 9 ga Mayu 1945. Ma'auratan sun haifi 'ya'ya shida, ciki har da Abdoulaye Hamani Diori wanda daga baya ya zama dan siyasa kuma dan kasuwa.
Aissa Diori ta kasance Uwa ga kungiyar Union des Femmes du Niger (UFN), kungiyar da ta kunshi masu fasaha da dama, irin su Bouli Kakasi, wacce ta rera mata Wakokin Yabo. An kafa UFN a ranar 6 ga Oktoba 1958. A karkashin jagorancinta, kungiyar ta jaddada shigar mata cikin ayyukan al'umma, ilimi, da samar da ayyukan yi. Ta kafa ƙungiyoyin mata na kasa (UFN) wacce tayi tasiri Sosai ga dokar da ke kare mata a matsayin mata da uwaye.
Diori ta zama uwargidan shugaban kasar Nijar a ranar 3 ga watan Agustan 1960, lokacin da aka rantsar da mijinta a matsayin shugaban kasa. A cikin tsarin siyasar kasa da kasa, Aïssa Diori ta kasance wani bangare na kusan dukkanin tafiye-tafiyen da Mijinta yayi zuwa Kasashen Ketare. A Amurka, ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen ba da tallafinta ga Yara Yan makaranta bakaken fata da ake nuna musu wariyar launin fata. A lokacin da take Nijar ta damu da ilimin yaran makiyaya, domin Ganin an Basu ilmi.
An harbe ta har lahira a juyin mulkin da akayi a Jamhuriyar Nijar a 1974 a ranar 15 ga Afrilu 1974, da Wani Sajan Niandou Hamidou ya yi. Jami’an tsaronta na Abzinawa su ma sun mutu a juyin mulkin, al’amarin da ya kai ga rusa gwamnatin mijinta. Wacce ta gaje ta a matsayin Uwargidan Shugaban kasa itace Mintou Kountche.
Muhammad Cisse ✍