Association of sokoto state. physiotherapist

Association of sokoto state. physiotherapist Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Association of sokoto state. physiotherapist, Physical therapist, Wamakko, Sokoto.

Assalamu Alaikum warhamatulla
Barkan ku da zuwa shafin kwararrun likitocin physiotherapy ( likitocin jijiya,kashi,da kuma tsoka) na jihar sokoto babban dalilin bude wannan shafin shine domin ilmantarwa tare da fadakarwa hadi da wayar da kan alumma akan

20/11/2025

Amfanin Atisaye Ga Mai Juna-biyu

Sashin lura da lafiyar mata na likitancin fisiyo na da muhimmancin gaske ga masu juna biyu. Saboda bincike ya nuna cewa masu juna biyun da s**a halarci ajujuwan ɗaukar atisaye yayin rainon ciki na samun garkuwa daga wasu matsalolin rainon ciki da haihuwa kamar haka:

1. Magance matsanancin ciwon baya da ƙugu.

2. Rage haɗarin kamuwa da ciwon siga yayin rainon ciki.

3. Rage haɗarin kamuwa da hawan jini yayin rainon ciki, wanda alama ce daga cikin alamun da ke nuni da haɗarin samun jijjiga yayin haihuwa.

4. Bunƙasa aikin tsokokin ƙugu da ke taimaka wa uwa yayin naƙuda, domin haihuwa cikin sauƙi. Bunƙasa aikin waɗannan tsokoki zai rage haɗarin kasa haihuwa da kai; wanda ka iya tilasta yin tiyata/aiki domin ciro jariri.

5. Rage haɗarin samun matsalar ƙwacewar fitsara, ko kuma yayyon fitsari.

6. Rage haɗarin buɗewar ƙugu - matsala ce da ƙasusuwan ƙugu kan buɗe fiye da ƙima saboda ɓallewar tantanan da ke riƙe da ƙasusuwan ƙugu yayin naƙuda.

7. Magance matsalar kumburin ƙafa, tafin sawu.

8. Magance matsalar ƙwacewar fitsari yayin da kuma bayan haihuwa.

9. Rage samun ƙiba/ teɓa fiye da ƙima yayin da kuma bayan haihuwa.

10. Rage damuwa / yawan bacin rai.

11. Rage haɗarin haihuwar bakwaini da dai sauransu.

Sai dai, atisaye yayin rainon ciki na buƙatar tantance mai juna biyu kafin ta fara atisaye. Saboda haka, zai fi kyau a yi atisaye ƙarƙashin kulawar likitan fisiyo domin wanyewa lafiya.

Tuntuɓi likitan fisiyo a dukkan asibitocin da ke da sashin fisiyo (physiotherapy) domin fara ɗaukar atisayen rainon cikin domin samun alfanun da aka ambata.







© Physiotherapy Hausa

20/11/2025
20/11/2025

Hanyoyin Kiyaye Tashin Ciwon Gaɓoɓi Lokacin Sanyi

Ciwon gaɓoɓi lalurori ne da ke da tasirin gurgunta lafiya, ingancin rayuwa, walwala da tattalin arziƙin mutum. Akwai lalurori fiye da ɗari da ke da alaƙa da ciwon gaɓoɓi. Sai dai, akwai nau'in ciwon gaɓoɓin da s**a fi afkuwa a cikin al'ummar wannan yanki.

Lalurorin ciwon gaɓoɓi da s**a fi afkuwa sun haɗa da:

1. Amosanin gaɓa: ciwon amosanin gaɓa, wanda ake kira da "osteoarthritis" a turancin likita. Ciwon gaɓa ne sakamakon sauye-sauye da ke faruwa a gaɓa wanda ke janyo zaizayewar gurunguntsin gaɓa.

2. Ciwon sanyin ƙashi: ciwon gaɓa na sanyin ƙashi, wato "rheumatoid arthritis" a turancin likita. Ciwon gaɓa ne da ke afkuwa yayin da ƙwayoyin halittar garkuwar jiki, wato "immune cells", s**a rikice, a maimakon su yaƙi ƙwayoyin cuta da s**a shiga jiki sai su koma yaƙar ƙwayoyin halittar jiki.

3. Ciwon gawut: ciwon gaɓa na gawut, wato "gouty arthritis" a turancin likita, ciwon gaɓa ne da ke afkuwa idan sinadarin "uric acid" ya hauhawa fiye da ƙima a cikin jini, wanda hakan kuma ke haifar da taruwar gishirin "urate".

4. Harbin ƙwayoyin cuta: ciwon gaɓa ne sakamakon harɓin ƙwayoyin cuta kamar bakteriya, wato "septic arthritis" a turancin likita.

5. Ciwon gaɓa daga bugu: "traumatic arthritis", ciwon gaɓa ne sakamakon lahani ga gaɓa daga bugu, faɗuwa, faɗowa, haɗuran ababen hawa ko mummunan lahani daga wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.

Alamomin Ciwon Gaɓoɓi
Alamomin ciwon gaɓoɓi sun haɗa da:

1. Ciwo a gaɓa

2. Riƙewar gaɓa

3. Kumburi a gaɓa

4. Wahala, kassarewa ko nakasar aikin gaɓa.

Alaƙar sanyi da ciwon gaɓoɓi

Da farko, a nan muna magana ne a kan sananniyar ma'anar sanyi, wato sanyi kishiyar zafi ko ɗumi. Wato kamar sanyi daga yanayin sanyi, ɗari ko hunturu, sanyin danshi ko laima, da kuma sanyin damuna ko sanyin fadama da dai sauransu.

Tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi na daga cikin ƙorafe-ƙorafen da aka fi yi wa likita lokacin sanyi ko hunturu. Sai dai, kamar yadda muka fayyace bayani kan sabuban nau'o'in ciwon gaɓoɓi a sama, za mu ga cewa bayanin ya saɓa da tatsuniyar da ke yawo a cikin al'umma cewa sanyi ne sababin ciwon gaɓoɓin. Kamar yadda ake cewa, "tashi" ko "ta'azzara", wato ciwon gaɓoɓin daman yana nan sai dai sanyin ne kawai ke tayar ko ta'azzara shi.

To amma me ke janyo tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi?

Har zuwa yanzu, a kimiyyance, ba a san haƙiƙanin sababin tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi ba. Sai dai, ana alaƙanta tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓin da abubuwa kamar haka:

1. Raguwar zafi ko ɗumi a muhalli ko sararin samaniya.

2. Danshi, laima ko kaɗawar sassanyar iska a muhalli ko sararin samaniya.

3. Raguwa ko ƙarancin sinadarin bitamin D.

4. Gado: Mafi yawan mutane sun gaji ƙwayoyin halitta da ke tayar ko ta'azzara ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi. Saboda haka, akwai mutane ƙalilan da sanyin ba ya tayarwa ko ta'azzara musu ciwon gaɓoɓi.

Hanyoyin kiyaye tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi.

1. Sanya tufafi ko sutura mai kauri ko kuma a ninninka tufafi domin jiki ya kasance cikin ɗumi. Haka nan, ya kamata a sanya safar hannu da safar ƙafa da kuma sanya takalmi sawu-ciki domin kauce wa ratsawar sanyi.

2. Amfani da ruwan ɗumi yayin ayyukan yau da kullum, kamar: sha, alwala ko wanka. Haka nan, masu aiki ko sana'a da ruwa, za su iya zaɓar ruwan ɗumi ko kuma ɗumama jiki lokaci-lokaci a yini domin kasancewar jiki cikin ɗumi.

3. Hasken rana: Lokacin sanyi hasken rana a muhallahi na raguwa. Shi kuwa hasken rana muhimmin sinadari ne wajen samar da sinadarin bitamin D, wanda jigo ne wajen gina lafiyayyen ƙashi da kuma magance lalurorin da ke lalata ƙashi da gaɓa.

Yayin da hasken rana ya sauka a kan fatar mutum, fata na amfani da hasken ranar domin samar da sinadarin bitamin D. Saboda haka, akwai buƙatar shan hasken rana lokacin sanyi domin samun wannan alfanu.

Har wa yau, zai fi kyau a zaɓi awannin aiki lokacin da gari ya yi ɗumi idan hakan mai yiwuwa ne.

4. Ingantaccen abinci/abinsha: Cina 'ya'yan itatuwa, ganyayyaki da kuma datsar hatsi na samar da muhimman sinadaran kiwon lafiyayyen ƙashi da gaɓoɓi. Bugu da ƙari, rage siga a abinci ko abinsha da kuma rage sarrafaffun abinci ko abinsha na taimaka wa gaɓoɓi su zauna lafiya. Siga da sarrafaffun abinci ko abinsha na da haɗarin haddasa kumburi a gaɓoɓi.

5. Atisaye ko motsa jiki: Kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da shawarar yin atisaye ko motsa jiki aƙalla na mituna 30 a kullum. Atisaye na taimaka wa jiki ya kasance cikin ɗumi. Kuma gaɓoɓin jiki za su kasance cikin lafiya da ingancin aiki yayin ayyukan yau da kullum.

Daga ƙarshe, idan kana fama da ciwon gaɓa, akwai buƙatar ganin likita domin gano sababin ciwon gaɓar domin bin hanyoyin magancewa dogaro da sababin ciwon gaɓar da likita ya gano.

©Physiotherapy Hausa

Ku yi sharing domin wasu su amfana.

20/11/2025

Samar da waraka ba tare da ƙwayar magani ba, na daga manyan muradun likitan fisiyo.

Daga cikin kayan aikin likitan fisiyo wajen magance ciwon jiki da gaɓoɓi akwai "Ultrasound Therapy", tsari ne da ke aiki da "Ultrasound Waves" wanda na'urar Ultrasound Machine ke samarwa.

Yana taimakawa bunƙasa warkewar raunuka da ciwukan da ke gaɓoɓi, tsokoki, gurunguntsin gaɓoɓi, jijiyoyin tantani, da sauransu.

Amma ba kowane ciwo ne yake buƙatar Ultrasound Therapy ba, likitan fisiyo yana zaɓar hanyoyin da s**a fi dacewa da kowane irin ciwo domin magance shi.

Shin an taɓa yi maka Ultrasound Therapy da ka je fisiyo?

© Physiotherapy Hausa

20/11/2025
20/11/2025

Bayan yanke sashin ƙafa, likitan fisiyo yana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da aikin dungulmi domin ya dace da ƙafar roba a shirye-shiryen koya tafiya da ƙafar roba wanda mai koya tafiya da ƙafar roba, wato "prosthetist" a turance, yake koyawa marasa lafiya domin su iya tafiya da ita da kuma sauran yadda za su yi ta'ammali da ita a cikin ayyukan yau da kullum.

Duba aikin likitan fisiyo bayan tiyatar yanke sashin jiki a nan https://www.facebook.com/share/p/1Cce3gRx6j/?mibextid=oFDknk

© Physiotherapy Hausa

Copied:  | Daga cikin matsalolin da ke yi wa lafiyar baya barazana akwai sauye-sauyen da ke faruwa a ƙashin baya yayin d...
20/11/2025

Copied:

| Daga cikin matsalolin da ke yi wa lafiyar baya barazana akwai sauye-sauyen da ke faruwa a ƙashin baya yayin da shekaru ke ƙara miƙawa. Waɗannan sauye-sauye na iya shafar ƙasusuwan baya, tsokoki, fayafayan tsakankanin ƙasusuwan baya, tantanai, laka da jijiyoyin laka.

Yin buris da ciwon baya ko kuma ɗaukar ɗabi'ar shan maganin rage ciwo kullum na daga cikin haɗuran da ke iya janyo tiyatar baya can daga ƙarshe.

Adana kuɗinka/ki ba sai ka sayi maganin ciwon baya kullum ba, tuntuɓi likitan fisiyo a yau.

Daga cikin muradan likitan fisiyo shi ne taimaka wa mai ciwon baya shawo kan ciwonsa ba tare da shan maganin rage ciwo kullum ba tare da ceto mai ciwon baya daga barazanar tiyatar baya.

© Physiotherapy Hausa

20/11/2025

| Daga cikin matsalolin da ke yi wa lafiyar baya barazana akwai sauye-sauyen da ke faruwa a ƙashin baya yayin da shekaru ke ƙara miƙawa. Waɗannan sauye-sauye na iya shafar ƙasusuwan baya, tsokoki, fayafayan tsakankanin ƙasusuwan baya, tantanai, laka da jijiyoyin laka.

Yin buris da ciwon baya ko kuma ɗaukar ɗabi'ar shan maganin rage ciwo kullum na daga cikin haɗuran da ke iya janyo tiyatar baya can daga ƙarshe.

Adana kuɗinka/ki ba sai ka sayi maganin ciwon baya kullum ba, tuntuɓi likitan fisiyo a yau.

Daga cikin muradan likitan fisiyo shi ne taimaka wa mai ciwon baya shawo kan ciwonsa ba tare da shan maganin rage ciwo kullum ba tare da ceto mai ciwon baya daga barazanar tiyatar baya.

© Physiotherapy Hausa

Big shout out to my newest top fans! 💎 Fatima Imam UmarDrop a comment to welcome them to our community,
15/11/2025

Big shout out to my newest top fans! 💎 Fatima Imam Umar

Drop a comment to welcome them to our community,

14/11/2025

Har a yau sai ka sha maganin rage ciwon wuya kake samun sukuni?

Ciwon wuya na iya kawo cikas wajen gudanar da ayyukan yau da kullum, a wasu lokutan ma har walwala da bacci zai iya hana mutum.

Shan magungunan rage ciwo na iya rage ciwon wuyan na ɗan lokaci. Sai dai, da zarar aikin maganin ya ƙare sai kuma ciwon ya dawo sabo!

Muradin likitan fisiyo shi ne magance ciwon wuya daga tushe ba tare da dogaro da shan magunguna kullum ba.

Fara ban kwana da ciwon wuya, tuntuɓi likitan fisiyo.

© Physiotherapy Hausa

Address

Wamakko
Sokoto
481001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Association of sokoto state. physiotherapist posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Association of sokoto state. physiotherapist:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram