16/12/2025
Alhamdulillah amadadin kungiyar gyara kayanka youths Foundation Dandinmahe (Hisba) suna mika godiya ta musamman zuwaga Hukumar yan sanda dake garin Dandinmahe akan wani samame da hukumar ta kai jiya cikin dare a dakunan mata masu zaman kansu (Karuwwai) inda ake aikata alfasha suna laka gidan sauro ga fili suna kwana da maza inda jami'an yan sanda da yan vegilenty(yan banga) s**a fatattaki wadannan mabarnata.
Ko shakka babu wannan abin ayabane kuma cigabane mai alfanu gameda sha'anin tarbiyya da wannan ne muke yabawa shugabanninmu da malumanmu da kuma wannan hukumar ta yan sanda da yan vegilenty kuma wannan wani karfafawane ga aikin da kungiyar Hisba keyi agarin Dandinmahe ta kewaye Dafatar Allah ya shirye mu zuwaga tafarki madaidaici.
Sako da kungiyar gyara kayanka youths Foundation Dandinmahe (Hisba)
Abdullahi Sambo (Secretary)