24/04/2024
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta fara binciken Gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai. Kan abubuwa 8
A wani wasika da majalisar jihar Kaduna ta turawa kwamishinan kuɗi na jihar mai lamba LEG/S.382/VOL.II/615 Wasikar, mai dauke da sa hannun Barr. Sakinatu Hassan Idris
kwamitin majalisar zai fara bincikar tsohuwar Gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai kan abubuwa 8
Ciki har da
1: Kuɗin lamani na babban Bankin Duniya
2: bayani kan albashin da a biya ma'aikata tun daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2022
3: bayani akan kuɗaɗe da majalisar ta san da su yayin karɓar lamani
4: bayanin kwararru na kuɗi na jihar Kaduna tun daga watan Mayu na shekarar 2015 zuwa 2022
5: An bukaci a kawo rahoton hukumar KADRIS tun daga watan Mayu 2015 zuwa 2023
6: Rahoto akan sharuddan kashe kuɗi tun daga watan Mayu 2015 zuwa shekarar 2015 zuwa 2023
7: Rahoton kayan tallafi dake da alaƙa da lamani - tun daga watan Mayu zuwa 2015 zuwa 2023
8: adadin kudaden kwangila da a kashe da shaidar takardunsu tun daga watan Mayu na 2015 zuwa 2023