25/05/2025
Wata rana mun shiga Tiyata Ni da wani Consultant Gynecologist ɗan ƙasar India tare da wasu abokan aiki na mutum 3 (Kabiru Abdullahi from Ringim, Yusuf Buhari from Taura da kuma wani Anaesthetist from Kazaure) kan wata mata mai juna biyu wadda za'a yiwa Caesarian Section. Har ga Allah nayi takaici iya takaici a wannan ranar saboda abin ya isa rai ya ɓaci indai mutum ya san abinda ya k**ata musamman al'ummar musulmi. An zo da matar ɗauke da juna biyu amma PCV (Packed Cell Volume) ɗin ta is less than 20% wanda zaka iya kwatanta shi da rabin gallon na adadin jinin da yake yawo a cikin jikin nata har jaririn. A yadda lissafin yake shine, aƙalla tana buƙatar leda 5 zuwa 6 har jinin da za'a zubar a lokacin da ake tiyatar. Ita matar daga ƙauye suke, kuma daman an fiya samun irin wannan matsalar ta ƙarancin jini daga ƙauye.
Lokacin da za'a yi tiyatar, daga Ni, Perioperative, Anaesthetist ɗin har Surgeon ɗin babu mace a cikin mu. Dukkkan mu maza ne. Hakan bawai kashi bane saboda dole ce ta tilasta hakan. Amma abin takaice ne gare Ni dana duba cewa meyasa ake samun mata da yawa a Unit Unit, Wards Wards na cikin asibiti tun daga kan Emergency, Female Ward, GOPD, har zuwa Maternity, amma idan ka shigo ɗakin tiyata sai ka tarar 95% duk maza ne?😡
Abinda na ƙiyasta a raina a wannan lokacin shine: yanzu fa da ace matata ce a irin wannan yanayin, ko shakka babu mu ɗin dai mune zamu ƙare mata komai A to Z a wannan theatre ɗin k**ar yadda muka yiwa wannan matar koda zuciya ta bata so.
Duk da cewa addinin Muslunci yayi restricting mata shiga cikin wasu abubuwa da dama saboda gudun buɗe kafar fitina, amma har yanzu babu inda addini ya hana mata zuwa neman ilimin likitanci. Tunanin wannan ne yasa har yanzu wasu mutanen suke ganin k**ar ma haramun ne mata su tafi Jami'a yin karatun lafiya bayan kuma idan ka kalli abin a mahanga ta ilimi, ɓarnar ma tafi yawa a rashin zuwan nasu yin karatun. Wasu ma har yanzu gani suke auren ma'aikaciyar asibiti k**ar ɓatawa kai lokaci ne saboda ai bata da lokacin ka wanda kuma fa a hakan so yake idan ita matar tasa ta cikin gidan bata da lafiya, in a yadda yake so ne kawai mace 'yar uwarta ta duba masa ita.
Ban san daga wacce jiha kake karanta wannan rubutun nawa ba, amma dai a iya sani na, based on current clinical data, kaf jihar Jigawa babu mata mutum 50 waɗanda s**a yi karatun da ya shafi ɗakin tiyata tun daga kan Perioperative, Anaesthesia, har zuwa kan General Surgery. Kai yanzu kayi nazari da kanka, shin yanzu idan mahaifiyar ka, ƙanwar ka, budurwar ka ko kuma matar ka basu da lafiya, idan ta k**a dole sai an musu tiyata a dalilin haihuwa, Appendicitis, vaginal surgery ko kuma wani condition na daban daya tilasta cewa dole sai anyi tiyatar, tsakanin ka da Allah 90% na waɗanda zasu yi musu aikin su waye? Amsar dai itace ko baka so ɗin dai mune zamuyi kane-kane sannan mu kalli abinda a zahiri bai k**ata mu kalla ɗin ba. Wannan kaɗai ya ishe ka abin takaici.
Wannan abun fa bawai presumption bane ko kuma wani theory na daban. Magana ce ta zahiri wadda currently haka abin yake tafiya a ƙasar tamu musamman mu musulman da muke cike da religious discipline da al'adu masu ɗauke da tarin restrictions. Ka ɗauka cewa wannan abun har a kudu ma haka ne, amma ka sani muninsa yafi ƙarfi a ƙasar Hausa musamman mu nan Arewa.
Ina faɗa maka ne from fundamental experience and current healthcare situation. Ko kana so ko baka so, 95% na Operation Theater a Arewa a hannun maza yake (Both public & Private Hospitals). Hatta In charge ɗin ma namiji ne. Ko yanzu idan ka kai wannan matar taka, ƙanwar ka ko mahaifiyar nan taka cikin asibiti saboda wata larura da ta tilasta sai anyi mata aiki a ɗakin tiyata, ka sani dai maza ne zasu mata dirar mikiya koda haihuwa za ta yi, haka kuma koda mutuwa za ka yi saboda takaici. That's all I want to tell you.
Salisu Yakubu
RN, RNT, CT
08033990930
Lafiyar ka itace mafi muhimmanci a rayuwarka saboda haka, ka kula da ita da kyau