11/02/2018
SHAHADAR MALAM KASIM UMAR BAIWACE DAGA ALLAH. Inji Hajiya Kulu Umar Mahafiyar Malam Kasim.
Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato.
"Lalle a hakikanin gaskiya babu wani abu da yake damuna na bakin ciki ko bacin rai dangane da Shahadar Malam Kasim domin kuwa nasan wannan abin baiwace daga Allah (t), kuma wannan Shahadar da Malam Kasim yayi abuce wacce ya nema daga gurin Allah (t) domin kuwa a duk lokacin da yayi Sallah sai ya roki Allah (t) akan ya datar dashi da Shahada, kuma Allah (t) ya cika masa gurinsa ya bashi kuma Malam Kasim ya gama lafiya kowa yana sonsa."
Zamantakewarsa; "Dangane da zaman takewarsa da Makwabtansa Alhamdulillahi kowa sai san barka tareda Allah waddai da abinda aka yi masa. Jama'a nata kai da kawowa suna zowa yi mana Jaje suna fadin cewa sune s**ayi rashi."
"Malam Kasim bayada abokin Fada, Malam Kasim bayada abokin gardama, duk wata rigima da ta taso anan Gida da Waje komi girmanta Malam Kasim yakan dauki nayinta gurin maganceta."
"Ko dazu wata mata tazo tana bayani dangane da Shahadar Malam Kasim inda take cewa; " mu mukayi rashi domin kuwa Malam Kasim yasa an gyara muna matsalolin Ambaliyar Ruwan Sama da take ta damunmu Shekara da Shekaru, ta kara da cewa; Duk da barayi dake addabarmu zowar Malam Kasim a Unguwarnan tamu ya magance muna ita domin kuwa ada bamuda ikon fita muje cikin gari kafin mu dawo anyi mana sata, amma zuwan Malam Kasim ko bamu rufe gida ba ba abinda zai samu Kayanmu."
"Malam Kasim babu ruwansa koda zaluntarsa mutum yake yi yana zama tare dashi, wani lokaci Ni da kaina idan naga abin yayi yawa nakan yi masa magana sai yace inkyalewata kawai ai yana sane, kuma baya gayawa kowa akan cewa wane na zaluntarsa."
A karshe Hajiya Kulu Umar wacce take Mahaifiya ce ga Malam Kasim Umar Sakkwato ta roki Allah (t) ya sakawa Malam Kasim ga wadanda s**ayi Kisansa tareda rokon Allah (t) yaji kansa yakuma karbi Shahadarsa.