18/03/2016
Gwamnatin jahar sokoto ta kaddamar
da kwamiti akan kafa kampanin takin
zamani da na kula da Gidajen
Marayu.
Gwamnatin jahar sokoto ta kaddamar
da wani kwamiti da zai bada
shawarwari akan kafa wani kampanin
takin zamani a jahar.
Kampanin dai wani kampanin takin
zamni mai suna "prime Gold fertilizer
and chemical company" dake garin
Port Harcourt, jahar Rivers ne zai
gina shi.
Da yake kaddamar da kwamitin a
ranar Talata, sakataren gwamnatin
jahar sokoto Professsor Bashir Garba
yace aikin na kafa kampanin takin
zamni a jahar sokoto na da matukar
muhimmanci ga gwamnati. Kuma
gwamnati zata yi iya wayinta wajen
tabbatar da nasarar aikin.
Ya ce kwamitin zai yi bita da kuma
duba irin bukatun da kampanin prime
Gold ya turo . kuma zai yi yarjejeniya
ta adalci zakanin kampanin da
gwamnatin jaha.
Kwamitin har wayau zai bincika ya
bayyana wurin da ya dace a gina
kampanin da bayyana yadda
gwamnatin jaha ya kamata ta shigo
ciki.
A cewarsa " kwamitin zai bada
shawarwari akan yadda za a samo
kudaden da z a ayi aikin".
Kwamitin dai an bashi sati hudu ya
gabatar da rahotonsa. Kuma
kwamishinan kula daskararrun
ma'adinai na jaha Hon. Bello
Goronyo.
Sauran Mambobin kwamitin sun hada
da kwamishinan ciniki da
masanaantu Aminu Bello sokoto ,
Darakatan cibiyar an kasuwa Sani
Musa, wakilin maikatar kula da aikin
Noma, da na majalisar kula da
albarkatun kasa.
A halin da ake ciki , gwamnatin jahar
sokoto ta nada wani kwamiti wanda
zai kula da tafiyar da gidajen Marayu
a jahar.
Dr Malami Muhammad Bankanu shine
zai jagoranci kwamitin.
Sauran mammbobin kwamitin sun
hada da, Malam Nura Attajiri, Hajiya
Inno Attahiru, Dr Sadiya Umar Bello
da kuma Mustapha Tangaza wanda
shine zai zama sakataren kwamiti.