
04/05/2024
Wallahi datar da kake sakawa a wayarka sai Allah ya tambayeka wane amfani kayiwa addinin muslunci da wannan datar??
Wani bawan Allah yace:
Alhassan zan baka shawara, nace ok ina saurarenka 👂
Sai yace: kai ma’aikacin lafiya ne, kaje kacigaba da aikinka kana ɗaukar albashinka, Allah ya rufa maka asiri baka buƙatar komai awurin kowa
Nace: eh hakane
Sai yace: saboda haka kafitar da kanka acikin harkar addini, ba ruwanka da abunda ya shafe addini, kaje kacigaba da aikinka zaifi alkhairi agareka
Sai na yanke chat 💬 dashi a messenger ❌
Wallahi acikin mutane akwai wawaye, masu tunani irin na dabbobi 🥲
Wasu dagacikin mutane sun ɗauka duk wanda yake yiwa addinin muslunci hidima baida aikinyi ne, kuma wannan babban kuskure ne.
Shi addinin muslunci, addinin kowa-da-kowa ne
Kuma Allah ta’ala yabada umarni, kowa yasamu hanyar da zai taimake addini:
Idan kai malami ne, karantarda al’umma ilimin sanin Allah da bautawa Allah wajibi ne agareka
Idan kai ɗan achaba ne, ko ɗan keke napep dole kasamu hanyar da zaka taimake addinin muslunci acikin sana’arka
Idan kai ɗan kasuwa ne, kayi amfani da dukiyarka ka taimake addini (Fitar da zakkah, gina masallaci, gina makarantun islamiyya, taimakon mabuƙata, marayu da gajiyayyu) dole ne agareka
Idan kai mai tarin followers ne a facebook, Instagram, Tiktok ko Youtube ka taimake addini ta hanyar ɗora karatun malammai, kira zuwaga gaskiya, kira zuwaga alkur’ani da hadissan annabi saw.
Wallahi duk wanda yake da followers a social media, Allah ta’ala zai tambayesa a ranar alƙiyama shin ka isarda saƙona zuwaga followers ɗinka na facebook??
Manzon Allah saw yace: (بلغوا عني ولو آية)
Ma’ana ku isarda saƙona zuwaga al’umma koda ayah ɗaya ce 👌
A ƙarƙashin wannan hadisin ne yasa muke ɗora karatun malamman sunnah da jan hankalin al’umma zuwaga gaskiya da ƙauracewa ƙarya.
Allah yasa mudace
Alhassan Mai Lafia