11/08/2022
Me ya sa yarona ya kasa riƙe wuya, zama da tsaiwa a watannin da ya kamata?
Daga cikin larurorin da ke shafar jarirai ko yara yayin da suke cimma matakan girmansu akwai larurar 'shanyewar ƙwaƙwalwa' ko kuma 'dakushewar ƙwaƙwalwa' da a ke cewa "Cerebral Palsy" a turancin likita, wannan larura ce da kimanin mutum miliyan 17 ke fama da ita a faɗin duniya. Kuma ita ce larura mafi nakasa yara yayin girmansu. Wannan matsala ce da ta fi shafar motsin gangan jiki, magana/furuci, gani, da sauransu sakamakon 'shanyewar ƙwaƙwalwa'.
Yawancin yaran da matakan girmansu ke tafiyar hawainiya suna fama da 'shanyewar ƙwaƙwalwa' ne saboda lahanin da ke samun ƙwaƙwalwarsu kafin ta gama girma kamar:
1. Yayin rainon ciki: misali,
i - jirkicewar jigidar halitta, wato 'genetic mutation' a turance.
ii - haihuwar bakwaini, da sauransu.
2. Yayin haihuwa: misali,
i - doguwar naƙuda,
ii - shaƙewar jijiyar jini ta cibiya yayin naƙuda,
iii - shawara, wato rikiɗewar fatar jiki da farin ƙwayar ido zuwa rawaya/zabibi.
iv - matsanancin zazzaɓi bayan an haifi jariri ko kuma a watannin farko na rayuwa da dai sauransu.
v - Haka ma jariran da s**a gaza yin kuka nan-take bayan haihuwarsu na da haɗarin samun wannan matsala.
3. Bayan haihuwa: misali,
i - cutar sanƙarau, wato 'meningitis' a turance.
ii - zazzaɓin cizon sauro mai ratsa ƙwaƙwalwa, wato 'cerebral malaria' a turance kenan.
Alamomin 'shanyewar ƙwaƙwalwa' sun haɗa da:
1. Kasa iya motsa sassan jiki; saboda waɗansu yaran jikinsu na da rauni, waɗansu kuma jikinsu ko gaɓɓansu kan rirriƙe ne. Misali, waɗannan yara kan gaza iya riƙe wuya a wata 3, zama a wata 7 – 8, rarrafe da riƙe abu a miƙe a wata 9, tafiya a wata 12 da sauransu. Saboda haka, wuce lokacin da ya kamata yaro ya cimma ɗaya daga cikin matakan girma da aka sani a al'ada na nuni da cewa akwai matsala.
2. Kasa iya magana/furuci.
3. Dalalar da yawu/miyau.
4. Matsalar gani, juyewar ido ko hararagarke.
5. Matsalar/wahalar cin abinci da sauransu.
Abubuwan da ya kamata ka sani game da yara masu larurar 'shanyewar ƙwaƙwalwa' sune:
1) Duk yaro ɗaya cikin yara huɗu ba ya iya furuci/ magana.
2) Duk ɗaya cikin uku ba ya iya tafiya da kansa.
3) Ɗaya cikin yara biyu na da dakushewar kaifin basira yayin koyo.
4) Ɗaya cikin huɗu na da farfadiya.
Sai dai, abin takaicin shi ne 'shanyewar ƙwaƙwalwa' ba larura ce da ake shan magani a warkewa nan take ba. Amma ƙwararru na yin duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa yaran sun cimma matakan girman da za su iya kula da kansu cikin ayyukan yau da kullum ba tare da sun zama nauyi ga iyaye ba.
Mafi ban takaici daga wannan ma shi ne yadda sau da yawa al'umma da iyaye ke tunanin wai irin waɗannan yaran aljanu ne s**a taɓa su, ko s**a shanye musu gaɓoɓinsu, ko kuma wai suna da taɓin hankali ne. Wannan sam ba haka ba ne! Wannan ya kan sa a bar yaro a gida ba tare da kai shi asibiti ba, hakan zai sa yaro ya nakasa har ya tsuguna ɗungurungum.
Muna ƙara jinjinawa iyayen yaran da s**a fahimci wannan larurar kuma suke ƙoƙari ba gajiyawa wajen zuwa asibiti akai-akai. Muna sake kira da kada a gajiya ganin cewa ba a samun ci gaba cikin gaggawa. Ya kamata a sani cewa wannan matsalar ba a shan magani a warke nan-take, saboda haka haƙurin ziyartar asibiti akai-akai ita ce mafita kawai.
Likitocin fisiyo na gaba-gaba wajen tallafa wa rayuwar waɗannan yara domin su sami mafi ingancin rayuwa gwargwadon tsananin 'shanyewar ƙwaƙwalwar' da s**a samu.
Yaran da s**a sami kulawar likitocin fisiyo tun da wuri na cimma matakan girmansu kaɗan da kaɗan, gaɓɓan jikinsu su yi ƙwari har su kamo sa'anninsu. Ta wannan hanya ce kawai irin waɗannan yara ake temaka musu har su iya kula da kansu, su je makaranta ko su koyi sana'a bayan sun girma, maimakon barinsu su nakasa kuma su zama nauyi ga iyaye ko kuma mabarata a titinanmu.
Garzaya da yaro asibiti da zarar an lura da matakan girmansa na tafiyar hawainiya, ko kuma bayyanar wasu daga cikin alamomin da muka ambata a sama domin ba shi kulawa ta musamman tun da wuri don ceto shi daga nakasa.
Physiotherapy Hausa