16/06/2025
CIKAKKEN BAYANI AKAN AIKIN KODA WATO ( KIDNEY )
KODA: Wata halittace ta 'ya'yan ciki dake zaune k**ar tagwaye don cirewa mutum abubuwa marasa amfani k**ar, Guba, Fitsari, Zuffa(gumi) da sauran su.
Mafi yawan mutane nada koda guda biyu, wadansu kuma guda daya kuma a rayu, dukkansu sukan zauna waje guda. Mu sani cewa, akan haifi mutum da koda daya wadansu kuma akan cire bisa dalilin wata cuta. Amma akan rayu a haka.
AMFANIN KODA
1. Cire abu marar amfani daga jini.
2. Daidaita ruwan jiki.
3. Daidaita lafiyar ala'ura ga maza da mata.
4. Daidaita yanayin jini da samar dashi.
5. Taimakawa wajen samuwar alli na kashi.
MATSALAR KODA
Matsalar koda kan faru idan ta sami matsala ko ta lalace gaba daya, sai abubuwa marasa amfani su rika taruwa a jiki.
Lalacewar koda kan afku ba zato ba tsammani wanda in anyi magani matsalar kan kauce da wuri.
Koda kan iya lalacewa ba'a sani ba har saita rube wanda hakan shine matakin karshe na ciwon don ba'a cika warkewa ba.
BARAZANAR CIWON KODA.
Afkuwar matsalar koda kan karu k**ar sau 7 cikin dari a fadin duniya. A kasar mu najeriya, matsalar koda yakan kai k**ar ga mutum dubu a cikin kowace miliyan daya, kuma a yanzu sun kai k**ar mutane dubu dari da ashirin a wani bincike da aka gudanar.
ABUBUWAN DA SUKAFI JAWO CIWON KODA.
- Abubuwan dasukafi jawo ciwon sune k**ar haka:
- Hawan jini,
- Kunburin koda,
- ciwon sugar
Koda na iya lalacewa ta hanyoyi da dama har sukai matakin na karshe na ciwon koda har su sata rubewa. Akwai karin abubuwa dake sawa k**ar yadda aka fada a baya sune:
- Hawan jini.
- Kunburin koda.
- Ciwon suga.
- Marurun koda.
- Cutar jini na cikin kashi.
- Dakuma harbuwa da cuta.
ALAMOMIN CIWON KODA
-Yawan fitsari mai kala
- Fitsari mai kumfa
- Amai
- Ciwon kai
- Kaikai
- Kunburin kafafu ko ido.
- Haki
- Bushewar fatar jiki
MATAKI DA MAGANI
1. Fitar da fitsari ko ruwan daya lalace ta (Dialysis) da kuma guba ko datti da tsiyaye jini.
2. Saka ruwa ta wajen cibiya (peritoneal dialysis).
3. Canjen koda ta hanyar tiyata (fida) don akanyi dashen koda a kuma ajiye wacce aka cire akasan mara ta bangaren hagu.
Koda da aka dasa takanyi aiki da gaggawa, amma wani lokaci akan dan sami jinkiri.
Allah yabamu Lafiya Ameen
ALLAH YASA MU DACE