27/06/2025
Wata rana wani uba ya bawa ɗansa jaka cike da ƙusa, sai ya ce masa:
"Ɗa na, duk lokacin da ka ci mutuncin wani ko ka cutar da wani, ka je ka kafa ƙusa guda daya a jikin katangar lambunmu"
Yaron bai fahimci dalilin da yasa mahaifinsa ya ba shi wannan umarnin ba, amma ya yarda ya fara aikata hakan.
Duk lokacin da ya aikata wani abu mara kyau ga wani, k**ar magana mara dadi, ko fada, ko duka, sai ya tafi ya kafa ƙusa daya a jikin katangar.
Da lokaci ya ja, sai yaron ya fara canzawa. Ya fara iya sarrafa fushin sa, kuma adadin ƙusar da yake kafa wa ya ragu.
Har ya kai ga wata rana bai kafa ko ƙusa guda daya ba!
Cike da murna, ya garzaya wurin mahaifinsa ya ce:
“Baba, yau ban cutar da kowa ba, ban kafa ko ƙusa guda ba!”
Sai mahaifinsa ya ce:
"Madalla yaro na! Yanzu ka zama mutum wanda ke iya sarrafa halinsa da fushinsa! Amma har yanzu aikinka bai kare ba."
Yaron ya yi mamaki, sai ya ce:
“To me zan yi yanzu, baba?”
Sai mahaifinsa ya ce:
“Daga yau, duk ranar da ka shafe ba tare da ka cutar da kowa ba, ka cire ƙusa guda daga cikin waɗanda ka kafa.”
Yaron ya fara cire ƙusoshin, ɗaya bayan ɗaya, a duk ranar da bai cutar da kowa ba.
Har ya kai ga rana guda da ya cire ƙusa ta ƙarshe daga jikin katangar.
Yana cike da murna, ya je wurin mahaifinsa yana mai farin cikin sanar dashi nasarar da ya samu.
Sai mahaifinsa ya k**a hannunsa, s**a tafi wurin katangar, ya ce masa:
"Ina alfahari da kai ɗa na! Ka zama mutum mai kyauta da tausayi, wanda baya cutar da wasu.”
Sai ya ce masa:
"Amma ka kalli waɗannan ramukan da ƙusar da ka kafa s**a bari a jikin katangar.
Zaka iya cire ƙusar, amma ba za ka iya goge gurbin da s**a bari ba."
"Kamar haka rayuwa take da mutane, ɗa na.
Idan ka cutar da wani, k**ar ka soka masa ƙusa ne a cikin zuciyarsa.
Ko da ka nemi gafara ka daina, gurbin zai ci gaba da kasancewa a zuciyarsa.
Wannan rauni zai iya warkewa, amma zafin da ya haifar da tunaninsa zai iya kasancewa har abada."
Bashir Suraj Adam