Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture

Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture, Medical and health, Near Wudil General Hospital Kano, Wudil.

Wannan Shafi yana gabatar da Ayyukan mu ne na wanzanci da magungunan Gargajiya a zamanan ce dan sanar da Al'umma iron cigaban da ake samu a sana'ar tare da gabatar da irin magungunan mu ga mai bukata.

21/11/2025

Hanyoyin Kiyaye Tashin Ciwon Gaɓoɓi Lokacin Sanyi

Ciwon gaɓoɓi lalurori ne da ke da tasirin gurgunta lafiya, ingancin rayuwa, walwala da tattalin arziƙin mutum. Akwai lalurori fiye da ɗari da ke da alaƙa da ciwon gaɓoɓi. Sai dai, akwai nau'in ciwon gaɓoɓin da s**a fi afkuwa a cikin al'ummar wannan yanki.

Lalurorin ciwon gaɓoɓi da s**a fi afkuwa sun haɗa da:

1. Amosanin gaɓa: ciwon amosanin gaɓa, wanda ake kira da "osteoarthritis" a turancin likita. Ciwon gaɓa ne sak**akon sauye-sauye da ke faruwa a gaɓa wanda ke janyo zaizayewar gurunguntsin gaɓa.

2. Ciwon sanyin ƙashi: ciwon gaɓa na sanyin ƙashi, wato "rheumatoid arthritis" a turancin likita. Ciwon gaɓa ne da ke afkuwa yayin da ƙwayoyin halittar garkuwar jiki, wato "immune cells", s**a rikice, a maimakon su yaƙi ƙwayoyin cuta da s**a shiga jiki sai su koma yaƙar ƙwayoyin halittar jiki.

3. Ciwon gawut: ciwon gaɓa na gawut, wato "gouty arthritis" a turancin likita, ciwon gaɓa ne da ke afkuwa idan sinadarin "uric acid" ya hauhawa fiye da ƙima a cikin jini, wanda hakan kuma ke haifar da taruwar gishirin "urate".

4. Harbin ƙwayoyin cuta: ciwon gaɓa ne sak**akon harɓin ƙwayoyin cuta k**ar bakteriya, wato "septic arthritis" a turancin likita.

5. Ciwon gaɓa daga bugu: "traumatic arthritis", ciwon gaɓa ne sak**akon lahani ga gaɓa daga bugu, faɗuwa, faɗowa, haɗuran ababen hawa ko mummunan lahani daga wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.

Alamomin Ciwon Gaɓoɓi
Alamomin ciwon gaɓoɓi sun haɗa da:

1. Ciwo a gaɓa

2. Riƙewar gaɓa

3. Kumburi a gaɓa

4. Wahala, kassarewa ko nakasar aikin gaɓa.

Alaƙar sanyi da ciwon gaɓoɓi

Da farko, a nan muna magana ne a kan sananniyar ma'anar sanyi, wato sanyi kishiyar zafi ko ɗumi. Wato k**ar sanyi daga yanayin sanyi, ɗari ko hunturu, sanyin danshi ko laima, da kuma sanyin damuna ko sanyin fadama da dai sauransu.

Tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi na daga cikin ƙorafe-ƙorafen da aka fi yi wa likita lokacin sanyi ko hunturu. Sai dai, k**ar yadda muka fayyace bayani kan sabuban nau'o'in ciwon gaɓoɓi a sama, za mu ga cewa bayanin ya saɓa da tatsuniyar da ke yawo a cikin al'umma cewa sanyi ne sababin ciwon gaɓoɓin. Kamar yadda ake cewa, "tashi" ko "ta'azzara", wato ciwon gaɓoɓin daman yana nan sai dai sanyin ne kawai ke tayar ko ta'azzara shi.

To amma me ke janyo tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi?

Har zuwa yanzu, a kimiyyance, ba a san haƙiƙanin sababin tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi ba. Sai dai, ana alaƙanta tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓin da abubuwa k**ar haka:

1. Raguwar zafi ko ɗumi a muhalli ko sararin samaniya.

2. Danshi, laima ko kaɗawar sassanyar iska a muhalli ko sararin samaniya.

3. Raguwa ko ƙarancin sinadarin bitamin D.

4. Gado: Mafi yawan mutane sun gaji ƙwayoyin halitta da ke tayar ko ta'azzara ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi. Saboda haka, akwai mutane ƙalilan da sanyin ba ya tayarwa ko ta'azzara musu ciwon gaɓoɓi.

Hanyoyin kiyaye tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi.

1. Sanya tufafi ko sutura mai kauri ko kuma a ninninka tufafi domin jiki ya kasance cikin ɗumi. Haka nan, ya k**ata a sanya safar hannu da safar ƙafa da kuma sanya takalmi sawu-ciki domin kauce wa ratsawar sanyi.

2. Amfani da ruwan ɗumi yayin ayyukan yau da kullum, k**ar: sha, alwala ko wanka. Haka nan, masu aiki ko sana'a da ruwa, za su iya zaɓar ruwan ɗumi ko kuma ɗumama jiki lokaci-lokaci a yini domin kasancewar jiki cikin ɗumi.

3. Hasken rana: Lokacin sanyi hasken rana a muhallahi na raguwa. Shi kuwa hasken rana muhimmin sinadari ne wajen samar da sinadarin bitamin D, wanda jigo ne wajen gina lafiyayyen ƙashi da kuma magance lalurorin da ke lalata ƙashi da gaɓa.

Yayin da hasken rana ya sauka a kan fatar mutum, fata na amfani da hasken ranar domin samar da sinadarin bitamin D. Saboda haka, akwai buƙatar shan hasken rana lokacin sanyi domin samun wannan alfanu.

Har wa yau, zai fi kyau a zaɓi awannin aiki lokacin da gari ya yi ɗumi idan hakan mai yiwuwa ne.

4. Ingantaccen abinci/abinsha: Cina 'ya'yan itatuwa, ganyayyaki da kuma datsar hatsi na samar da muhimman sinadaran kiwon lafiyayyen ƙashi da gaɓoɓi. Bugu da ƙari, rage siga a abinci ko abinsha da kuma rage sarrafaffun abinci ko abinsha na taimaka wa gaɓoɓi su zauna lafiya. Siga da sarrafaffun abinci ko abinsha na da haɗarin haddasa kumburi a gaɓoɓi.

5. Atisaye ko motsa jiki: Kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da shawarar yin atisaye ko motsa jiki aƙalla na mituna 30 a kullum. Atisaye na taimaka wa jiki ya kasance cikin ɗumi. Kuma gaɓoɓin jiki za su kasance cikin lafiya da ingancin aiki yayin ayyukan yau da kullum.

Daga ƙarshe, idan kana fama da ciwon gaɓa, akwai buƙatar ganin likita domin gano sababin ciwon gaɓar domin bin hanyoyin magancewa dogaro da sababin ciwon gaɓar da likita ya gano.

©Physiotherapy Hausa

Ku yi sharing domin wasu su amfana.

09/11/2025

Shawara | Da zarar an lura da alamun SHANYEWAR ƁARIN JIKI sun fara bayyana ga mutum ya k**ata a dakatar da duk wani yunƙuri na ba shi duk wani nau'in abinci, abinsha ko magani ta baki har sai an garzaya asibiti likita ya tabbatar da babu matsalar haɗiya.

Domin shanyewar ɓarin jiki tana zuwa da matsalar haɗiya. Saboda da haka, a maimakon mutum ya haɗiye zuwa ciki sai ya sauya hanya zuwa cikin maƙogaro har ya kai ga cikin huhu.

Idan kuwa abinci, abinsha ko magani s**a shiga cikin huhu hakan zai haifar da gagarumar matsalar numfashi wacce sau da yawa ita ce ma ke sanadiyyar mutuwar mutum ba ita shanyewar ɓarin jikin ba.

Saboda haka ne ake sanya wa mai shanyewar ɓarin jiki robar hanci domin kiyaye wannan matsalar numfashin.

© Physiotherapy Hausa

KAKA, Kaka lokaci ne da ake tanadar MAGUNGUNAN GARGAJIYA domin kar su bushe su zube musamman Wadanda suke dauke laima a ...
09/11/2025

KAKA, Kaka lokaci ne da ake tanadar MAGUNGUNAN GARGAJIYA domin kar su bushe su zube musamman Wadanda suke dauke laima a jikin su kuma basa girman Bishiya, Dibansu yana bukatar sanin lokaci,Tsaftar Kayan aikin diban da yadda za ayi aikin diban gwargwadon irin Dabi'ar Tsuron, Sinadarai da ya kunsa da kuma gurin da ya fito. Ko ka Shirya diban Naka?

07/11/2025

"trapezius muscle" kenan. Wane suna ya k**ata a raɗa mata da Hausa?😁

07/11/2025

Allah Gwani | Ko Ka San Ayyukan Hanta A Jikinka?

1. Hanta guda ce daga cikin muhimman kayan ciki. Kuma tana nan a cikin ciki a ɓangaren dama daga sama, ƙasa da faffaɗar tsokar nan da ta shingice tsakanin ciki da ƙirji.

2. Nauyin hantar mutum ya kai nauyin kilogiram ɗaya da rabi (1.5kg).

3. Hanta na samun jini da ya kai yawan lita ɗaya da rabi (1.5L) a kowane minti ɗaya.

4. A hanta ne ake gama narka sinadaran abinci yadda jiki zai iya amfani da su k**ar dangogin siga, furotin, kitse/mai, magunguna, bitamin da sauransu.

5. Hanta taska ce da ke ajiye muhimman sinadarai zuwa lokacin da jiki zai buƙace su, k**ar siga, narkakken furotin, nau'o'in bitamin da sauransu.

6. Hanta na samar da sinadarai k**ar gulokos, narkakken furotin da sauran muhimman sinadaran da jiki ke buƙata.

7. Hanta ce ke samar da ruwan maɗaciya. Ruwan maɗaciya na amfani wajen narka abinci ajin kitse/mai yadda jiki zai iya zuƙar kitse/mai daga ƙaramin hanji zuwa cikin jini sannan jini ya kai shi zuwa dukan sassan jiki.

8. Hanta na yin aikin kawar da guba, muggan sinadarai da ƙwayoyin cuta k**ar bakteriya da bairos.

9. Hanta na sarrafa / samar da jini ga ɗan-tayi, haka nan, tana ajiyewa da samar da muhimman kayayyakin sarrafa jini k**ar sinadaran 'vitamin B12' da 'Iron'.

10. Jajayen ƙwayoyin jini na shafe kwanaki 120 suna rayuwa ne a jiki. Bayan saifa, hanta na daga cikin sashin jiki da ke kashe raunanan jajayen ƙwayoyin jini bayan sun cika kwanaki 120 suna aiki.

11. Hanta ce sashin da ke samar da mafi yawan zafi/ɗumi da jiki ke amfani da shi wajen ci gaban rayuwa.

12. Hanta ɓangare ne na garkuwar jiki. Domin hanta na samar da sinadaran da ke yi wa garkuwar jiki ƙaimi, bayan nan, tana yaƙar baƙin abubuwa da ke shiga jiki ta hanyar abinci, harbin ƙwayoyin cutuka da sauransu.

©Physiotherapy Hausa

07/11/2025

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Wannan 3D CT scan kenan, ba ƙirƙirarren hoto bane' na gaske ne, yadda Machine din ke fitar da hoto kenan, Inda zamu ga hoton na nuna mummunan raunin da ya jawo katsewar ƙashin gadon baya tare da laka zuwa gida biyu sak**akon hatsarin babur.

In kuka duba da kyau zaku ga akwai; karairewar ƙasusuwan haƙarƙari, tsinkewar laka, karyewar ƙugu, karyewar ƙashin cinyar kafar dama, tare da munanan raunuka a fuska da kokon kai mai tsanani.

Wannan ya nuna irin tsananin gudun da Matashin keyi kan babbar hanya, yayin da lokaci guda yai taho mu gama, A tsarin ginin jikin Ɗan Adam ba zai yiwu jikin ya iya rarraba ƙarfin bugun da duk zai sami jikin ba bai daya. Koda mutum na sanye da kayan kariya irinsu HELMETS da robobin hannu, Karo a sami irin waɗannan raunukan barazana ne ga rayu.

Raunin ya faru a dede inda muke kira T12 na ƙashin gadon baya, wanda in baku mance ba na taba fadamuku ƙashin gadon baya da kuke gani kowanne gado jijiyoyin da s**a shiga s**a fita daban ne kuma inda suke sarrafawa ajikin mutum daban ne.

Yanzu shi wannan a dalilin hatsarin nan da ya sami matsala a T12 bazai kuma takawa da kafafunsa ba har abada, bazai taba iya rike fitsari ko kashi ba, hanjinsa bazai iya tafi da abinci ba, ta yadda koda jikin ya samar da kashi saide ai masa Stoma ta saman cikinsa ake janye kashin amma bazai tafi da kansa ba, uwa uba bazai taba iya kusantar Mace ba har abada ya riga ya rasa wannan ikon, gaban baxai ma mike ba ballantana wanda kaga Matarsa ba lallai ta zauna ba, ya jawowa yan uwa da kansa wahala.

Thank God ya riga ma ya Mutu, ballantana aita kisan kudi tare da daga kadarori abanza inma dasu kenan. Kunga kowa ya huta

Wannan shine tsadar da jiki keda shi, ya ku matasa ku nisanci guje-guje akan abin hanwa bama Mashin ba har Mota, wallahi seconds daya ya maida mutum haka angama.

Sannan a daure ake sanya kayan kariya irinsu Hular kwano, seat bell , rage gudu, kuma ko yaushe ka ɗauka cewa direbobi basa ganinka. Ɗan lokaci kaɗan na gudu zai iya sauya rayuwarka gaba ɗaya na har abada.

Desclaimer/Takeaway: This post is for educational purposes only. And remember to always wear protective equipment, slow down, and always assume drivers don’t see you. One moment of speed can change everything.

© Ibrahim Y. Yusuf

29/10/2025

Tsutsar ƙwaƙwalwa mai tsawon santimita takwas likitan tiyatar ƙwaƙwalwa ya cire wa wata tsohuwa mai shekara 64 ƴar ƙasar Australia. Mafi ban mamaki shi ne tsutsar da ranta!

Hoton ƙwaƙwalwar tsohuwar na MRI ne ya nuna wani baƙon abu k**ar kumburi a cikin ƙwaƙwalwar bayan ƙorafin matsalolin ƙwaƙwalwa da tsohuwar ke fama da su.

Domin binciken baƙon abun a ƙwaƙwalwa ana tsakuro samfur ɗin abun sannan a gudanar da gwaji a kansa a ɗakin bincike domin tantance wace irin cuta ce, wato "biopsy" kenan a turance. To sa'ad da ake tsaka da tsakuro samfur ɗin ne likitan tiyatar ƙwaƙwalwar ya lura da wani baƙon motsi, da farko abokan aikinsa sun zaci jijiyar jini ce, ashe tsutsa ce take mutsilmutsil. Lamarin ya zo da mamaki kwarai da gaske.

Muna da labarin tsutsa a sauran sassan jiki dai, amma kun taɓa jin labarin tsutsar ƙwaƙwalwa?

© Physiotherapy Hausa

28/10/2025

Duba hanyoyi 14 da hawan jini ke yin mummunan lahani ga sassan jiki kafin a ankare.

1. Rarake jijiyoyi ko hanyoyin jini: Lafiyayyun jijiyoyin jini suna da ɗabi'ar balan-balan ne, wato suna iya talewa ko buɗewa yayin da zuciya ta bugo jini sannan su koma yadda suke. Amma idan aka samu hawan jini, ƙarfin bugun jinin na wuce yadda jijiyar jinin za ta iya jurewa. Saboda haka, yau da gobe, bugun hawan jinin a cikin jijiyoyin zai rarake cikin jijiyoyin. Rarakewar jijiyar jinin zai haifar da raguwar talewa ko buɗewa don wucewar jini cikin sauƙi.
Haka nan, da zarar cikin jijiyoyin sun rarake, kitse zai kwanta a duk gurbin da jijiyar ta rarake. Rarakewar jijiyoyin jinin, tare da kwanciyar kitse a cikin jijiyoyin jinin zai sa jijiyoyin su yi tauri tare da cushewarsu.

2. Bullin jijiyar jini: Hawan jini na iya bunƙura wani sashi na jijiyar jini har ta yi bulli. A duk lokacin da jijiyar jini ta yi bulli kuwa, ingancinta na raguwa, kuma tana iya fashewa a kowanne lokaci yayin da zuciya ta harbo jini. Fashewar jijiyar zai kawo ɓallewar jini a sassan jiki, musamman a jijiyoyin jini na kusa da zuciya da ƙwaƙwalwa.

3. Cutar jijiyoyin jinin zuciya: Kamar yadda kowanne sashin jiki ke da jijiyoyin da ke kai masa jini, haka ma zuciya da kanta tana da jijiyoyin da suke ba ta jini. Kitse kan taru a cikin jijiyoyin sai ya toshe jijiyar jinin. Wannan zai kawo cikas wajen gudanar jini ga zuciya, sannan ya haifar da ciwo ko zafin ƙirji da kuma rikicewar bugawar zuciya.

4. Bugun zuciya: A yayin da tittika ko diddigar kitse ta toshe wata daga cikin jijiyoyin jinin zuciya, hakan zai kawo ƙarancin iskar oksijin ga tsokar zuciya – sai zuciyar ta buga – aikinta ya tsaya.

5. Cutar jijiyar jini nesa da zuciya: Ƙunci ko toshewar jijiyar jini na iya faruwa a can nesa da zuciya, misali, a ƙafa wanda ke iya kawo ciwo ko damƙa, musamman yayin tafiya, a dambubu ko sha-raɓa.

6. Kassarewar zuciya: Hawan jini na sa jijiyoyin jini su yi tauri kuma su matse. Saboda haka, sai zuciya ta yi aiki tuƙuru don harba jinin zuwa dukkan sassan jiki. Aiki tuƙuru, ba dare ba rana, zai sa zuciya ta yi rauni har daga ƙarshe ta kassare.

7. Buɗewar zuciya: Ma'ana, aikin zuciya tuƙuru, domin ta harba isashshen jini, zai sa ta riƙa buɗewa, wato ta riƙa ƙara faɗi daga ciki. Kuma ƙaruwar faɗinta na nufin raguwar ingancin aikinta.

8. Shanyewar ɓarin jiki: Hawan jini shi ne kan gaba wajen haddasa shanyewar ɓarin jiki. Wani sashi na ƙwaƙwalwa zai fara mutuwa saboda rashin zuwan iskar oksijin sak**akon fashewa ko toshewar wata jijiyar jini a wani ɓari na ƙwaƙwalwa.
Alamun shanyewar ɓarin jiki akwai: karkacewar baki, rauni ko shanyewar hannu ko ƙafa, karyewar harshe, da sauransu.

9. Gigi/ruɗewa: Hawan jini na kawo canjawar aikin ƙwaƙwalwa saboda matsalar gudanawar jini a ƙwaƙwalwa. Wannan zai kawo gigi, ruɗewa, da ƙarancin nutsuwa a ayyukan yau da kullum.

10. Kassarewar ƙoda: Hawan jini shi ne na biyu a jerin sanadan da ke kassara aikin ƙoda. Tauri da matsewar jijiyoyin jini, ga masu hawan jini, na kawo cikas a ayyukan ƙoda k**ar tace guba daga jini zuwa fitsari, daidaita ruwan jiki da sauransu.

11. Matsalar gani: Hawan jini na rage gudanar jini a ido wanda hakan kan lahanta jijiyar laka ta ido, wacce take sadar da saƙonnin gani daga ido zuwa ƙwaƙwalwa domin fassarawa. Lahani ga jijiyar lakar ido zai kawo raguwar gani ko makanta gaba ɗaya.

12. Matsalar saduwa da iyali: Kamar yadda hawan jini ke rage gudanawar jini a dukkan sassan jiki, haka ma yake rage gudanawar jini a azzakari da farji yayin saduwa. Sannan matsalolin saduwa da iyali su biyo baya.

13. Raunin ƙashi: Fitsarin masu hawan jini kan kasance ɗauke da sinadarin kalsiyam (calcium) a ciki fiye da ƙima. Ana ganin yiwuwar hawan jinin ne ke sa jiki fitar da sinadarin kalsiyam zuwa cikin fitsari. Kuma, kasancewar kalsiyam muhimmin sinadarin ginin ƙashi ne, raguwarsa a jiki yau da gobe na kawo haɗarin karayar ƙashi, musamman ga tsofi.

14. Katsewar bacci: Hawan jini na sa hanyoyin iska na maƙogaro su saƙi, wannan zai kawo rufewar maƙogaro yayin bacci. Rufewar maƙogaron zai hana shaƙar iska wanda hakan zai sa mutum farkawa daga bacci ba shiri.

©Physiotherapy Hausa

28/10/2025

Physiotherapy Hausa is doing well for the achievement of public health matters, we appreciate it very much, Thanks

28/10/2025
27/10/2025

Ciwon gawut, wato "Gouty arthritis" a turance, nau'in amosanin gaɓa ne da ke faruwa sak**akon taruwar gishirin "urate" a cikin gaɓa.

Ciwon gawut na k**a gaɓoɓin jiki, sai dai, ya fi k**a gaɓar gwiwa da gaɓar babban yatsan ƙafa.

Ciwon gawut na faruwa sak**akon hauhawar sinadarin "uric acid" a cikin jini. Hauhawar wannan sinadari na iya faruwa daga sabuba k**ar: gazawar ƙoda wajen aikin tace sinadarin daga cikin jini zuwa cikin fitsari ko kuma hauhawar sinadarin daga cimaka da ke maƙare da sinadarin "purines".

Tuntuɓi likita da zarar kana jin ciwo a gaɓar tushen babban yatsan ƙafa ko kuma gwiwa domin yin cikakken bincike.

Domin ƙarin bayani kan ciwon gawut duba nan:https://facebook.com/100025077457099/posts/1012760169569889/

© Physiotherapy Hausa

26/10/2025

Tirƙashi! Likitan da ya yi wa kansa tiyata karon farko a duniya.

Daga cikin baƙin abubuwa mafi bam mamaki da duniyar likitanci ta gani akwai tiyatar cire afendis da Dr. Leonid Rogozov ya yi wa kansa. Dr. Rogozov, ɗan shekara 27, likita ne ɗan ƙasar Rasha da ke cikin tawagar mutum 12 ƙwararru da ƙasar Rasha ta tura zuwa Ƙuryar Kudancin Duniya, wato yankin 'antarctica', a karo na shida don bincike da kuma kafa sansani a shekarar 1960 — 1961. Bayan tawagar ta gama gina sabon sansanin a shekara ta 1961, sai aka ajiye Dr. Rogozov a sansanin domin zama cikin shirin ko-ta-kwana ga lafiyar 'yan tawagar.

Sai dai wannan tawaga ta mutum 12 ta gamu da cikas na katsewar sadarwa da sufuri zuwa sassan duniya saboda matsanancin sanyi da ruwan dusar ƙanƙara da akai ta yi tun a watan Maris na 1961.

Kwatsam, a safiyar ranar 29 ga watan Afirilun 1961, Dr. Rogozov ya fara jin kasala, tashin zuciya, zazzaɓi, daga baya kuma ya fara jin ciwo a kwiɓin cikinsa na dama. Abinka da likita, da jin waɗannan alamu ya san cewa alamun ciwon afendis ne ke bayyana gare shi. Kuma ya san ciwon afendis ciwo ne da kan buƙaci tiyatar gaggawa don cire shi domin guje wa fashewa da fantsamarsa zuwa sauran kayan ciki wanda hakan na da haɗarin gaske ga lafiya.

Sai dai, Dr. Rogozov ya yi rashin sa'a inda ya kasance likita tilo a cikin wannan tawaga ta mutum 12. Saboda haka, babu wani likita ko ma'aikacin lafiya a tawagar da zai iya ba shi wani temako game da lafiyarsa.

Don haka, Dr. Rogozov ya tsinci kansa cikin wani mawuyacin hali na "kai ne likita; kuma kai ne mara lafiya". Kamar yadda Malam Bahaushe ke cewa "wanzami ba ya son jarfa", amma dole ta sa Dr. Rogozov aniyar yi wa kansa tiyata domin ceto rayuwarsa. Wannan ya isa ka gane girman matsalar da ta tilasta wa Dr. Rogozov tunkarar ƙalubalen da bai taɓa mafarkinsa a rayuwarsa ba, wato yi wa kai tiyata.

Bayan da likitan ya ɗauki ƙudirin yi wa kansa tiyata, sai ya rarraba wa wasu daga cikin 'yan tawagar aiki domin temaka masa yi wa kansa tiyata; akwai mai riƙe masa madubi don ya riƙa ganin sassan jikin da ba zai iya gani kai tsaye ba, wani kuma mai miƙo masa kayayyakin tiyata.

Bayan ya yi wa kansa allurar kashe ciwo, sai ya shiga yi wa kansa tiyata. Wannan tiyata mai cike da fargaba da mamaki, an fara ta ne da misalin ƙarfe 2:00 na safiyar ranar 1 ga watan Mayun waccan shekara. Yayin da likitan ke tsaka da tiyata ya riƙa hutawa duk bayan mintina 30 — 40 saboda kasalar jiki da hajijiya / juya da s**a riƙa zuwa masa akai-akai. Amma duk da haka, daga ƙarshe-ƙarshe sai da ta kai shi ga hutawa tsawon sakanni 20 — 25 duk bayan minti 4 — 5. Daga ƙarshe, likitan ya sami nasarar cire wa kansa ciwon afendis, ya kuma sanya maganin kashe ƙwayoyin cutuka a cikinsa, sannan ya ɗinke duk a cikin awa ɗaya da mintina 45.

Dr. Rogozov ya ce wani babban ƙalubale da ya fuskanta yayin tiyatar shi ne yadda madubin tiyatar yake nuna masa sassan jikinsa a juye, wannan ya tilasta masa ajiye madubin daga ƙarshe, ya kuma koma amfani da lalume da hannunsa.

Dr. Rogozov ya cire zaren ɗinkin tiyatar bayan sati ɗaya inda kuma ya koma bakin aiki cikin sati biyu. Wannan baƙon al'amari da namijin ƙoƙari da likitan ya yi, ya janyo hankalin duniya a lokacin. Hakan ya sa ƙasar Rasha ta karrama shi da lambar girma ta 'Order of the Red Banner of Labour'.

Wannan haziƙin likita, ya kasance shugaban sashin tiyata a Cibiyar Bincike ta Saint Petersburg a ƙasar Rasha daga shekara ta 1986 — 2000.

Sai dai, Dr. Rogozov, ya mutu a shekara ta 2000 a ƙasar Rashan yana da shekara 66 a duniya bayan ya sha fama da kansar huhu.

Daga ƙarshe, yi wa kai tiyata da Dr. Rogozov ya fuskanta, wata manuniya ce ta cikakken ƙudirin aniya da kuma kyautata fata nagari a duk lokacin da ka fuskanci kowane irin ƙalubale a rayuwa.

Duba Abubuwa 10 da ya k**ata ka sani game da ciwon afendis:

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=196272912737083&id=111898987841143

Address

Near Wudil General Hospital Kano
Wudil

Telephone

+2348172333323

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Sarkin Aska Modern Cupping & Traditional Medicine Venture:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram