23/01/2026
Dental Caries (Ciwon Hakori / Ruɓewar Hakori)
Menene kogon Hagori (Dental Caries?)
Kogon Hakori (Dental caries) cuta ce da take sa hakori ya ruɓe ko ya samu rami, sakamakon ƙwayoyin cuta da suke amfani da s**ari su samar da acid wanda ke lalata hakori a hankali.
Me ke jawo shi?
🦷 Cin abubuwa masu s**ari da yawa
🦷 Rashin wanke hakori yadda ya kamata musamman da dare
🦷 Shan kayan zaki akai-akai
🦷 Rashin zuwa duba hakori lokaci-lokaci
📍Alamomi:
🔹 Zafi yayin cin abu mai sanyi ko zafi
🔹 Rami ko baki a hakori
🔹 Warin baki
🔹 Ciwon hakori mai tsanani
💊Magani:
🦷Filling (cike rami) idan anje Assibiti da wuri
🦷Root canal idan ya ciwon ya tsananta
❌Cire hakori idan ya lalace baki daya
💉Rigakafi:
✔️ 🦷☃️ Wanke hakori sau 2 a rana da man goge mai fluoride
✔️ 🍹 Rage cin s**ari
✔️ 🪥 Amfani da asawaki ko floss
✔️ 🏥 Zuwa duba hakori akai-akai
Akiyaye Riga kafi yafi Magani
Malami Yabo Rchp