03/08/2023
KUMBURIN DASASHI (GINGIVITIS)
Gingivitis Wanda a turance akafi Sani da Gum Disease: kumburi ne wanda ke shafan dasashi wanda aturance muke kira da "Gum" wanda ya kewaye hakora. Kuma yana daya daga cikin abubuwan dake rike da hakora wato "Supporting structures" aturance.
Gingivitis yakan iya zarcewa zuwa periodontitis idan har ba'asamu anyi treatment nashi ba, wanda hakan yakan iya jawo rasa hakora baki daya.
ALAMOMIN SA:
1: Warin baki (Bad breath)
2: Fitar jini daga dasashi
3: Kumburin dasashi (Swollen gum)
4: Chanzawan launi na dasashi zuwa bright red/purple
5: Dasashi mai yalki (shiny gums)
6: Dasashi mai laushi (soft gum)
ABUBUWAN DAKE KAWO SHI:
1: Shan hayaki (smoking 🚬)
2: Rashin Daidaituwan Hakora (Maloclussion)
3: Bushewar baki (Dry mouth)
4: Rashin abinci mai gina jiki (Malnutrition)
5: Rashin goge baki yadda ya dace
6: Rashin sinadarin Vitamins musamman Vitamin C
7: Chanjin yanayi:- wanda yakan iya faruwa lokacin juna biyu, lokacin al'ada da kuma girma.
8: Cututtuka kamar su: kanjamau (HIV), ciwon sugari (Diabetes) da kuma cutar daji (cancer).
9: Tarihi daga yan uwa: masana sunce wanda yan uwansa ke dauke da cutar zai iya kamuwa dashi.
HANYOYIN RIGAKAFI
Hanyoyin da zaku iyabi wajen kare kai daga wannar cuta sun hada da:
1: Goge hakora sau biyu (2) a Rana
2: Kiyaye shan hayaki
3: Shan ruwa akai-akai
4: floss ta hanyar amfani da Dental floss/zare don cire raguwan abinci dake tsakanin hakora.
5: Cin abinci masu gina jiki
6: Ziyartar likitan hakora don wanke baki duk bayan wata shida (6 month).
MAGANI:
Domin samu magani da kuma ingantacce kulawa sai a ziyarci asibitin hakori mafi kusa.
✍️ Comr Ayuba Musa
2nd Aug 2023,