27/03/2017
ALFIRDAUS TAHIR ALIYU DA UMMU MUSADDAD ISLAMIC QIESTIONS N ANSWERS AL- ASHMAAWIY Bismillah wassalatu wassalamu ala rasulillah. (24) CIGABA DA KARATU CIKIN BABIN AZUMI Malam yace: Kuma Mustahabbi ne azumtar ranar arfa ga wanda baya aikin hajji, da azumtar goma ga Zulhijja da Almuharram da Rajab da Sha'aban, da kwanaki uku ako wani wata, Amman Malik ya karhanta su zama cikin ayyamul beed saboda gudun kar a iyakance kwanakin. Haka ya karhanta azumumtar sittu shawwal saboda tsoron kar jahili ya hadeshi da ramadan. Haka an karhanta dandanon gishiri ga mai azumi, in kuma yayi to ya tofar dashi kuma in babu wani abu nashi daya kai maqoshinsa to babu komai akanshi. Haka somi somin jima'i makaruhi ne ga mai azumi, kamar su sumbata, da shafa, da kallo wanda zaa dade (adade ana kallon har shaawa ya motsa), da wasanni in ansan bazaa sami matsala a yin hakan ba. (in ansan ko anyin mutum zai iya mallakan kanshi kar ya fadama abinda aka hana to shine yake matsayin makaruhi) amman in ba haka bama to haraamun ne yin hakan akanshi, amman in ya fitar da maziyyi saboda hakan da yayi to akwai ramuwa akanshi, in kuma ya fitar da maniyyi toh zaiyi ramuwa tare da kaffara. Qiyamu ramadan mustahabbi ne (tsayuwan dare) kuma an kwadaitar akan yinshi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce: Duk Wanda ya tsaya awatan ramadan yana mai imaani da neman lada to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa. Kuma anso ( yin tarawihi agida) daya, daya ( agida ba a jam'in masallaci ba) in har ansan bazaa bar masallaci ba kowa ba. Allah shine mafi sani. Nan muka kawo qarshen wannan littafi mai albarka: العشماوية في العبادات على مذهب السادة المالكية للشيخ عبد الباري العشماوي الرفاعي. Allah ya sakama Malam da alkhairi ya gafarta masa kurakuransa tare da sauran Malamanmu. Mu kuma albarkaci rayuwanmu, ya bamu ilimi mai albarka ya bamu ikon aiki da ilimin. Littafinmu na gaba shine Iziyya in Shaa Allah agaba kadan. Abinda muka fada daidai Allah yabamu ladansa, wanda mukayi kuskure ya gafarta mana, ya fahimtar damu kuma yabamu ikon gyarawa. سبحانك اللهم وبحمدك نشهد أن لا إله إلا أنت نستغفرك ونتوب إليك. ALFIRDAUS TAHIR ALIYU DA UMMU MUSADDAD ISLAMIC QIESTIONS N ANSWERS