10/18/2023
MUYI KOYI DA HALAYENSA!!!
Shifa Manzon ALLAH (SAW) Ya Kasance Lahira kadai Yake Hangowa da zuciyarsa Amma duniya Sam ba ta Gabansa, Don Haka Ya kasance bawan ALLAH Na Gaskiya, Mai Saukin kai ga Muminai
Yakan dade a Tsaye Tare Mai bukatar zantawa da shi.
Yakan je ya duba Marar Lafiya Yana kuma tausaya wa Mai Rauni, Yana Taimaka wa Mabukaci.
Yana Wasa da Kananan Yara, Yana Tsokanar iyalansa, Yana Cin Abinci Tare da Sahabbansa. Yakan Zauna a kan dandamalin kasa, Har Ma Yakan yi barci a kanta idan ya bukaci haka,
ko kuma ya kwanta a kan kungurumin tabarma wadda babu shimfida a kanta. Shuhura da neman suna ba sa gabansa, tunaninsa ko Yaushe Shi Ne neman yardar ALLAH
Ψ΅ΩΩΩΩΩ Ω±ΩΩΩΩΩ°ΩΩ ΨΉΩΩΩΩΩΩΩ ΩΩΨ’ΩΩΩΩ ΩΩΨ³ΩΩΩΩΩ
Ω
Baya son ya ji ana wuce iyaka wajen yabonsa, don haka yake tsawatarwa yana cewa:
Kada ku wuce iyaka wajen yabona, kamar yadda Nasara s**a wuce iyaka wajen yabon dan Maryam, (ANNABI ISAH) Yana Cewa ni bawan ALLAH ne, mu kuma sai muce bawan ALLAH kuma MANZON ALLAH
Bai yarda wani ya mike masa tsaye ko ya tsaya a bayansa shi yana zaune da sunan girmamawa ba. Duk sanda ya zo majalisa, to yakan zauna inda duk ya sami wurin zama. Idan yana cikin sahabbansa kuwa yakan saje da su har bako idan ya zo banda hasken fuskarsa da qwarjininsa da bazai iya tantance shi a tsakaninsu ba
Wannan digon-digo ne daga tekun kyawawan halayen Manzon Allah (SAW) da saukin kansa, wadanda dasu ne ya gagari duk makiyansa, da kuma sune ya mamaye zukatan mabiyansa, har s**a so shi s**a kuma kaunace shi fiye da komai a rayuwarsu.
Ψ΅ΩΩΩΩΩ Ω±ΩΩΩΩΩ°ΩΩ ΨΉΩΩΩΩΩΩΩ ΩΩΨ’ΩΩΩΩ ΩΩΨ³ΩΩΩΩΩ
Ω
Brother Mu kwatanta wasu daga cikin halayensa a rayuwarmu, don mu ga irin girman tasirin da za suyi mana wajen samun nasara a komai na rayuwarmu duniya wa lahira
Yusuf Hassan Jahun
Abou Ahmad Tijjani